← Book details Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 30

Sashe 6

Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.......Da sauri Hayatu dake tsaye daga bakin ƙofa yaja da baya kansa a ƙasa yana ƙoƙarin ƙumshe dariyar dake neman kufce masa. Isowarsa dai-dai saitinsa ya sashi haɗiye dariyar da ƙyar ya buɗe masa ƙofar da sauri yana ƙoƙarin matsawa.
     “Kuzo da kayan”.
Ya faɗa a hankali dai-dai yana ficewa gaba ɗaya daga ɗakin.
         “A lallai Mu'azz ka haifoma kanka jaraba wlhy.”
    Hajiya Mammah ta faɗa cikin tafa hannaye da riƙe haɓa. Babu wanda ya iya cewa da ita komai dan duk abin faɗar ya gudu musu a bakuna. Sai ma Baba prof ne daya motsa a hankali kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki yabi bayansa. Dole duk suma sauran duk suka motsa suka take masa baya. Sai da suka gama fita Hayatu ya ƙarasa gaban doctor ɗin. Kallon Mama Balki yay yayi murmushi. Itama sai ta murmusa tare da nufar kayayyakin su kawai ta shiga haɗawa. Doctor data gama shiga cikin ɓacin rai kallon Hayatu tayi zatai magana. Da sauri ya katseta da faɗin, “Doctor kiyi haƙuri kawai ki bada takardar sallamar nan. Dan wlhy boss da kike gani baya magana biyu. Tunda ya yanke hukunci ya yanku, ya kuma fiki sanin muhimmancin wannan patient ɗin taki”.
      Cikin ɗan ɓacin rai ta ce, “Wane muhimmancin ta ya sani anan?. Ana gaya masa haɗarin da yarinya ke a ciki saboda zaluncin da akai mata yana nuna kamar ma baya fahimta. Ni ban taɓa sanin guy ɗin nan stubborn bane sai yau. Idan ma ɗakin ne bai masa ba way not yay magana sai a canja mata da wani”.
    Murmushi kawai Hayatu yayi dan ya fahimci bafa zata fahimta ba. Itama sai ta fita rai a ɓace tana mita dan gani gake shima Hayatun neman raina mata hankali yake yi. Binta kuwa yayi bayan ya amshi kayan da Mama Balki ta haɗa suka fito tare. Yana zuwa office ɗin doctor ta miƙo masa takardar sallamar a harzuƙe. Komai baice mata ba ya ɗauka ya juya abinsa ya fito.
          Samunsu yay suna shiga mota, dan shi gogan nasa ma har ya shige abinsa. Gaba ya buɗe ma mama Balki ta gefen sa ta zauna, shima yana ƙoƙarin shiga Baba prof ya ƙaraso wajen, umarni ya bama Mama Bilki kan ta fito ta koma motarsa, shi kuma ya shiga gaban ya zauna yana bama Hayatu umarnin suje *_KARAMCI HOSPITAL_* asibitin Hajiya ƙarama kenan. Amsawa Hayatu yay yana satar kallon Maash dake a baya tare da Samraah ta cikin mirror. Jingine kansa yake da kujera idanunsa a lumshe tamkar bai san mike faruwa ba. Shi kuma ya tabbatar duk yana jinsu. Kallo ɗaya yay ma Samraah dake kwance kanta a saman cinyar Maash ɗin itama idanunta a rufe ya ɗauke kansa yana ɗan sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya......

        🌿❤️‍🔥🌿❤️‍🔥🌿

     Hajiya Sakeena na kai ƙarshen bayaninta Mansoor ya fasa wata gigitacciyar ƙara da ɗaga Centre table ɗin gabansu ya wancakalar. Babu wanda bai firgita ba. Ƙafa yasa ya bugi table ɗin da masifar ƙarfi, badan takalmin dake a ƙafarsa ba babu abinda zai hanashi jin ciwo. Da sauri Attahir ya miƙe yana ƙoƙarin riƙo hannunsa da kiran sunansa. Amma sai shima yay wani irin wancakalar da shi gefe har sai da Attahir ɗin ya zube a kujera. Cikin zafin zuciya da basu taɓa sanin yana da ita ba ya nuna Hajiya Sakeena da Mamynsa da take wani irin kuka tamkar ranta zai fita. Cikin kaushin murya da rufewar idon da fushi ya haifar masa ya ce, “Na tsane ku. Ku biyun nan ba bana son sake ganinku a rayuwata har abada. Kuma yanda kuka zama sanadin rabani da ita kuma na barku har abada!!!!!!”.
     Daga haka ya figi bag ɗinsa fuuuu zai fice. Ƙoƙarin miƙewa Attahir yay cikin ƙarfin hali yana kiran sunansa. Yayinda Mamy tai wani irin fashewa da kuka ta bisa da gudu ta riƙo rigarsa. Ko juyowa ma baiyi ba yasa hannu ya kaɓe natan tare da hankiɗata yay ficewarsa. Kafin ta miƙe tabi bayansa tuni yama fice a gidan ko mai kama da shi babu a compaund. Nan ɗin ma fita Attahir yay a guje, sai dai yana fitowa napep ɗin data ɗauki Mansoor na barin ƙofar gidan. Komawa yay cikin gida da gudu bawan ALLAH duk ya ruɗe. Dan key ɗin mota yake lalube amma ya gagara ganin ko guda ɗaya. Haka ya sake fitowa da gudu ya fita shima ya tare napep ya shiga suka bi bayan Mansoor. Amma ko mai kama da shi basu gani ba. Har airport yasa suka bishi a tunaninsa can zaiyi. Sai dai nan ɗin ma babu alamar Mansoor ɗin. Abinda bai sani ba kuma Mansoor bai je airport ba, dan ya fahimci abu na farko da zasu farayi kenan dan haka yaje ya kama hotel anan anguwarsu da yasan bazasu taɓa tunanin zai tsaya anan ba. Na kwana ɗaya ya kama, dan daga yau zuwa gobe yake son sake barin ƙasar nan. Sam bazai iya zama ba. Gara yayi nesa nesa can inda bazai sake ganin kowa ba a cikinsu har ƙarshen rayuwarsa...

      Duk wannan budiri da ake Dad bai ko motsa ba. Yana zaune ne kawai kamar saƙago a falon. Ba haka Hajiya Sakeena taso ba. Taso ace tana gama bada labarin nan yanda Mansoor ya fusata shima Dad ya fusata ya dinga ɗirkar Mamy da jera mata kalmomin saki uku sannan yace ta bar masa gida. Amma ba komai, ko yanzu ma ai tasan ƙurar bawai ta ƙare bane ba. Dan ita shaidace akan zuciyar Dad tamkar akku kuturu yake. Kusan zuciyar tasa ce ma yau Mansoor ya kwatanta. Shi kansa shirun da yayi ta tabbatar zuciyar ce ta kume ƴan maza wayaga kutu-ban-ban. Haka ta fito babu tausayi babu imani ta tsallake Mom da nunfashi ke neman ƙwacewa tai ficewarta. Acewarta ai itama haka Mansoor ya tsallake tata ɗiyar ɗaya kwallin kwal a duniya ya tafi babu tausayi balle imani bayan ya gama zana mata kalaman saki uku da gasa mata magana iya son ransa...

     Duk neman daya dace Attahir yayi ma Mansoor amma bai gansa ba. Dole ya haƙura cikin maɗaukakin tashin hankali ya koma gida ransa duk a dagule. Yana zuwa kuma ya iske Mamy a sume a farkon shiga falo. Tashi hankalinsa ya sake yi, dan ga Dad zaune tamkar saƙagon gunki zuciya ya kumesa tamkar shima ɗin ya suma. Baima san ya sunkuci Mamy yay waje ba cikin tashin hankali yana kwala kiran sunan drivernsu.....

🪴🪴🪴🪴🪴

     *_KARAMCI HOSPITAL_* asibiti ne da zamu iya kiransa tsaka tsaki a girma. Dan bai kasance ƙaton gaske ba, bai kuma kasance ƙarami ba. A ɓangaren kayan aiki komai an wadatashi da shi. Duk da sunansa asibitin kuɗi ana aiki a cikinsa tamkar ƙyauta ne saboda sauƙi da sauƙaƙama al'umma. Hakan yasa mafi yawan talakawa suke saurin garzayowa jiyya da karɓar magani a cikinsa. Sai dai da yake komai nasu a tsare yake bazaka taɓa samunsa barkatai ba komansu a tsare yake.
      Kamar dai yanzu daya kasance rana ta fara ɗagawa, tako ina tsaftace yake sai ma'aikata dake ɗan kai kawo. Sannan shiru yake babu wata hayaniya ko yawan kai-kawon mutane bayan ma'aikatan saboda dokarsu ce irin yanzu ba'a zuwa duba mara lafiya sai yamma daga huɗu zuwa shida. Koda motocin su Maash suka iso ma da farko securitys ɗin ƙin tashi sukayi su buɗe saboda dokarsu ce ba'a ganin mara lafiya da dare ko safiya zuwa kafin cikar huɗu ko kai wanene, sai da Hayatu yay kiran number Hajiya ƙarama sannan securitys ɗin suka tashi cikin rawar jiki suka wangale gate ɗin. Suna gama parking Tsaki Hajiya Mammah tayi tana mita harda zagin Hajiya Ƙarama lokacin da take fitowa. Babu dai wanda yace da ita komai.
        Hajiya ƙarama da kanta ta fito tana musu barka da zuwa dan ita tunda safe tana anan asibiti batama san sunje duba Samraah ɗin ba, ana gama case ɗin human right ta baro gidan. Cikin girmamawa ta gaida Baba prof.. ya amsa mata tare da mata bayanin maido Samraah da sukai nan dan a cigaba da kulawa da ita duk da dai shi ba sunanta ya ambata ba ya dai ce yarinyar dake jiyya. Amma kuma yanata tunanin a ina yasan fuskar yarinyar ne tun ɗazun. Cike da girmamawa Hajiya ƙarama ta amsa musu. Tare da musu jagora har cikin manyan ɗakunan jiyyarsu na vip na ƙarshe a daraja. Kowa baiyi mamakin rashin biyosu da Maash yayi ba, dan sai da Baba prof ya koma da kansa ya masa umarnin bari a shiga da ita kasancewar tare ya tafi da nurses dake ɗauke da gadon ɗaukar mara lafiya. Amma mi, ammakinsu ma ko kallon inda Nurses ɗin suke baiyi ba yanzun ma ya sake ɗaukarta camak yay cikin asibitin. Da kallo kawai Baba prof ya bisa abubuwa da yawan gaske na masa kai-kawo. Dan a wannan gaɓar ya gama sarewa da al'amarin jikan nasa. Sai ma yake wasiwasi anya kuwa shine ya aikata fyaɗen nan kamar yanda Nafisa ta faɗa. Dan al'amarin akwai matuƙar ban al'ajabi a cikinsa da ma ban tsoro.
      Acan daga ciki suma kansu kallonsa kawai suke kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa musamman ma Hajiya ƙarama da bata ga abubuwan daya faru a farko ba sai wannan ɗin. Dan baki ta hangame har sai da taji iska na kai mata har maƙoshi sannan ta iya haɗiyewa da ƙyar.........✍️

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙_
Chapter 6 · 0% Book details