Sashe 30
Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ganin har gab da magriba bai sake fitowa ba munata hirarmu da Mama a falo Yaya Musaddiq yay min nuni da hanyar bedroom ɗinsa cikin hikima. Jinai duk kunya ta gama kamani, sai dai bazan iya musa masa ba. Dan haka na tashi sum-sum na wuce. Yanzun kam ban tsaya knocking ba na murɗa handle ɗin ƙofar a hankali na shiga kaina a ƙasa. Dan har yanzu ina jin nauyi da kunyar abinda ya faru a tsakaninmu ɗazun. Jin ɗakin shiru kamar babu motsi ya sani ɗan ɗagowa ina kallon ko ina. Sauka idanuna sukai a kansa. Yana zaune a cikin sofa sanye da bathrobe alamar bai cire ba tunda ya fito wankan, bowl ne na glass a saman cinyarsa da uban chocolates a ciki. Da mamaki nake kallon chocolates ɗin kafin na ɗan ɗaga idanuna akan fuskarsa. Da farko na zata ma barci yake a hakan, sai da naga gashin idonsa dogaye sosai sun ɗan motsa alamar kallona yake ƙasa-ƙasa. Kauda nawa idanun nayi kamar zan juya naji ya furta, “Zo nan”.
Idanuna na ɗan rumtse, dan duk sanda saukar muryarsa zai shiga cikin kunnuwana sai na jisu har tsakkiyar brain ɗina. Sai da na ciza lips da sauke numfashi sannan na juya kaina a ƙasa na nufesa. Ban zauna a kujerar da yake ba doguwa sai na zauna akan ɗayar dake gefensa dan guda uku ne dama. Doguwa ɗaya sai biyu masu zaman ɗai ɗai a gefe da gefen ta.
“Mi kike buƙata?”.
Ya faɗa a daƙile yana kai sauran chocolate ɗin hannunsa ƙaramin bakinsa. Satar kallonsa nayi ina mamaki a raina, namiji da cin chocolate, ai kayan yara ne da mata, duk yau banga ni dai ya ci abinci ba, sai dai ko da suka fita yaci. Ganin ya zuba min ido na ɗan girgiza masa kaina da faɗin, “Ba komai, kawai na jika shiru ne baka fito ba. Ga kuma abinci duk yau naga baka ci ba”.
Shiru bai tanka min ba tsahon kusan mintuna biyu, kafin ya ɗago a nutsensa zaune sosai tare da ajiye bowl ɗin chocolates ɗin nashi a Centre table. Murya can ƙasa ya ce, “Gashi ina ci”. Yay maganar yana nuna bowl ɗin chocolates ɗin. Da mamaki na ɗago idanuna sosai na warosu a kansa. Tare da furta, “Chocolate ne abinci? Abin kwaɗayin yara ne fa. Kai kuma ƙatoto da kai ka zauna kana ci, kuma amma ce fa maza basa cin zaƙi hak.....”
Ganin yanda yake kallona da mayatattun idanunsa na kasa ƙarasawa, sai ma na miƙe cikin wayancewa na ce, “An kira magrib bari na shirya kar su zo suna jirana”. Na wuce bayi da sauri.
Da kallo ya bita harta shige, sai kuma ya girgiza kansa shima yana miƙewa zuwa closet ɗinsa yin shirin massalaci.
💕💕💕
Bayan sallar magrib Hayatu da kansa yazo ɗaukarmu. Ogan nasa bai dawo ba. Amma tunda shi yace zamuje dama sai ban damu ba na shirya tsaff cikin atamfa riga da skirt a kayan daya kawo min. Ni da Hafizzullah da Mama a baya, Yaya Musaddiq da Hayatu a gaba. Yanda naga bakinsa yaƙi rufuwa saboda farin ciki nasan Mama ta gaya masa komai ko mahaifinsa. Nayi matuƙar mamakin ganin ƙayataccen gidan da shima yake a ciki. Sai na sake yarda da batun Mama Balki da tace su suna zaune a Maash Mansion ne kawai saboda Ummie. Shine gaba muna biye da shi, sosai ta ciki ma gidan yay ƙyau da tsaruwa. Sai da muka zauna ya kwala kiran mai aikinsu wata ƴar budurwar yarinya ta fito. Gaishemu tayi sannan ya bata umarnin kawo ruwa da abinci shi kuma yay sama. Babu jimawa sai gashi ya fito riƙe da ƙyaƙyƙyawar matashiya, gaskiya zata iya girmata koda shekara uku ne, da ƙyar take tafiya saboda cikin jikinta da yay girma sosai. Duk da fuskarta ta ɗan yi fushi irin na masu ciki hakan bai ɓoye kammaninta da Hafizzullah ba. Yanda muka zuba mata ido haka itama ta zuba mana nata. Lokacin da suke isowa gab da mu jikinta har rawa yake yi. Haka ta dinga bimmu ɗaya bayan ɗaya da kallo, kafin ta maida kan Mama da ke kallonta itama fuskarta ɗauke da murmushi. Cikin langaɓar da kai ta ce, “Mama ina ji a jikina su ɗin jinina ne. Dan ALLAH Mama kada kuce dani ba haka bane ba. Yaya Hayat yace bazai faɗa ba sai dai na gani da ido na”.
Murmushi mukayi mu dukanmu, kafin Mama ta gyaɗa mata kai. “Tabbas su ɗin jininki ne Falaq. Ga babban yaya Musaddiq, sai Samraah ban ƙanwa, sai auta Hafizzullah”.
Kuka ta saki a hankali idonta akanmu muduka ta ce, “Wlhy yaya kamar Baba, suna kama sosai”. Ta faɗa tana sake fashewa da kuka mai ban tausayi. Gaba ɗaya muka miƙe muka rufu kanta. Yaya Musaddiq akwai son ƴan uwansa, tuni ya janye ta daga jikin Hayatu ya kamata ya zaunar a kujera, gabanta ya durƙusa cikin lallashi yake mata daɗaɗan kalamai. Sai ta fara dariya ga hawaye. Ganin haka nima na zauna a kusa da ita na shiga share mata hawayen nata. Sai ta haɗamu ta rungume, tare da miƙawa Hafizzullah hannu alamar shima yazo. Ta ɗayan gefenta ya zauna shima muka haɗe kai waje guda muka bar Mama da Hayatu ƴan kallo. Mun jima a haka kafin Mama su dinga lallashinmu. Sallar isha'i data gitta ya samu miƙewa, mazan suka fita mu kuma mukayi anan gida. Koda suka dawo sabon babin hira muka buɗe, Yaya Musaddiq da Mama nata bamu labarin Baba. Dan Hayatu fita yayi wai Maash ya kirashi akwai inda zasu je. Banyi mamaki ba, dan sukam ko aljanu haka suka gansu suka barsu saboda shegen yawonsu. Sai naji tausayin Falaq ya kamani, haka take haƙuri (kema haka zakiyi haƙurin) zuciyata ta ayyana min. Da mama ke sanarma Falaq ɗin ni matar Maash ce a yanzu wani irin ihun farin ciki ta saki tana rungumeni, koba komai ƴar uwarta ta dawo kusa da ita. Tsaff suka bata labarin yanda komai ya faru, ta dinga farin ciki da ƙorafin Hayatu ita bai sanar mata ba. Kamar wasa sai ga lokaci yaja. Dan sai da sha biyu tayi sannan Hayatu ya dawo, shine yake cewa ga Maash a waje yana jiranmu. Kuka Falaq ta sanya wai anan zamu kwana, ita bata gaji da ganinmu ba. Cikin dariya Hayatu yace, “Nikam babu ruwana Hubby, keda yayanki jeki gashi can”.
Aiko miƙewa tai tana ɗaukar mayafina, itako Mama Balki ta miƙe tana faɗin, “A'a nidai kam nayi nan”. Dariya muka sanya mata, dan muma ba son tafiyar muke ba, saboda hirar bata ishemu ba. Sai addu'a nake a zuciyata ALLAH yasa ya yarda. Kusan mintuna biyar sai gata ta dawo tana tuttura baki. Mayafina ta cire ta miƙamin tana faɗin, “Ya yarda da ƙyar su Yaya su kwana anan ɗin, amma wai ke kije lil sis...”.
Ɓata fuska nayi nima kamar zanyi kuka. Nace, “Amma baki roƙesa ba ko Aunty?”.
“ALLAH har kuka na masa. Kin san taurin kan Yayana kuwa. Idan yace a babu mai canja masa zuwa b. Cayay da ma wai idan na haihu zaki zo. Bama gobefa kenan”.
Dariya Hafizzullah ya fashe da ita, harara na balla masa da ɗaukar mayafina fuuu na nufi hanyar fita...
Shima dai Yaya Musaddiq da ke riƙe dariyarsa da Hayatu sai da suka dara, kafin su miƙe subi bayanta.
Sanda suka iso ina tsaye jikin motar ta saitin inda yake ina masa magiya amma ɗan mannin bai ko buɗe idonsa dake lumshe ba ya kallan bare ya tanka. Haushi da takaici ya sani balla masa harara na koma ta ɗayan side ɗin dan Mama ce a gaba kusa da TJ, da sauri TJ ɗin dake a waje ya buɗen ƙofar yana wani risinawa. Ko kallonsa banyi ba na shiga na zauna na juya ƙeyata. Koda su Yaya Musaddiq suka iso wajen inaji yana magana da su wai ƙanwarsa ta masa fin ƙarfi shi da baƙi ita da ƙwacesu su kwana. Ina jin yanda suke ƴar dariya da bashi haƙuri. Basu wani jimaba yace ma TJ muje Mama ta gaji. Suna min sallama ƙin kallonsu nayi, ina jiyo dariyarsu su duka ukun sai naji idanuna sun cika da ƙwalla........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*