Sashe 18
Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.......Hannun bra ɗin ya maƙala min a inda ya zare, a tunanina zai matsa ne sai naji saɓanin hakan. Matsoni ya sake yi ta yanda har nake jin saukar numfashinsa a saman wuyana, sai kuma ya saƙalo hannun nasa ɗaya ta saman cikina. Yanda na sake matsewa a bangon bai hanashi jawoni baya ba a hankali, kansa ya ɗoro a saman kafaɗata tattausan gashin kumatunsa dake da laimar da nake ƙyautata zaton zufa ce tunda sports wear ne a jikinsa na gugar gefen fuskata. Ɗayan hannun ya ɗaura a saman nawa dake rufe da ƙirjina har yanzu zai zame, aiko naƙi yarda na sake ƙanƙamewa.
“Na cire towel ɗin kenan?”.
Soft voice ɗin sa dake fita low sosai cikin maƙoshi ta ratsa kunnuwana. Kaina na girgiza masa alamar a'a idanuna na cika da ƙwala.
“Oya remove your hand kona ciresa tas”.
Nasan zai iya, dan kaɗan daga ƙaramin aikinsa ne. Dan haka na shiga zamesu a hankali hawayen da nake maƙalewa na sake taruwa cikin idanun. Sake matsesu nayi jin yanda yake jan towel ɗin a hankali, har ya gama sauke b ɗin kan jikina babu kunya babu tsoron ALLAH ya gyarata ta zauna da ƙyau sannan ya maida min towel ɗin a sama.
“I love white musamman yanda wannan ta miki ƙyau”. Ya faɗa cikin kunnena cikin raɗa.
Da sauri na toshe kunnena tare da ture masa kai dan bana ma son ji. Maimakon ya barni kamar yanda naso sai ma ya sake nanne ni da jikinsa tare da sumbatar wuyana da hannun dana toshe kunnen. Ni kaɗai nasan kalar masifaffiyar kunyar da nake a ciki da mamakin tasa rashin kunyar dan shi komai yana yinsa ne kansa tsaye. Mun kai tsahon mintuna biyu a haka sannan ya janye jikinsa a nawa tare da kama hannuna. Ban buɗe idanuna ba, sai alamar zaunar dani da naji yayi a bakin gado. Jin kamar ya jawo kujera ya zauna gab dani dan har ƙafafunmu na a cikin na juna ne ya sani buɗe idanuna dake mar-mar. Kamar yanda nayi hasashen hakanne kuwa. Ya jawo kujera gab da ni ya zauna hannunsa ɗauke da rigar asibitin da aka ajiye min a saman gadon. Idanunsa kan p ɗin dana ajiye. A zabure na kai hannu na ɗauke ina ɓata fuska kamar zan yi kuka na cikukuyesa a hannuna na tura ƙarƙashin cinyata. Mayatattun idanunsa ya zuba min tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Hand”.
Bani da zaɓin daya wuce miƙa masan kawai, dan nasan ko cewa nayi bana so bazai barni ba. Inaji ina gani ya saka min rigar sannan ya miƙar dani a gabansa kamar wata ƴar yarinya ya zare towel ɗin ya ajiye gefe. Hannu ya miƙa min wai na bashi p ɗin dana sake saurin ɗaukewa. Kafaɗa na maƙe masa ina juyar da kaina gefe. shima sai ya taɓe nasa bakin kawai. Turaren dana ajiye gefe ya ɗauka ya ɗan duba jikinsa, sai kuma ya ɗan sake taɓe baki kaɗan, batare da yace komai ba ya ɗan fesa min ya maida ya ajiye. Ni dai uffan bance masa ba, kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hannuna. So nake na tambayesa yaya Ummie amma duk ya dabaibaye ni da salon da ban taɓa zaton gani daga garesa ba. Gashi duk abin nan da yake fuskar nan na'a tsukenta kamar bashi keyi ba. Da ƙyar na iya dauriyar faɗin, “Ina kwana? Yaya jikin Ummie?”.
Jin shiru bai amsa ba ya sa na ɗago idanu na a hankali kamar wata matsoraciya. Kamar yanda nayi zato shima nasan a kaina suke, dan haka da gudu nai yunƙurin kauda nawa amma sai ya riƙo haɓata da yatsunsa biyu.
“Ina miki aiki bazama kince kin gode ba”.
Baki na tura masa. Cike da ƴar jarumtar dana tattaro a tsiwace nace, “To ni dai ai bance ina so ba”.
Maimakon ya bani amsa sai naga ya saki wani shegen murmushi. Cike da suɓutar baki da mamaki na ce, “Lah yau ma kayi murmushi”.
Janye hannunsa yayi, tare da tsuke fuskar. Ni sai ma abin ya bani dariya. Sai kace wani ɗan yaro. Dariya nayi ina ƙoƙarin kare bakina na ce, “Ikon ALLAH, to kai baka so ace kayi murmushin ne? Sai kace wani abun mugun abu. ALLAH idan ma kayi murmushin kafi ƙyau. Amma kullum fuska a ɗaure kamar wani ma'aikin mutuwa.” na ƙare maganar ina haurawa saman gadon gaba ɗaya tamkar banga irin kallon da yake faman bina da shi ba. Sai da naja bargon na rufe ƙafafuna sannan na kuma marairaice fuska. A hankali na ce, “Yaya Awwab!”. Shiru yaƙi amsa min, sake maimaita kiran sunan nashi nayi a shagwaɓe. “Yaya Please answer me”.
Nan ɗin ma kamar bazai amsa ba. Na sake ƙoƙarin yin maganar cikin harara ya katseni da faɗin, “Ba kunni ke ji ba ne”.
Baki na tura sosai. Na ce, “To ai dai ba daɗi mutum yayi magana aƙi amsa masa.”
Banza yay min bai tanka ba. Nima sai na cigaba da faɗin, “Dan ALLAH ka taimaka a sallaman yau a asibitin nan. Idan ba hakaba ALLAH zan gudo gida. Ina missing ɗin Ummie sosai. Ni wlhy na warke fa”.
“Na gani”.
Ya faɗa kamar bashi ba yana ƙoƙarin yaye bargon dana rufama ƙafafun nawa. Da sauri na waro idanuna ina riƙe hannunsa. Kaji mun mutum to mizai gani?. Shanyayun idanunsa ya ɗago ya zuba min, ni kuma na marairaice fuska har idanuna na tara ƙwalla. Hannun ya janye kawai batare da yace min komai ba. Nima sai na sauke ajiyar zuciya dan al'amarin wannan mutumin yasha kan nawa ƙaramin tunanin gaskiya. Sake matsar da kujerar da yake zaune yayi gaban side drawer. Batare da yace komai ba ya shiga ƙoƙarin haɗa tea dan akwai babban basket mai murfi dake cike da kayan shayi kala-kala da su chocolate da kullum Hayatu baya gajiya da sayowa. Yo ni Hayatu ai zance tunda dai shine ke zuwa da su. Banda jiya da bai zo ba ɗayan yaron nan nasa da har yanzu ban san sunansa ba ya kawo snacks. Tea ɗin ya haɗa a zatona shine zai sha, har na fara gulmarsa a zuciyata sai naga ya miƙa min mug ɗin. Tsayawa nayi kawai ina binsa da kallon mamaki, dan haka muka ƙurama juna ido. Kusan minti ɗaya muna a haka kafin ya janye nasa da suke juyewa golden ƙwayar tsakkiya na zama siririya a wani irin salon yuuu ya ɗan lunshe su. Nima nawan na ɗauke da sauri ina haɗiyar wani yawu mai kauri dan gaba ɗaya jinai maƙogwarona ma ya bushe. Kofin ya ƙara miƙamin kansa a gefe, sai kuma ya miƙe.
Haka kawai kallon nima yay matuƙar min tasiri a cikin jiki da ma jinina, dan haka na gagara sake kallon inda yake har ya buɗe ƙofar ya fita. Ajiyar zuciya mai nauyi na sauke tare da rumtse idanuna na cije lips da ƙarfi. Tea ɗin na cigaba da sha da ɗan zafi-zafi batare dana san abinda nake ba. A haka aka sake buɗe ƙofar, a zatona shine dan haka na gagara ɗaga ido na kalli wajen. Sai da mama Balki ta rangaɗa sallama sannan na ɗago da sauri fahimtar itace.
Inda nake ta ƙaraso cike da tsokana take faɗin, “A lallai ɗiyata ta fara samuwa. Yau kece da haɗa shayi da kanki batare dana sha fama ba kina bata fuska da korafin bakinki ba bu ɗanɗano. To UBANGIJI ya ƙara sauƙi.”
A hankali nace Amin, dan a zatona bata haɗu da wannan pepper ɗin mutumin ba, sai naji hakan yamun daɗi. Sai dai me, bayan kamar mintuna biyar da zaman Mama Balki sai gashi ya sake dawowa tare da doctor. Miƙewa Mama Balki tayi fuskarta ɗauke da murmushi tana faɗin, “Har an kammala Alhaji ƙarami?”.
Cikin girmamawa, muryansa can ƙasa ya ce, “Eh mama sai ku shirya”. Jin abinda ya faɗa ɗin ya sani ɗagowa da sauri na kallesa. Sai muka haɗa ido. Da gudu na janye nawa na maida kan doctor dake min magana ɗan ji nake kamar ma kowa zai gane abinda ya faru tsakaninmu yanzu. Tambayoyi tamun tare da bani shawarwarin yanda zan kula da jikina yanda ya kamata har komai ya ƙarasa dai-daita. Duk bayan kwanaki biyu kuma zata zo har gida koni nazo asibitin za'a dinga sake dubani. Dan ba yau suka so sallamata ba. Sake ɗagowa nayi da mamaki sashen da yake. Yana tsayen dai har yanzu sai Mama Balki ce ke fita da kayayyakin mu tana dawowa alamar a iya ƙofa ake amsarsu. Yanda ya maida hankalinsa akan wayar hannunsa sai naji nutsuwa da alama baya jin duk abinda doctor ɗin ke faɗa. Taimaka min doctor tayi na sakko a saman gadon, hannunta riƙe da nawa ta ce, “Muje ki ɗan tattaka ƙyaji daɗin ƙafafunki tunda kwana da kwanaki kina zaune waje ɗaya babu ko babban motsi. Kaina kawai na jinjina mata, ta ɗauki hijjab da Mama Balki ta ajiye sabo ta saka min da kanta. Har ƙasa hijjab ɗin ya kaimin kamar wanda nake amfani da su a gida. Sai naji daɗi sosai dan yaushe rabo. Ta gabansa mukazo muka gitta bai kallemu ba bai kuma motsa ba har sai da muka fice gaba sannan. Kusan ƴammatan Nurses ɗin nan da suka dinga kulawa dani dasu aka ɗunguma min rakkiya har gaban mota. Sosai motar tai min ƙyau, banyi tunanin yana bayanmu ba, sai da muka iso ina sallama da Nurses ɗin da doctor naga an buɗe masa ya shiga, ba'a rufe ƙofar ba alamar ni ake jira. Ji nai kamar na fasa kuka, dan hakan na nufin a kusa da shi zan zauna kenan. Babu yanda zanyi, dan doctor da kanta ta taimaka min na shiga. Sai da aka maida ƙofar aka rufe har Mama Balki itama ta shiga gaba an ma tada motar muna shirin barin asibitin sannan na lura da shegen karen nan nasa dake tacan jikin waccan ƙofar. Wani irin fasa ƙara nayi tare da daka tsalle na faɗa jikinsa a matuƙar firgice, bazaki gane yanda nake masifar tsoron kare ba wlhy Bily.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_