← Book details Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 30

Sashe 25

Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

       A hargitse Hajiya ƙarama ta koma office ɗinta. Kofar ta kulle dan bata buƙatar ganin kowa. Kai-kawo ta shiga yi cikin Safa da marwa. Kafin ta jawo waya ta shige cikin toilet. Sau uku tana kira amma ba'a ɗaga ba. Kanta ta dafe cike da takaici. Yanzu haka yana can yasha giyar tashi yana shaɓar barci. “Motsoww” taja tsaki tare da fitowa. Wayar ta wurga saman desk ɗinta, itama ta zube a kujera tana mai dafe kai. Ji take yana wani irin sara mata. So take tai magana da wani ko zataji daɗi. Amma dawa ɗin zata yi. Da sauri ta sake rarumo wayar ta danna ma Jannifer kira. Bugu ɗaya kuwa ta ɗauka. Jin muryarta wani iri ta sata jan tsaki. “Malama dalla koma dawa koke tare ta tashi taba mutane waje magana zamuyi.”
        “Bara dai ni in tashi”.
    Jannifer ta faɗa tana ƴar shaƙiyar dariya. Tsaki kawai Hajiya ƙarama tayi batace komai ba. Sai da Jannifer ta sanar mata ta fito tana jinta sannan ta sake jan tsaki da fara magana. “Jannifer wai ina kika samo yarinyar nan ne? Wlhy tunanina gaba ɗaya nan birkicewa yake a wannan gaɓar?”.
       Da mamaki Jannifer ta ce, “Kamar ya? Wani abu ne ya sake faruwa?”.
    “Miye ma bai faruba. Yanzu nan nazo asibiti na samu wai banzan yaron nan Awwab yazo ya ɗauke yarinyar nan sun wuce gida?”.
            “Tofa babbar magana. Wai Maash kike nufi?”.
    “To in ba shiba waye zaima mutane wannan gadaran”.
Dariya ce ta kufcema Jannifer, sai da tayi mai isarta kafin da ƙyar cikin dariyar ta ce, “Kai amma yaron nan ƙwallon shege ne wlhy. I like him style wlhy. Komansa yake baya tsoron uban kowa. Ya taka na waje kuma na gidan bai barku ba ciwon kan da gwale-gwale yake baku. To wai kodai son yarinyar nan yake ne? Abinfa da mamaki wlhy, dan ni bammaga wani damuwa a tattare da shi akan abinda ya aikata ɗin ba. Ka ɗirkama yarinya fyaɗe amma ka dinga abu It's like you don't care, I really like this boy's style.”
      “Mtsowww!! Jannifer ban son shirme. Ina miki maganar serious kina mun wani soki burutsu.”
       “Ehm sorry Maa. ALLAH abunne ya ban dariya ya kuma burgeni. Samun irin stubborn mazan nan ba ko inaba. A Abuja nasan yarinyar ni gaskiya......” ta kwashe komai data sani akan Samraah ɗin tun daga haɗuwarsu da abinda ya faru kuma duk ta gaya mata”.
     Cikin damuwa Hajiya ƙarama ta ce, “Amma kema kinyi ganganci da baki san labarin nata ba”.
       “To banda abinki Hajjaju mizai sa na damu da labarinta. Ni fa dama irinta na fita nema. Sai kuma na samu miya rage min. Kaiwa na ɗako nazo na samu kuɗaɗena ai.”
    “Mtsoww!! Aikin kenan. To ita kuma Mashi'a ya akai ta zaɓi yarinyar? Bayan nasan idan kin kawo yara sai sunyi fin wata biyu ma kafin ki saida su. Musamman irinta ma ai baki badata a masu aiki?”.
       “Hummm ki bari kawai, wlhy kuɗaɗe kawai na gani. Dan an samu kuskure ne dana aika a kira min su ta biyosu. Nace ta koma Alaja Mashi'a ta ganta ta nace ita take so harda ninka min kuɗi. Ni kuma kawai naga bazan iya ba na sallama. Dan nasan ko ƙasar waje na kaita ba lallai na samu abinda na samun ba a wajenta. Kuma ina ma jin nauyin Alaja Mashi'a wlhy. Kin san dai ba wannan karon ne na farko dana fara samo mata masu aiki ba. Tunda kusan yaran gidankun nan duk a wajena aka amshesu mafi yawanci kuma itace ke zuwa da ɗauka musamman ma masu kula da Hajiya Babba.”
    Numfashi Hajiya ƙarama ta furzar, dan tasan gaskiyar zance Jannifer ke faɗa mata. Mashi'a tana kallon Jannifer ne kawai a mai kawo ƴan aiki. Kuma zama ta iya cewa itace ta nuna mata gidanta a lokacin da take neman masu aiki da zata wuce da su can Germany, shine take faɗa mata gidan Jannifer ɗin. Tunda ta ɗauka wancan yaran biyu ta wuce da su taji daɗin zama da yaran sai yazam duk sanda ta shigo Nigeria takan ɗaukama Hajiya Babba masu kula da ita. Ko idan taji wasu nason masu aiki takan musu hanya. Da yake itama halin Maash ne da ita yanzu haka yaran data ɗauka su biyu duk sunyi karatu a can. Ɗaya a cikinsu ma ta kusa aure da ƙanin mijin ita Mashi'a ɗin. Ƙaramin tsaki taja da ture batun Mashi'a ta koma wanda zai amfaneta. Amma ba komai, ita Awwab ɗin ma ya saukaƙa mata aiki, a gidan ma wasan zaifi armashi tunda yarinyar a sashen masu aiki take. Zata dakata ta dawo sashenta da kwana, ta nuna saboda abinda ya faru ta ƴanta yarinyar. Zata nema mata makaranta  kawai a wata ƙasar daga haka shikenan ta gama samun cikar burina..........✍️

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_
Chapter 25 · 0% Book details