← Book details Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 30

Sashe 12

Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    A gidan Abba Imamu rayuwa ta matuƙar juyama Mom baya. Dan sam ta kasa gane komai akan al'amarin Halime. Yarinya ce shu'uma matuƙa. Ga kalolin baƙin ciki da take tura mata iri daban-daban. Yanzu har takai Abba ya sallami mai aiki yace kowa tai aikinta ranar girkinta. Mom son jiki, Bibaa da Baby basu iya komai ba. Sai yazam a gidan duk ranar aikin Mom yini ake da yunwa, dan ko anyi abincin da wahala ya ciyu. Daga ƙarshe su ƙare da rigima ita da Abba. Dan ya tabbatar mata shi kam bazai ɗauki wannan banzan halin ba da almabazarancin abinci. Ashe da can duk wahalar gyaran gidan da abinci dama Samraah ce keyi ita kaɗai nata ƴaƴan na kwance. To ta sani bata cutar masa ɗiyar ƴar uwa ba kanta ta cuta. Dan ba baki ya mata ba ƴaƴanta in har a haka zata kaisu gidan miji to ta shirya kuwa za'a dinga koro mata su. Wannan magana tasa ta ƙona mata rai a ranar sai da suka tafka rigima sosai data kaisa da bata wan shika. Aiko dai tace babu inda zata. Kota kanta baibi ba yay ficewarsa.
      Sam Halime bama tasan abinda ke faruwa ba ita. Dan kwanakin nan gaba ɗaya bata ganema kanta. Kullum bata da aiki sai barci, itama dai aikin gidan a ranar girkin nata ƙarfin hali kawai take yi wajen yinsa. Sai yamma taji zazzaɓi yace salamu alaikum. Bazata taɓa samun nutsuwa ba sai irin sha ɗayan nan na dare. A yau ɗin ma da aka tafka rigimar har ya bama Mom sakin tana barci bata san bikin da akeyi ba. Amma mi, Bibaa da Baby na ganin Abban ya fita suka afka ɗakin Halimen wai zasu daketa. Sun san itace ke ƙullama Mom ɗinsu munafunci. Miye-miye dai magana tsaff a bakunansu. Cikin barci kawai Halime taji an sauke mata uban dundu. A firgice ta farka tare da sakin ihu. Sai kuma ta tsaya cak ganin Bibaa da Baby tsaye kanta suna huci. Kallon mamaki ta bisu da shi, sai kuma ta tashi da ƙyau cikin dakewa ta tambayesu ko lafiya?.
        “Uwarki zamu ci, shegiya annoba. Wlhy yau sai mun miki jina-jina a gidan nan dan ubanki”.
      “Tofa babbar magana, wai kishiya taga abin cikin zanen kishiyarta”. Halime ta faɗa tana yayimar ɗan kwalinta ta aza bisa kai tare da sakkowa a gado. Waya ta ɗauka tana cigaba da faɗin, “Ai ku jira bani kaɗai ya kamata ku cima uwar ba, dole na kira Imamu kamar abin zaifi armashi. Kunga sai ku tuɓe ƙaton banza ku haɗamu ku lakaɗa mana dukan tsiya tunda shine ya kawoni gidan”.
     Sororo Baby da Bibaa sukai suna kallonta. Kafin cikin ƙarfi hali da tsiwa Bibaa ta ce, “Badan Abbanmu ne ƙaton banza ba dan ubanki. Sai dai idan kece ƙatuwar banza. Kuma wlhy yau sai kin ban mana gidanmu”.
         Dariya sosai Halime ta sheƙe da shi, kafin ta riƙe haɓa da faɗin, “Oh ni Halimatu. Gidanku dai gidanku dai. To ke banda abinki Habi wace sakarar mace ke alfahari da gidan tsohonta? Ai macen data kai mace gidan mijinta take ma fata da alfahari, dan acan ne idan ta tadda komai rigijif-jif-jif sai kiga ta gyara gidansu albarkar iyaye ta bata tsaro tako ina. Dan haka riƙe cika bakin nan naki wannan gidan Halime ne da Jalilah, Habi dai har yanzu bata da gida sai na raɓe-raɓe. Garama ita wannan galwalin ta kusa shiga daga ciki”. Tai maganar tana nuna Baby..  
        Cikin fusata Baby tace, “Waye Galwali? Aiko yau sai na tabbatar miki na fiki hauka da tashanci”. Fuuu tayo kan Halime.......✍️

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_

......Kafinma ta kai hannu kanta ita ta ɗauke fuskar Baby da maruka. Ta shaƙo wuyan Bibaa dake bayanta itama ta bata nata. Basu gama dawowa a hayyacinsu ba ta shiga musu dukan kan mai uwa da wabi. Yo har a gayawa Halime iya danbe. Ita da ake kira giwar dambe a wajen ɗibar ruwa a garinsu. Kai hatta a islamiyya duk wanda ya sake ta haɗosu da Halime aka haɗu a lungun kaci uwaka bayan an tashi to ranar kuwa sai yaci uwar tasa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta musu lis da duka. Sai gasu a ƙasa suna faman ribzar kuka. Itako ta ɗauki sabuwar wayarta da Abba ya siya mata kwanan nan tayi kiransa tana kuka wai yazo gasu Baby da taɓare zasu bigeta.
     Bawan ALLAH sai gashi a haukace harda Alhaji Sadisu. Suka ko sameta kwance tana ɗan nishi ita adole ga wadda taci duka. Gashi ta kawo jan baki ta ɗan sassaka a wasu wurare na fuskarta da hannu wai duk sayin duka ne. Abinka da fara saika ɗauka haka ɗinne. Ido rufe Abba ya dinga sauke musu maruka abinda bai taɓa koda kwatanta yi ba. Sai dai ma idan Mom ta zugashi akan Samraah yana mata faɗa ita yana marinta suna dariya. Haukace masa Mom tayi da kuka da ihu, amma ada idan ta zuga aka mari Samraah daɗi take ji, ya kuma tabbatar mata idan har ta matso shi sai ya ƙara tsinke igiyar aurensu data rage. Dole taja birki tana kuka sai Alhaji Sadisu ne ya amshesu da ƙyar. Amma sai da yay musu lilis da duka ga wanda Halime tayi musu. Ya kuma tabbatar da ya matso da auren Baby nanda ranar juma'a ko daga shi sai mutanen anguwa ne za'a ɗaura ta tafi haka dan ta ishesa. Itama kuma Bibaan idan bata kama kanta ba zai aurar da ita ga duk wanda ya masa babu abinda ya shallesa da wani karatunta. Haka suka dinga kuka. Shiko ya kama Halimensa sukai ɗaki yana lallashi. Sai dai ita kuma duk jikinta yayi sanyi, dan harga ALLAH batayi zaton zai dakesu haka ba. Ita kawai tayi ne a tunaninta faɗa kawai zai musu a wuce wajen. Koda suka shiga ɗaki sai ta kasa haƙuri ta fito ta sanar masa gaskiyar abinda ya faru harda dukan datai musu. Tama nuna masa video data ɗauka dan sanda tace zata kirashi da farko bashi ɗin ta kiraba ashe video tajeyi.
      Wannan halin nata shine abu na farko da yake sakashi jin ƙaunarta fiye da koda yaushe. Dan a ɗan zamansu sam ya fahimci Halime bata iya ƙarya ba. Sannan bata taɓa kawo masa ƙarar Mom ta mata wani abu a gidan ba idan baya nan kosu yaran sun mata. Sai dai ita Mom ɗin ta tonama kanta da kanta asiri ta hanyar gaya masa. Shiyyasa yau data kirashi ya taho a rikice. Amma Mom wani lokacin ma tun suna rigimar take kiransa ta sanar masa ƙarya da gaskiya cikin kunfar baki. Idan ya dawo gida yana jiran yaji Halime tace wani abu sai yaji shiru, ko yama samu tana firinfijimarta a gidan hankali kwance tamkar komai bai faru ba. Dan ita in har akwai wuta tv na kunne shikenan tace bata da sauran takaici a duniya. Balle ta haɗa uban shayinta cikin ƙaton kofi da burodi ta soya ƙwai ta zauna tana sha tana kallo ai ji take duniya babu ya ita. Har da rana da yamma shan shayi take saboda masifar ƙaunarsa da takeyi tun tana ƙaramarta. Abinci ma bai cika damunta ba in dai akwai shayi da burodi balle ga madara a ciki yaji da sauran kayan shayi ace kuma akwai soyayyen ƙwai wayyo jinta take kamar a aljanna. Yasha gwadata akan magana da Mom take sanar masa game da ita. Amma mutuniyar sai ta basar tama nuna ita yaushe akayi hakan, idan ma anyi to ta manta. Koda yake harga ALLAH bawai tanayi don makirci bane ko wani abu. Kawai ita har cikin ranta da halayenta da anyi abu ya wuce shikenan kawai sai wani ya taso kuma. Wannan dai ta gama da babinsa. Idan ko har kakaga Halime ta riƙe abu a rai ya dameta to lallai al'amarin babbane matuƙa. Dan wahalar data sha a hannun innarta da ace tana riƙewa a rai da tuni hawan jini da ciwon zuciya sun kai rayuwar yarinyar ƙasa....

    ❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥

         Ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna suke shigowa gidan. Har gaban dashensa TJ ya faka motar, da sauri Shu'aibu ya fito ya buɗe masa. Koda ya fita maimakon shiga sashen nasa sai ya koma ainahin ƙofar shiga babban sashen gidan. Babu kowa a falon sai Azizat dake dakon jiran dawowarsa. Yana shigowa kuwa ta miƙe zambar. Fuskarta ɗauke da murmushi ta nufosa tana masa sannu da zuwa cike da shagwaɓa. Sai da tazo gab da shi ya wani watsa mata mummunan kallo yayi wucewarsa upstairs. Kai tsaye sashen Ummie ya nufa ya barta nan tsaye baki sake tana binsa da kallo ga hawaye na gudu a fuskarta. Sai kuma ta kwasa da gudu tai sashen Hajiya Mammah itama. Sai dai tana murɗa ƙofar bedroom ɗin ta tajita a rufe gamm. Jingina tayi jikin ƙofar tana sake fashewa da kuka. Sai kuma wani ɗan nishi-nishi da take juyowa kamar daga cikin bedroom ɗin ya sata fara sassauta kukan nata tai tsai alamar saurare. Tabbas daga ɗakin mahaifiyar tata ne. Knocking ƙofar ta farayi da kiran sunan ta amma babu alamar za'a buɗe, sai dai kamar anyi shiru an daina nishin. Sake fashewa tayi da kuka tare da barin jikin ƙofar da gudu tai ɗakinta.

     Wata shegiyar dariya Arwa dake laɓe tun ɗazun tana kallonta dan komai akan idonta ya faru ta saki, sai kuma cike da farin ciki ta furta, “Iska na wahalar da mai kayan kara” ta juya cike da takun girgiza jiki ta koma nata ɗakin dake a sashen uwarta Hajiya ƙarama. Dan su dukansu kowanne a sashen mahaifiyarsa yake har suma su Malika....
Chapter 12 · 0% Book details