← Book details Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 30

Sashe 4

Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

       Maash kam daga falon hanyar da zata sadashi da sashen Ummie ya nufa. Ya samu sashen na sabon ƙamshi alamar an masa gyara. Sosai yayi mamakin waye kuma? Tunda yasan ita tana asibiti. Yana shiga yaci karo da mama Balki na shirin fitowa. Cikin kasa ɓoye mamakinsa ya ce, “Mama kece?”.
     Murmushi tayi cike da kulawa ta ce, “Eh Alhaji ƙarami. Ai mutuniyar taka ce tun asuba data farka take ta roƙona nazo na duba mata Ummie, tasan maybe bata ci abinci ba. Harda kukanta. Dan haka ina yin sallar asuba gari yay haske nai shirin tahowa sai kuma ga Hayatu ma yaje kai abinci shine na biyosa ya kawoni. Gata nan har ma taci abinci tasha magani barci ya ɗauke ta. Sauri nake kuma na koma can asibitin yanzu dan zata iya ƙin shiga ruwan zafin dana bar mata itama”.
            Idanunsa ya ɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya. Sai kuma a hankali da silent voice ɗin nan nasa ya furta, “ALLAH ya saka da alkairi Mama”.
    “Amin Alhaji ƙarami ai yiwa kaine. Bismillah ka shiga, Bara naje Hayatu na jirana zai maida ni”.
     Shiga yay ita kuma ta fice. Ya jima a ɗakin yana kallon Ummie har sai da kansa ya fara juya masa sannan ya fito. Da gaske sauƙi ya fara samuwa. Dan inda dane a yanda ya shigo ɗin nan komai barcin da take yi saita tashi kansa. Amma kalla jiya yafi zaman awa biyu amma harya fita bata ko motsa ba sai shine da ciwon kai ya addaba. Sashensa ya koma batare daya bi takan su Paah dake a falo ba. Yay wankansa ya shirya tsaff da shi. Bayan ya gama fesa turarurtukansa masu ƙamshi da tsada kala kusan biyar, shiyyasa ba'a gane ainahin turaren da yake amfani da shi yay zaman saka takalmi. Wayarsa da akai kira ɗazun bai ɗauka ba ya duba. MD ɗin companyn sa ne na Kano. Kiransa yay back, dan yasan akan maganar Musaddiq ne. Cike da girmamawa baturen mutumin ya gaishesa da ga can. Kafin ya ɗora masa bayani akan komai na Musaddiq ɗin ya kammala. Zuwa next week zai biyo jirgi zuwa nan Lagos daga nan sai ya wuce. Kamar yanda ya saba amsa wayarsa bata wuce ɗaya biyu koda zakuyi maganar awa ne ya amsa masa da “Okay” kawai ya yanke wayar. Daga haka ya ƙarasa shirinsa ya fito.
    Hayatu da Tj kawai ya samu a falon suna jiransa. Bai zauna ba da ga tsayen ya amsa gaisuwarsu yana mai ɗan kallon agogon hannunsa mai shegen tsada da ƙyau. Sai kuma a hankali ya furta, “Let's go”. Duk miƙewa sukayi, yana gaba suna binsa a baya, sai ma Hayatu ne dake ɗan masa bayani daya shafesu dan akan kasuwanci ne har suka iso gaban motocin da aka gama shiryawa domin fitar tasa. A tare guards ɗinsa da sauran ma'aikatan gidan suka dinga kawo gaisuwa da jajanta abinda ya faru, tare da masa addu'ar kariya daga sharrin duk wani abun sharri. A karo na farko ya ɗan saki gajeren murmushi tare da haɗe hannuwansa a waje guda alamar ya gode. Kamar ko yaushe yana baya TJ na mazaunin driver Hayatu a gefensa. Sai motar guards ɗinsa guda biyu ata gaba da baya su suna tsakkiya.
     Sam yawo da guards ɗin nan ba sonshi yake ba. Sai dai baida wani zaɓin daya wuce hakan saboda yanayin ƙasar tamu balle shi mai yawan maƙiya da masoya. Yasha tsallake tarko da aka shirya halaka rayuwarsa. Ana kusan ƙarshe ne da har ya samu harbi gab da shirin buɗe Companynsa na kano har aka harbesa, ALLAH dai ya taƙaita wahala harbin ya samesa a gefen kafaɗarsa ta hagu, daga nan ne Hayatu ya dage akan fitarsu da Guards ɗin.
      Tsaiwar motocin ya sashi kauda tunanin ya ɗago, ganin asibiti ya sashi ɗan kallon Hayatu daya buɗe masa ƙofa. Murmushi Hayatun yayi yana duƙar da kai da sosa ƙeya. Komai baice masa ba face ɗan girgiza kansa kawai ya zuro ƙafafunsa ya fito. Ciki suka nufa batare da ya lura da motocin su Paah ba, amma shi Hayatu sarai ya gansu dan tsakanin isowar tasu da tasu ma ƴan mintuna ne.........✍️

To Masha ALLAH. Barkan mu da dawowa, ku tayani addu'ar dagewa na gama book ɗin nan kafin salla😀🥰

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓_

_______

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG

https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

____________

......A ɓangaren su Paah kuwa isowarsu kenan asibitin suma. Ba kuma su san da su Maash a bayansu ba. Kai tsaye suka nufi cikin ɗakin bisa rakkiyar Mama Balki da sukai kira a waya. A tsorace cikin damuwa ta musu jagora dan bata san dami suka zo ba. Sai dai babu yanda zatayi dole tabi umarninsu. Sauƙin ma taga akwai Baba prof a tare da su. Sun shigo Samraah na zaune a kan gadon jingine da filo tana shan tea ɗin da Mama Balki ta haɗa mata a hankali. Fes take dan har tayi wanka saboda gashin ruwan zafi da Mama Balki tai mata bisa umarnin likitan. A hankali ta ɗago ta kallesu.
Chapter 4 · 0% Book details