← Book details Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 30

Sashe 22

Tsutsar Nama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

*_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏_

.......Mun jima zaune a hakan kafin ya mike a fusace. Taku ɗaya biyu ya tsaya cak, batare da ya juyoba cikin kaushin murya ya furta, “Daga yau zaki cigaba da zama anan”.
         Wani irin zabura nayi yan hanjin cikina na wantsalawa tare da bugun zuciyata. Bamma san sanda na furta, “Anan kuma?”. Ko kallon inda nake baiyi ba yayi wucewarsa hanyar bedroom ɗinsa. Wani irin bugawa zuciyata keyi diff-difff!! Dan har ga ALLAH maganar tashi tayi masifar ratsa min ƙashi da bargo. Wane irin neman bala'ine haka dan ALLAH. Taya zan cigaba da zama a side ɗinsa bayan Mama Balki ta sanar min babu wanda yasan akwai aure tsakanina da shi. Sannan yan uwansa ma abinda ya faru kallonsa suke ama tsayin fyaɗe. “Na shiga uku ni Samraah mutumin nan zai kasheni. Ni wlhy koma ba duk wancan ba bazan iya zaman anan da shi mu biyu kacal ba. Mutumin daya nema kusan kasheni ina gaskiya bashi yiwuwa. Gara ma tun kan wankin hula ya kaini dare na kama gabana. Inama laifin yace na koma sashen Ummie dan ALLAH. Zaram na miƙe, har haɗawa nake da sassarfa na nufi ƙofar fita. Sai dai kuma gam take alamar an kulle. Idanuna ne suka cika da ƙwalla. Ji nake kamar na saki ihu. Na jima a wajen kafin na yanke shawarar zuwa na bashi haƙuri tare da fahimtar da shi illar wannan hukuncin nasa dan bazai haifar mana da ɗa mai ido ba daga ni har shi ɗin....

🌜🌜💮🌛🌛

“Nafisatu ai ba amsar bane matsalar. Maganar kuma zamowarmu kuma family na farko a jihar nan a tunanina tuni muna ɗaya daga cikin masu wannan matsayin ama Nigeria ba jihar Lagos ba. Ɗanki ya jima da samo mana wannan sunan ama duniya ba'a ƙasar haihuwarmu kawai ba. Siyasa ta wuce duk yanda kike tunani, cike take da rikice-rikice da matsaloli iri-iri. Bazaki gane hakan ba sai mun farata. Amma dai ki bari zan tattauna da Awwab. Kin sanshi yanada experience akan irin waɗan nan abubuwan”.
       “Baba yanzu nan duk mu yawan yaranka har mu huɗu cif babu wanda zaka iya shawara da shi a shekarunmu sai jika. Awwab har wani hankaline da shi wanda ko aure baiyi ba.”
    “Humm Nafisatu, aure ai lokacine da shi ko?”.
          “Baba yana da lokaci, amma kuma kaima ya kamata ka motsashi, yanzu irin wannan abun daya faru idan da maganar nan ta fita mi muke tunani? Ni yanzu ma tsorona ALLAH tsorona yaji daɗi ya cigaba da aikatawa tunda ba kunya garesa ba. Ballema yaga ba'a ɗauki wani mataki ba akai ai kaga abun bamusan kuma ina zai tsaya ba. Tun fa yana taɓa ƴan aiki wlhy wataran kan ƙannensa zai dawo. Dan Awwab yariga yayi gaurin da macen kawai yake buƙata fa. Ya kamata a duba wannan zancen Baba. Idan yana akan bakansa shi baiga wadda yake so ba ai ga ƴar uwarsa nan Azizat. A haɗasu mana kawai tunda Ita dai bazataƙi bin umarninmu ba. Shima kuma idan yaga kowa yaƙi saurarensa ai dole ya amince a wannan karon tunda koba komai yana son asirinsa ya rufu kar duniya ta sani”.
        Jinjina kai kawai Baba yake. Sai da takai har ƙarshe sannan ya nisa. “Shawararki abar dubawace Nafisatu, kuma zan duba. Awwab ɗinne sai a hankali, yaro ne mai shegen taurin kan tsiya. Yanzu fa ki duba ki gani saboda yasan abinda yay ba dai-dai bane sam yaƙi zuwa gidan nan. Idan naje can duk yanda zai zame ya gudumin ya sani. Amma barshi nasan mi zanyi. Zanzo yau da dare na ritsashi in sha ALLAHU. Da zarar ya shigo gida ki kirani kawai”.
     Cike da farin ciki Hajiya Mammah ta amsa da, “To in sha ALLAHU kuwa Baba. Amma maganar siyasar nan itama dai dan ALLAH a duba mana. Yaya kaga Nafisatu Adams K/Mashi ɗiyar gwamnan jihar Lagos”.
    Yanda tai maganar tasa baba ƙyalƙyalewa da dariya. Itama dariyar takeyi....

        ❤️❤️❤️❤️

      Kamar mai tsoron a jita a hankali nai knocking ƙofar, shiru babu motsin komai. Sake yi nayi har fin sau uku. Ganin dai bazai kulani ba na yanke shawarar buɗewa kawai ma shiga. A hankali na murɗa handle ɗin kuwa. Sai ko gashi ya buɗe. Sai da na sauke ajiyar zuciya tare da tsayawa na daidaita kaina sosai sannan na tura na shiga da sallama. Turus na tsaya ina kallonsa dan zaune yake akan sofa daga shi sai towel da waya a hannunsa yana magana cikin yanayin nan nasa a daƙile kamar wanda akama dole. A hankali na maida ƙofar na rufe ina mai duƙar da kaina dan bazan iya jurar kallonsa a yanda yake ba. Nafi minti biyu a wajen ina sauraren wayar tasa dana fahimci da Hayatu yake yinta. Sai dai abinda ya ɗan ja hankalina jin yana faɗin idan sun huta Hayatun ya kawosu nan gida. To ko su waye keda irin wannan matsayin haka. Dan na fahimci tunda nazo gidan nan ban taɓa ganin wani baƙo daya shafesa ba yazo. In banda ranar birthday ɗin nan da Bahijja tace min wanda suke zaune a waje ɗaya abokansa ne, kuma duk ba'a ƙasar suke ba idan ka cire ɗan sarkin Lagos ɗin. Ganin har ya kammala ya miƙe yana ƙoƙarin nufar mirror ya sani gyara tsaiwata. Dan ya wani basar tamkar baima ganni ba. Kuma na san yasan na shigo ɗin rainin hankalinsa ne kawai. Kaina a ƙasa daga ƙofar ɗakin na furta, “Dan ALLAH ina son muyi magana”.
    Bai tanka min ba, bai kuma fasa abinda yake ba. Sai da ya mula dan kansa kusan minti biyu sannan ya magantu. Cikin silent voice ɗin nan tasa a daƙile ya furta, “Ki wuce wanka baƙi zasu shigo”.
        Ji rainin hankali, ina masa wata maganar yana min wata. To ina ruwana da wasu baƙinsa. A zahiri kam sai na ƙara sauke murya har lokacin kan nawa a ƙasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri ka barni naje can inda na saba. Ko kuma na koma sashen Ummie tunda dama a yanzu kusan acan ɗin nake. Ya Awwab taya zan dawo nan bayan kasan akwai matsala. Babu fa wanda yasan akwai wani maganar aure a tsakaninmu a gidan nan. Mi kake tunani zasu fassara zaman nawa?”.
       “Su fassara duk yanda yay musu! Idan kuma kina buƙatar su sanin ne, yanzun nan sai na tarosu su sani”.
    Da sauri na ɗago ina kallonsa. Yanda yay maganar kansa tsaye babu wani alamun ya ɗauki zancena da muhimmanci. Kai wlhy stubborn mutumin nan ya fara isata. Da ƙyar na iya dannewa muryata na ɗan rawa na ce, “Idan kai zaka iya fuskantar su ka kuma ɗauka komai wlhy ni bazan iya ba. Sannan ba wannan rigimar nake so ba yanzu lafiyar Ummie ce damuwata. Dan ALLAH ka duba zance na yana da muhimmanci...”
        “Kin dameni Madam wuce wanka kafin nazo kanki”.
    Ya faɗa da ɗan kaushin harshe yana ajiye cumb ɗin hannunsa yana barin wajen. Karan farko naji hawaye sun gangaro min.
      “Karna fito na sameki a wajen”.
  Ya sake faɗa dai-dai yana shigewa cikin cikin closet ɗinsa. Hannuna na dunƙule kamar zan kaima bango naushi sai kuma na tausayama kaina dai. Dan nasan nice zan sha wahalar a ƙarshe hannunna ya rugurguje a banza. Hararar inda ya shige ɗin nayi ina cizar lips ɗina da ƙarfi, ga hawaye share-share a fuskata. Jin motsin kamar zai fito ya sani zabura na nufi bathroom ɗin. Dole ina ji ina gani na haɗa ruwan wankan nai ƙoƙarin fara yi. Wankan nake ina hawaye da hango irin bala'in da zai iya biyo baya. Dan wlhy abin bazai zama mai sauƙin ba a gareni. Gara sashen Ummie da nake zama shi wannan suna ganin ai kamar ina cutuwane shiyyasa aka ɗagamin ƙafa. Amma nan fa? Ni kaina idan an titsiyeni ban san mizan ce ba. Dan nayi alƙawarin in har bada kansa ya fito ya bayyana musu wacece ni ba wlhy ko za'a kasheni bazan faɗa ba. Sai da na kammala wankan sannan hankalina ya tashi, dan ban san yaya zanyi da kayan sakawa ba kuma. Bathrobe ɗin sa na ɗauka na saka. Sallar walha da nake son zuwa nayi dan lokacinta yayi ya sani haƙura na fito, amma sai da na leƙa cikin ɗakin sannan. Shiru babu motsin komai, sannan a iya hangena ban hango alamar akwai mutun ba. Ɗan ajiyar zuciya na sauke na fito a ɗan ɗarare. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ganin tabbacin baya ɗakin, tunanin sauri na shafa mai yazo min, dan haka na nufi gaban mirror ɗin nashi. Zama nayi tare da bin kayan dake akai da kallo, cikin ɗan taɓe baki na furta, “Sai kace mace”. Da ƙyar na iya gane man shafawa, ina son na fara dubashi ina tsoron yin jinkirin da har zai dawo ya saman a wajen. Da sauri-sauri na shafa man da duk abinda zan iya amfani da shi a wajen. Na miƙe raina fal tashin hankalin kayan daya kamata ace na saka ya shigo. Daburcewa nayi dan abin yazo min a bazata. Rasa makamar riƙewa ta sani komawa kan stool ɗin kujerar na zauna tare da duƙar da kaina. Baiyi magana ba, sai madaidaicin akwati da yazo ya ajiye gab dani. Juyawa yay yayi ficewarsa yana faɗin, “Zanje wajensu, da munyi salla zasu shigo. Zaki iya zuwa duba Ummien kafin”. Daga haka yay ficewarsa. Da kallo na bisa duk kaina duk a ɗaure. Sai dai furta zan iya zuwa duba Ummie ne yay matuƙar wanke min zuciya. Mikewa nai cike da zumuɗi harda daka tsalle dan farin ciki, tuni na nema damuwata da tunanin wasu baƙi da ya ishi mutane da zancensu na ɗauki akwatin daya ajiye ɗin. Saman gado na kaisa na buɗe.........✍️

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
Chapter 22 · 0% Book details