← Book details Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 30

Sashe 19

Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_

......Da uban sauri TJ ya taka birki dan shima firgita yayi, hakama Mama Balki, ya juyo zaiyi magana da sauri ya kauda kansa dan gaba ɗaya Samraah ta koma saman jikin ogan nasa ne. Mama Balki ma kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta tana Murmushi. Shiko gogan tun faɗa masa jiki da tayi idanunsa kawai ya lumshe saboda ƙarar da tai har cikin tsakkiyar brain ɗinsa ya jita. Shi mutum ne da sam baya son hayaniya. Taɓasan da Laalah ya ɗan yi yana gurnani ya sa ya fahimci abinda take ma tsoro. Lumsassun idanunsa ya buɗe, ya ɗan kalli Laalah ɗin sai kuma ya kalleta. Tayi masifar cikuykuye sa daga ita har ƙatoton hujjab ɗinta. Shi sai abinma ya so bashi dariya. Amma sai ya danne baiyi ba.
        Cikin silent voice ɗin nan tasa yay kiran sunan TJ. Amsa masa yay da girmamawa, sai kuma ya buɗe motar ya fita. Kasancewar glass ɗin ta inda Laalah yake an saukesa ya sa ya ɗan duƙo ta wajen sai dai kansa a ƙasa ba kallonsu yake ba. Maimakon amsa masa sai ya ɗan shafa kan Laalah ɗin tare da furta, “Maidashi wajen su Shu'aibu”. Kaɗa bindi Laalah yay alamar dai yaji ubangidan nasa. Tj na buɗewa ya dira da kansa.
        Duk abinda suke ina jinsu. Ina jin ya fita na sauke ajiyar zuciya mai nauyi tare da zame jikina daga kan nasa. Ban yarda na kallesa ba na koma can jikin ƙofa na lafe. Ban kuma sake yarda na ɗago ba har muka iso gida. Sosai naji wani irin farin ciki da zaƙuwar ganin naje ga Ummie, dan bazan ɓoye miki ba har cikin tsakkiyar rai nake jin ƙaunar baiwar ALLAHr nan wlhy bily. Ƙagara nayi motar ta tsaya, amma sai bata tsayan ba sai da akaje har ƙofar sashensa. Muna fitowa ina zumuɗin tafiya na koma waccan ƙofar Mama Balki ta dakatar da ni, magana na ɗago zanyi ta dakatar dani, tare da jan hannuna muka shige sashen nasa dan shi tuni yama shige abinsa. Mamaki ne ya kamani, yanzu kam kasa haƙuri nayi sai da nai magana kamar zanyi kuka.
         “Mama mi kuma zamuyi anan? Dan ALLAH mu tafi sashenmu ko wajen Ummie”.
      Kanta tsaye ta ce, “Banda ikon yanke wannan hukuncin Samraah. Sai dai mu jira daga bakin Alhaji ƙarami”.
    Sosai mamaki ya ƙara kamani, zan sake magana ta kama hannuna tai ciki dani. Zaune muka samesa a falo TJ na ajiye masa kofin coffee daketa tururi alamar yanzu nan ya haɗo masa shi. Tj ne ya amsa sallamar tamu, amma shi ko kallon ta inda muke ma baiyi ba. Wajen zama Mama Bilki ta nuna min, ban musa mata ba na zauna fuskata a kumbure. Kobi takaina batayi ba ta juya ta fita. A zatona wani abu zata ɗakko ta dawo, sai naji shiru har tsawon wasu mintuna. Ga TJ shima ya fice da ga ni sai shi. Karo na farko cike da ƙosawa na ɗaga kai na kallesa. Coffee ɗin sa yake sha hankali kwance tamkar ma bai san da zamana a wajen ba. Jinai raina ya sake ɓaci, amma sai na danne murya a sanyaye na ce, “Dan ALLAH zanje wajen Ummie na ganta”.
       Kamar bai jini ba, sai da ya mula dan kansa sannan ya ɗan ɗago idanunsa ya kalla ta inda nake. Dai-dai na ɗan hararesa ni kuma batare da tunanin zai ɗago ɗin ba.
    “Oh hararata ma kike?”.
   Ya faɗa fuska a dake. Da sauri na marairaice fuskata kamar bani ba, cikin kalar tausayi na ce, “No ALLAH ba haka bane. Kawai an samu kuskure ne ni yazan harareka”. Na ƙare maganar a matuƙar karyar da kai. Ɗauke idanun nasa yay cike da basarwa ya cigaba da shan coffee ɗinsa. Naji tamkar na fasa ihu kona kamashi da duka. Amma duk babu dama. Sai kawai na dake tunda na fahimci ƴan wulaƙancin ne a kansa....

        🌜💮🌛

    Kamar kullum tsaff ta fito cikin gayunta. Arwa ce riƙe da handbag ɗinta tana mata shagwaɓar ta bata kuɗi. Itako sai faman latsa waya take tana tafiya kamar ma bata jin ɗiyar tata. Sai da suka gama sakkowa da ga upstairs ɗin sannan ta miƙa mata hannu alamar ta bata handbag ɗin. Sake marairaicewa Arwa tayi da maida hannunta baya ta ɓoye jakar. “ALLAH Ummy ni bazan baki ba, just 200k fa nake so bawani kuɗi masu yawa ba. Gift da zan sayama Lubnah yau birthday ɗinta. Kuma motana fa nace miki duk friend ɗina sun sanni da shi, dan ALLAH ki bani baƙin naki, ALLAH bazanyi tuƙin banza ba i promise ”.
       “Riƙe promise ɗinki. Dan bazan baki motana ba. Ga dai 100k nan na saka miki je kiyi manage da shi banda kuɗi yau. Give me my bag jare. Kuma ki tabbatar kin dawo gidan nan kafin ten na dare. Dan karna shigo ban sameki ba. Zan ɓata miki rai”.
    Baki cike da iska Arwa ta miƙa mata handbag ɗin, babu ko godiya ta juya fuuuu ta koma sama. Kai kawai Hajiya ƙarama ta girgiza ta juya tai tafiyarta. Babu kowa a falon sai su A'i dake gyarawa. Gaisheta sukeyi cike da girmamawa. Itako tana amsa musu a nutsen nan nata babu alamar hayaniya a tattare da ita. Daka ganta kaga mace mai haƙuri da iya zama da mutane. Compaund ta fita, kai tsaye tai wajen motarta dan ita sam bata da driver. Bata yarda da kowa ba ita ke tuƙa kanta, tana ƙoƙarin ajiye handbag ɗinta a side ɗin mai zaman banza dai-dai nan Hajiya Mammah ke fitowa itama cikin wani shegen shiga na manyan mata dake ji da kansu. Kallon juna sukai, amma sai Hajiya Mammah ta watsar da Hajiya ƙaramar tamkar bata ganta ba ma. Lips Hajiya ƙarama ta cije tare da faɗin, (zanyi maganinki ne) a zuciyarta. A zahiri kam sai ta saki murmushi tare da nufar Hajiya Mammah ɗin cikin girmamawa ta gaisheta. A ɗage Hajiya Mammah ta amsa tana ƙoƙarin shigewa motar da drivern ta ya buɗe mata. Itama sai Hajiya ƙaramar tai murmushi ta juya ga tata motar ta shiga. Kusan a tare suka fice a gidan. Sai dai suna fitowa babban titi kowa yay hanyarsa. Ita Hajiya Mammah gidan Baba prof ta nufa, itako Hajiya ƙarama asibiti ta nufa...

          ⭐⭐⭐
Chapter 19 · 0% Book details