← Book details Yancin Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 11

Sashe 10

Yancin Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*STORY WRITTEN BY*
*SURAYYERH B.ABDUL*
Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSAIN 80k*
Special gift to my besty *UMAMATU UMAR ADAM*
*____________________________________*
KAINUWA WRITERS
ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*PAGE 10*
Ganin sunyi shiru ne yasa doctor yaci gaba da bayani"Ni a gani na hakan ba wata damuwa bane indai har zaku samu wadda za'ayiwa dashen,sannan.....Ya isa plz!!Cewar yarima sameer cikin kosawa da maganar doctor,kamar bayason mgn yace "wannan maganar Sam kabarta doctor don abine Wanda baxai yuba,akan me za'a dibi sperm dina Wai a zubawa wata,never!!,ai wannan cutar da wadda aka sawa ne,idan ma batada aure mene matsayin budurcinta???Idan tarasa Shi fa????,,Dasauri gimbiya jalila tace "To ai wannan Abu ne me sauk'i prince,me zai hana tana shiga watan haihuwarta sai ayi c.s a ciro Mana yaron namu??Kaga kenan baza'a samu matsala ba muma Kuma zamu samu cikar burin mu,,,,tunda gimbiya jalila tafara magana yarima yake yimata wani d'an iskan kallon Amma bakida hankali,tana gama magana yaja wani d'an iskan tsaki yamike cikin bacin rai yabar dakin,a ransa yana ayyana cewa lallai gimbiya jalila ta haukace,,,ganin haka yasa gimbiya jalila tamike tsaye idonta akan doctor tace "wannan ba matsala bace doctor zamu dawo Kuma za'ayi dashen",,Gyad'a Kai kawai doctor yayi badon ya yadda zasu dawo din ba don baiga alamar yarima zai amince da hakan ba saboda yanda yaga ya fusata Kuma yasan halinsa.
Su muwadda suna inda su gimbiya suka barsu sukaga wucewar yarima sameer kamar a fusace yake,ba'a Jima ba Kuma sai ga gimbiya jalila itama dai kamar tana ckn damuwa,kafin suyi wani yunkuri sukaji muryar ta a tsawace tana fadin "Don ubanku ku mahaukatan ina ne???Uban me kuke jira da baxaku wuce mutafi ba??!!!,dasauri suka rufa mata baya suka fito,suna fitowa suka hango d"aya daga cikin motocin da suka kawosu tafice daga hospital din,ko ba'a fadawa gimbiya jalila ba tasan yarima ne,shiga mota tayi su muwadda ma suka shiga tasu,gimbiya a ranta take fadin "duk abinda xanyi don ganin ka amince zanyi Shi yarima Kuma xaka amince ne,matsala ta daya bansan wa za'ayiwa dashen ba",,Kai tsaye hotel din da suka sauka suka nufa.
Yarima sameer ne tsaye gaban mirror yana taje hadadden gashin kansa da ke ta zuba kyalli gimbiya jalila tashigo da alamun itama tayi wanka saboda ta canja kayan jikinta,ta jikin mudubi ya hangota Amma Sam bai nuna yaji shigowar ta ba saima cigaba da shirinsa yayi hankali kwance,ganin haka yasa ta k'araso inda yake tarike turaren da yake fesawa idonta a kanshi,kawar da kanshi yayi tareda sakar mata turaren yadauki wayarsa yana kokarin barin wajen,,dasauri tasha gabanshi idonta taf da kwalla tace "Don girman Allah prince katsaya muyi magana,,Sam baiyi niyyar tsayawa ba Amma jin tace girman Allah yasa yatsaya tareda kafeta da shu'umin idanuwansa Mai dimauta y'ammata,,ajiyar zuciya tayi tanajin yanda kirjinta yake bugawa,dakyar ta saita kanta tace "Mene abin fushi kuma prince??Ai ni a gani na abin farin ciki ne,abinda muka jima Muna nema shekara da shekaru Amma why zakayi haka???,,cikin hasala yarima Sameer yace "Keee karki rainamin hankali nifa ba shashasha bane kuma inada hankali,inason ki fadamin ta yaya su Mai martaba zasu yadda da wanna banzar maganar,,saboda haka yakamata kisan abinda kike fad'a,neman haihuwa ai ba hauka ba ne,sannan ki kwana da sanin gobe zamu koma gida,yakarashe yana kokarin wucewa,dasauri tarikosa tareda sakin wani marayan kuka tana fad'in "prince wannan abin fa ba haramun bane,akanme baxaka tausayamin ba Naga kwaina a duniya,,wlh ina matukar kaunar yara don Allah prince ka tausayawa rayuwa ta karkamin haka,shekara bakwai da aure na fa Amma banda d'an da zankalla naji dad'i,don Allah kayimin wannan alfarmar Naga kwaina d'aya ma Tak a duniya don Allah!!!!!,,,A hankali yacire hannun ta daga rikon da taimasa ganin tana neman sauya Masa ra'ayi saboda jikinsa da yayi sanyi ganin yanda take garshek'en kuka sai tabashi tausayi,Amma da yake namijin duniya ne Sam bai bari ta gane ba illa ma d'an iskan kallon da yabita dashi kafin yarab'a ta gefenta yafice daga d'akin,kwafa gimbiya jalila tayi tana share hawayenta kafin a fili ta furta "Matukar dai ni d'ince jalila dolenka ka amince prince!!!.
Su muwadda ne zaune a d'akin hotel d'in da suka sauka,hira sukeyi jefi jefi maganar muwadda bata wuce "Eh" A'a",Saboda gabadaya hankalinta yana kan mahaifiyar ta,tanason sanin halin da suke ciki,tanason jin muryarta Amma ta ina??Tasan dolenta hakuri zatayi har zuwa ranar da zasu koma wadda sudai basu santa ba a matsayinsu na y'an rakiya wadda ba wata k'ima ce dasu ba,,ajiyar zuciya tayi kafin tamike cikin zazzak'ar muryarta tace "Zan d'an fita waje",,Nasiba ce tace "Ai Kam dai kwara kid'an fita kiga yanayin wajen Amma da kin kule a d'aki kink'i motsi,,hmm Koda yake halinki ne haka Sai kace wata jinin sarauta",,,gajeren murmushi muwadda tayi batareda tace komai ba tafita daga d'akin,don inda sabo ta Saba da yanda mutane suke cewa Wai idan tana Abu tamkar jinin sarauta ,jin Kai tareda Shan kamshi,Wanda ita a zahiri batamasan tana da su ba.
Tafiya takeyi Amma gabadaya hankalinta bayaga tafiyar,don kallon da tafito yi Sam bashi takeyi ba,,batai aune ba taji tayi karo da mutum ,,dasauri ta tsugunna sakamakon wayar wadda sukai karo da Shi da ta subuce ta fad'i,,dai
lokacin shima yakai hannu zai dauki wayar,,haduwar hannuwansu ne yasa muwadda dagowa dasauri Saboda wani shock da taji,tareda wani mugun laushi na kyakykyawan hannun gami da sassanyan kamshi da yake tashi,,ido hudu sukayi da *YARIMA SAMEER* Wanda yai sanadiyyar bugawar kirjinsu lokaci guda,a Matukar tsorace muwadda tamike cikin rawar murya tace "Don girma Allah yarima kayi hakuri wlh bansani ba,,,batare da yarima ya kalleta ba balle ya kulata yaja dogon tsaki Yana karewa hannunsa kallo tareda yatsina fuska ,jiyake kamar ya shaketa Saboda takaicin goguwar hannunta da nashi,ganin haka yasa muwadda taci gaba da fad'in "Don Allah ka tausayamin ranka Shi dad'e wlh....."Kee!!!! "Yarima yakatseta a tsawace Wanda yasa muwadda zubewa dasauri jikinta yana rawa,ckn hasala yace "Ke wace iriyar mahaukaciya ce mara nutsuwa????Baki iya magana d'aya ba ne??Kindamu mutane da surutu da wani k'azamin banzan bakin ki,mtsewww yaja tsaki yabar wajen,,,Cikin tsantsae takaici muwadda tamike tana share hawayen da yake tsere a kumatun ta,itakam Sam a rayuwa tarasa meyasa masu mulki suke son yiwa na kasansu wulakanci,sunason k'ask'antar dasu su a dole sun fisu,,jitayi gabadaya ma baxata iya fitar ba,jiki a sanyaye takoma d'akin su.
Yarima kuwa yaja tsaki yafi cikin kwando,,gabadaya ma kyankyamin hannunsa yakeyi,d'aki yakoma inda ya tadda gimbiya jalila tanata kwasar baccin ta, bathroom yafad'a,yashiga wanka,dirje hannun yadingayi sosai tamkar zai sauya wani,yanayi yana yatsina fuska yana jan tsaki,,yadauki lokaci me tsawo kafin yabarshi haka badon ya yadda yafita yanda yake so ba,,fitowa yayi d'aure da towel hannunsa Kuma wani karami ne sky blue colour Yana goge lallausan gashin kanshi dashi,,shiryawa yashigayi lakwai
skin tamkar wata gold,yadauki lokaci kafin yashirya cikin wasu hadaddun riga da wando yasa masu tsananin kyau da tsada,red nd black colour,sannan yadora jacket a sama,,kamshin sassanyan turaren sa ne ya farkar da gimbiya jalila,,a hankali ta bude idonta tana k'are masa kallo,,wata iriyar muguwar kaunarsa takeji a kowani sassa na jikinta,,a hankali ta zuro k'afafunta tasauko,ra mirror ya hangota Amma bai juyaba,tana zuwa tayi hugging dinsa ta baya ckn iyayi tace "My prince kayi kyau da yawa fa",,Gajeran murmushin sa yayi tareda mirginota tadawo gabanshi,ckn kulawa yace "Kema haka",,Dariya tayi tana k'ara makalkaleshi,ganin lokacin salla yayi ne yasashi zameta Yana fadin "Kije kiyi wanka Kema ni zanyi salla ne",,Dasauri ta rikoshi tasa gwuiwowinra a k'asa tana hawaye tace "Wannan Shi ne karon farko da natab'a neman alfarmarka a rayuwa ta prince,,idan bakayimin va wlh bakin ciki zai iya kasheni,,Zan koma ga mahalicci na da Wannan tabon na kunci,don Allah ka tausayamin ka amince tunda ba haramun ba ne,ko ckn sirri zamuyi abinmu babu Wanda zai sani,wlh zanyi yanda kowa zaiyi tunanin nice na haihu da kaina,,Wannan sirrinmu ne mu kad'ai,,,"Ita Kuma wadda za'ayiwa dashen fa???yajefa mata tambayar,,Dasauri tace "Zatasani Mana prince",,Idonsa a kanta yace "Wace ce ita????cikin zumud'i tace zansamo wlh prince Zan samo,,mikewa yayi yadauki dadduma yatada sallah don matuka karshe tabashi tausayi Kuma ta raunata mishi zuciya tayaji tayi zancen mutuwa,shiyasa har yakejin zai amince,musamman da gimbiya jalila tace Masa zasu iyayi a sirrance har ace itace ta haihu batare da me martaba da kowa yasani ba.
Ita kuwa gimbiya jalila kamar tayi hauka Saboda farin ciki,don yarima Yana sallah tana zuba tsalle,hangota takeyi kawai gata rike da baby,,addu'a tashiga you Allah yabasu namiji don Shi tafi so tunda sune masu mulki,,tunani tashigayi wadda za'ayiwa dashen,tanason yarinyar taxama kyakykawa,me hankali,me nutsuwa,uwa uba shiru me sirri,,tunani tashigayi a kaf bayin masarautar su Wace tahad'a siffofinnan,,naxari tashigayi Amma a iya tunaninta tagaxa samu,lokaci guda zuciyarta tabata *KUYANGA MUWADDA!!!*,,,A fili ta maimaita tabbas muwadda itace yarinya me tsananin sirri tareda tsoro,baxata taba tona sirrin ba,,mikewa tayi ckn farin ciki tana tsalle tashiga bathroom yin wanka.
Bayan gimbiya jalila tayi wanka tafito tashirya tayi sallah,,sunacin abinci da yarima tanata zubamasa hira Saboda tsananin farin cikin da take ciki,sanar masa tayi yarinyar da ta yanke shawara a kanta,,wani d'an iskan kallon bakida hankali ta wurga Mata,,cikin kissa tashiga yimasa abubuwa tana fad'a Masa dalilanta,da yaduba Kuma Sai yaga gsky tafad'a,,Amma Shi Sam baiso haka ba Saboda baya kaunar ko ganin muwadda Sam,,a Daren ranar suka Kira doctor suka sanar dashi,sosai yayi mamaki kafin yace gobe da karfe 11 na safe suzo da yarinyar ayi aikin tunda tashin yamma zasuyi,,a ranar gimbiya jalila tamkar ta zuba ruwa a k'asa Tasha Saboda farin ciki,,yarima Sameer kuwa yaga tsantsar soyayya tamkar zata cinyeshi a daren ranar.
*Plz kutayani addu'a Allah ya shirye ni nadinga typing akan lokaci
don wlh naxama lazy wajen typing ynz
```Typing error zaku iya cin karo da Shi don bansamu damar editing ba```shi.*'YANCIN BAYI*
{Historical fiction}
Chapter 10 · 0% Book details