Sashe 14
Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
......Zuru Paah yay masa yana kallo, sai kuma ya haɗiye yawu masu kauri yana jinjina kansa. “Muhammad wai sai yaushe zaka yarda dani akan mahaifiyarka ne? Ƙarshen maganata da kawai kaji baka san akan mi nakeyi ba, ba kuma kasan dawa nake yi ba”.
Fuska sosai Maash ya yamutse ransa na ƙara masa suya akan halin mahaifin nasa. Duk yanda yaso danne kar ya biye masa bazai iya ba, a fusace ya bashi amsa da, “Sai randa ka canja Paah. Sai randa ka ajiye son zuciya ka tuna da halacci. Bazan hanaka yin dukkan abinda kai niyya ba. Sai dai wlhy ina gab da ɗaukar mummunan mataki. Sannan yaronka na bashi nan da kwana uku ya sallami waɗan nan ƴan iskan yaran daya tara min a company, idan ba hakaba duk wani mai alaƙa dasu ya kuka da kansa. Kuma shima ya ajiye aiki da hannunsa kar ya bari na ziyarci Company yana ciki”
Cikin ɓacin rai da tsarguwa Paah ya ce, “Muhammad kana zargina ne?”.
Shiru yay yaƙi tankawa. Sai da Paah ya miƙe zuwa gabansa. Cikin sauke murya ya sake furta, “Muhammad miyyasa kai baka yafiya ne? Miyyasa kake da riƙo? Sai yaushe zaka yarda dani? Dan kawai kaji ina waya sai ka fasaarata da wata siga daban har kana tunanin sallamar waɗanda basu ji ba basu gani ba daga aiki”.
“Sai randa ka daina saka wannan ɗan iskan yaron na maka kawalcin yara ana kawosu da sunan wai ma'aikata. Paah na sanka fiye da yanda nasan kaina. Dama na jima ina zargin waɗan nan yaran zaman iskanci suke min a company. To wlhy na basu daga daren yau zuwa gobe su koma inda suka fito, in ma gidan karuwai zaka buɗe musu bai shafeni ba rayuwarka ce”.
Rumtse idanu Paah yayi da ƙarfi. Sosai kalaman ɗan nasa ke masa amsa kuwwa a cikin kunne. Yasan wanene Awwab idan yay fushi. Sam baya tauna magana yayin faɗarta balle shakka. Jin alamar zai bar wajen ya sashi buɗe idanunsa. Cikin ɓacin rai ya dakatar da shi da faɗin, “Miyasa baka tauna magana yayin furtata? Ina matsayin mahaifinka amma baka shakkar tauna magana yayin furta min ita. Komai ya zo maka a rai saika yaɓosa waje”
A daƙile da yanayin zafin rai shima Maash ya furta, “Ni ɗankane bani da hurimin hanaka duk abinda ka tsarama rayuwarka kam. Amma ka sani bazan iya cigaba da jurar ganin kana kana takamin mahaifiya a ƙarƙashin takalman ƙafarka ba Paah. Abinda na ɗauka kafin yanzu bazan iya ɗaukarsaba a yanzu. Idan da kace rashin mace ke saka aikata abinda kake aikatawa yanzu minene hujjarka kuma tunda kana da wata matar? Kai da kanka kamin alƙawarin dainawa, ashe baka fasa ɗin ba. Idan mace ɗaya ta maka kaɗan ka ƙara auren mana. Ka ƙaro uku su zama huɗu yafi min wannan mummunar ɗabi'ar taka mai zubar da mutunci ga zunubi wajen UBANGIJI.....” ya ƙare maganar cikin ƙaraji dasa hannu ya watso kayan saman mirror ɗinsa gaba ɗaya. Sai kuma ya kaima mirror ɗin naushi, a take kuwa ya shiga tsatstsagewa. Sake kai masa wani naushin yayi, ya kuma tsagewa tare da jimasa ciwo. Sai ga saman yatsunsa duk jini ya ɓata. Da sauri Paah ya kamo hannun nasa jikinsa har rawa yake. Amma Maash ɗin sai ƙoƙarin ƙwacewa yake yi. Dan so yake kawai ya ƙara kaima mirror ɗin duka ko zai samu sauƙin zugin da zuciyarsa ke masa...
“Please sweetheart relax. Dan ALLAH try to calm down. Jifa yanda kake jima kanka ciwo Muhammad”.
“Is not your business Paah. I beg you leave me alone”.
“Naƙi ɗin, nace maƙi na barkan! Miyasa kake da zuciya ne Muhammad. Fushinka yayi yawa. Taya zan Barka ka cigaba da jima kanka ciwo. Nace kayi haƙuri! Haba Muhammad”. Ya ƙare maganar cikin sanyin murya tare da jawoshi jikinsa ya rungume. Abinka da su duka dogaye, sai gasu kai ɗaya. Ƙarfi da cikar zati kawai Maash zai nuna masa saboda shi yana akan ƙuruciyarsa, shiko koba komai girma ya kamashi.
Luff Maash yayi a jikin mahaifin nasa, sai faman sauke zafafan ajiyar zuciya yake a jajjere. Yayinda Paah ke jin yanda zuciyar tasa ke gudu da ƙarfi. Sunfi mintuna uku a haka sannan ya ɗagosa. Kama hannun nasa yay suka nufi wajen gadon, zaunar dashi yay sannan yaje ya ɗakko first aid box ya dawo kusa da shi ya zauna. Hannun nasa dake ta tsatstsafo da jini ya kamo, cike da kulawa ya fara masa treating. Ko sau ɗaya Maash bai motsa ba, bai kuma kalla mahaifin nashi ba har ya kammala ya naɗe masa da bandage. Zama yay zai fara magana Maash ɗin kawai ya miƙe, da sauri Paah ya riƙosa ya maida shi ya zaunar. Bai musa ba ya zauna, sai dai yaƙi kallonsa yanzu ma. Shiru Paah yay yana kallonsa, sai kuma ya sauke numfashi a hankali yana sake tattaro abinda yake son faɗar. “Muhammad kayi haƙuri, tabbas nasan bana ƙyauta muku, sannan ban yima kaina adalci ba. Bazan kira abinda nake aikatawa da ƙaddara kawai ba, harda sa kai. Shiyyasa tabbas a rayuwa ka guji aikata mummunan aiki a ƙuruciya, idan kuma ya zama jarabawarka ce ka fara kayi gaggawar tuba. Idan ba haka ba wannan abin zai ta bibiyarka ne a lokacin girma, a lokacin da kuma kake son ka daina ɗin amma abin yabi jininka. Wannan maganar mahaifiyarka tasha faɗa min ita da maimaita min a duk sanda ta sameni a halin rashin gaskiya. Amma mi a lokacin bana gane karatunta, gani nake ai duk sanda na shirya zan iya dainawa”. Yay murmushin takaici, mai nuna ainahin ciwon da yake ji a zuciyar yasa. Cikin ɗan yarfar da hannu ya cigaba da faɗin, “Abubuwa da yawa sun faru, wasu ma suna kan faruwa da ni kaina ban san adadi ba. Ni ne ya kamata ace na tsaya muku, amma sam ban taɓa yunƙurin hakan ba koda sau ɗaya. Hatta da rashin Fahad a kusa da mu yana damuna. Sai dai ban san taya zance komai ba. Muhammad! Banso ace halin da nake ciki yayi nason da zai shafeku ba kamar yanda mahaifiyarku tasha yin fata. Sai dai a wannan gaɓar na fahimci zancen nan na masu iya magana da kance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Wlhy bazan ɓoye maka ba, case ɗinka akan yarinyar nan ya tsaya min ta yanda na kasa haɗiyeshi, sannan yanda kake bama yarinyar kulawa tamkar ba abinda ake gudu bane ya shiga tsakaninku na sake ɗaga min hankali. Bana son ace sunanka ya ɓaci a duniya Muhammad, wlhy bana son abinda wani zai aibantaka da shi, koda bazan ce komai ba ina jin zafi, matuƙar zafi a cikin zuciyata. Dan ALLAH ina roƙonka idan an sallami yarinyar nan daga asibiti gobe idan ALLAH ya kaimu zan haɗa mata sha-tara ta arziƙi tare da siya mata ticket ɗin jirgi idan ba ƴar cikin garin nan bace ta koma garinsu. Idan kuma a cikin garin nan take da iyayenta nasan zata iya yiwuwa a gidan haya suke ko wani muhalli ƙaskantacce. Zan saya musu gida a ɗaya daga cikin jihohin arewa su koma can, kar su sake waiwayar Lagos har abad....”
Karan farko Maash ya zuba masa idanun kawai yana masa wani irin kallo mai wahalar fassara. Kallon ne ya dinga ratsa Paah sai ya gagara ƙarasa abinda ya faro ya ja bakinsa kawai yayi shiru. Wani irin murmushin ƙasaita da ɓacin rai Maash yayi, sai kuma ya ce, “Ya kayi shiru kuma, ina jinka Paah.”
“Saurarena kawai kake amma ba jina ba Muhammad abar maganar kawai”. Ya faɗa cikin ɗan borin kunya da kame-kame. “Ka kwanta ka huta dare yayi, zuwa safiya sai mu ƙarasa, amma ka daina kira min ƙara aure har ma na mata uku, kai ka sakar min Ummu-Hidaya ɗin ne da kake cireta a matsayin matata”. Ya sake faɗa yana nufar ƙofa cikin ƴar sassarfa ya fice. Tsahon lokaci Maash ya ɗauka yana kallon ƙofar kawai. Sai kuma ya cije lips ɗinsa da masifar ƙarfi zuciyarsa na masa wani irin suya. Yasan mahaifinsa fiye da sanin da kowa ya masa a rayuwa. Amma bazai ce komai ba ALLAH mai ji ne mai gani. Yana kuma roƙonsa ya shiryeshi...
🤥Humm, kai dai Paah ALLAH ya shiryeka dai to gaskiya😏. Yayanmu kayi haƙuri mahaifi mahaifine koda na banza ne😭.
💦✨💦✨💦
Tun wucewarsa daga asibitin abubuwa suka sake cinkushe min kai. Kalamansa sai faman maimaita kansu suke a cikin kaina. Duk da nasha magani zafin zazzaɓin nan yaƙi bari na. Zaune na tashi ina kallon Mama Balki da barci ya ɗan fara figa. Sai kuma na miƙe cikin sanɗa na nufi ƙofar fita.
“Samraah ina zaki je?”.
Muryar Mama Balki a bazata ta daki cikin kunnena. Cak na tsaya tare da runtse idanuna. Sai kuma na juyo a hankali cikin son wayancewa zanyi magana ta dakatar da ni.
“Baki iya ƙarya ba Samraah, kada ki farata yanzu”.
Sosai furucin nata ya dakeni, dan haka na sauke ajiyar zuciya tare da dawowa a hankali na koma saman gadon na zauna. Kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna nace, “Kiyi haƙuri Mama. Ba wani abu zanyi ba. Reception zanje na samo pen da takarda zanyi amfani da su”.
“Amma a daren nan Samraah. Na kula tunda Alhaji ƙarami ya tafi baki da nutsuwa. Bana fatan ace kina son samo takarda da biron ne dan kiyi rubutun da zaki bar masa ki gudu”.
A karo na farko nayi murmushi tare da girgiza mata kaina. “Haba Mama, ai a yanzu wlhy koda shine da kansa yace na tafi gidanmu bazan je ba. Dan insha ALLAHU sai na sauke alkawarin dana ɗauka akan Ummie. Kawai zanyi amfani da sune dan ina son yin lissafi dalla-dalla. Ba kuma zai yiwu a cikin ƙwaƙwalwa ba dole sai da taswira a rubuce”.
Ajiyar zuciya Mama ta sauke. Batare da tambayata abinda zanyin ba ta miƙe. “Shike nan ki zauna ni bari na fita na samo miki. Kin san dai ba'a son ki yawaita motse-motse mai ƙarfi saboda ɗinkin jikinki”.
Bance mata komai ba sai duƙar da kaina dana sake yi. Itama sai ta fice abinta bayan ta zumbula Hijjab ɗin ta..........✍️