← Book details Tangaras Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 10

Sashe 9

Tangaras Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan tanamasa magana cikin wannan sigar shiga Wani yanayi yake shiyasa baicikason zuwa inda takeba Domin dulmiya masa lissafi take, Ruby Kenan rubai'a wadda ke Ansa Sunan ruby danger gogaggiya, wayayya Kuma y'ar bariki Ruby bata ma'amala da k'ananun Maza sai manya Kuma Y'an siyasa masu k'ud'i, Ak'alla tayi Abortion sau 3 saidai yanzu tadaina gangancin d'aukar cikin ba iyanan tatsaya ba harda k'waya shisha takansha giyace kawai batasha Amma har kokin tanasha, Kuma tana taya manyan k'asar safaranta Saidai tanada wayau da matik'ar b'adda kama Domin indai zata fita cikin manyan hijabai take Sam bata fidda tsaraicinta indai bakasanta farin saniba to bazaka tab'a cewa itad'in ba mutuniyar kirki bace, A restaurant tahad'u da Uncle Sadeeq tinda taganshi taji cewar zata iya Auransa Musamman data samu labarin tarin dukiyar Mahaifinsa kuma kallo d'aya tamasa taji takwad'aitu dashi saidai bincikenta yanuna mata shid'in kamilin mutum ne koda tafito tanuna masa maitarta Afili bazai yarda ba kuma zata b'ata Shirintane Hakan yasa tarufe Ainahin siffarta tafito A mutuniyar kirki tadawo Rubai'a A idanuwansa cikin ikon Allah kuwa tasamu shiga domin tazoda equality's d'inda yakeson Macce, Maikyau, Mai boko wayayya ai Kuwa ruby duk tahad'a quality's D'in kusan harda deegri gareta b'angaren nazartar halin d'an Adam Hakan yak'ara mata gogewa da wayau, itad'in Y'ar Wani d'an Siyasace sosai yasagarceta da k'ud'i saboda mamanta tarasu shikuwa baicika zama ba, Hakan yabata damar shek'e Ayarta yarda ranta yakeso, takasance tamkar *TANGARAS* ga idanuwan jama'a zuwa shikanshi Uncle Sadeeq

Cikin wata d'aya Soyayya tayi k'arfi tsakaninsu har dazuwa gidansu yaga iyayenta sukayi magana Kuma sunbashi damar turo iyayensa,

B'angaren Uncle sani kuwa sosai soyayya tayi girma tsakaninsu da Ramla harma Abba yabada damar kowa yagabatar da Wanda yakeso,

Zaune suke gunda Akatanada Domin hutawa, Labarin cewar Abba yace yaturo iyayensa take Basa, sosai suka shagala da fira cikin Annashuwa da farin ciki,

Tinda yashigo da hancin motarsa gidan yahangosu ransa yasoma Suya kenan haryahzu tana Tareda guy nan waima wannan y'ar yarinyar za'a bawa damar kula samari A Fili yayi maganar tareda Jan tsaki

Dariya Sani yayi "wato big broo idan ba'a mata damar kula Samarin ba Kai zaka auretane? Kace baka Sonta babu soyayya sai Zumunci to kanme zaka shiga tsakaninta da masoyanta, yarinya kamar wannan ga Kyau ka diri ga Ado ga su....,"

"Is okay sani Ina ruwanka daduka halittar nata shin yaushema ka iya hango duka wannan Abun tareda ita Kenan kullum idanka Kanta yake? Banaso kada kasake Irin wannan Kuma wallahi Bai isaba shid'inma dole yarabu da ita ai y'ar uwatace inada damar bata Miji ni Sam wannan guy baimin ba wllh dole yarabu da ita," yak'arasa maganar yana taka Wani wawan birki Wanda Saida yajanyo hankalinsu zuwa garesa,

Duk k'ok'arin sani nadakatar dashi kafin yarik'osa tuni yafice ko kulle motar baiyiba kamar Wani kububuwa haka tahangoshi yanufosu ganin yanayinsa Saida gabanta yafad'i amma tadake tareda b'oye tsoronta, Amma tasakawa ranta yau kam bazata k'yaleshiba Saidai Ayi rigima Agidan

Yana isowa ga mamakinta saitaga fuskarsa tasauya zuwa murmushi tareda sallama yana mik'awa Hydar Hannu Alamar gaisawa shikansa Hydar yayi mamaki Amma ya danne yabashi suka gaisa itakam sake Baki kawai tayi tana kallonsa mamaki

"Am Abokina bata fad'a Maka gaskiya bane, Dana sake ganinka yanzu ma,"?

Kallonta Hydar yayi cikin mamakin kafin yamaida kallonsa ga Uncle Sadeeq yace"Mekenan bata fad'amun komai ba,"

"Haba gaskedai Domin nasan saidai kayi k'ok'arin Aikata Zunubi cikin Rashi sani Domin dai ga Alama kanada ilimi Kuma nasani sarai kanada tarbiya maikyau, to Atak'aice dai Anbayar da ita gawani so kasan dai Neman aure kan Aure haramun ne,"

Cikin tsananin mamaki da tsorata Hydar yamik'e tsaye yace"Kamar ya Anbayar da ita bayan yanzu haka take fad'amun Abba yace naturo itayena Kuma zakazo da kalan wannan maganar, my love kinajin Abunda yake fad'a shin hakane,"?

Shi kuwa Sadeeq haushi yabashi wai my Love
Dan k'wafa yayi tareda cewa"itace takeda iKon kanta wai kodai bakasan matsayina garetaba inada Ikon Bada so ni nariga namata mijin bakai zanbawa ba so kawai kayi hak'uri Kuma katashi kabar gidanan daga k'arshe Kuma Ina gargad'inka kada kasake dawowa gidannan, idan Kuma kak'iji bazakak'i ganiba,"

"Wai meye Hakane Uncle Sadeeq waimeke damunka ne, nasha fad'a Maka dakafita Rayuwata yanzu Bada bane wallahi baka isa kayimin katsalandan Acikin Rayuwata ba kaiba Ubana bane saboda haka ninakeda damar zab'ar Wanda nakeso Kuma shi nakeso Saboda haka babu Wanda ya Isa ya......,"

Marinda yasauka fuskartane yasata kasa k'arasa maganar, kafin tadawo hayyacinta Ansake d'auketa dawani d'agowa tayi cikin zafin marin domin ganin waye yamata wannan Abun, Abun mamaki saitaga Uncle Aliyu sai cika yake yana Hura hanci, Uncle Sadeeq yarik'eshi yana bashi hak'uri domin ko dukan farkon daya mata Saida yaji zafinsa A Zuciyarsa,

"Shashashar banza dawufi Muna ganin kamar kinyi hankali Ashe da Saura Dan bakida mutunci Sadeeq daya gyara Rayuwarki harshi ya iyajin Sonki shizakiwa rashin kunya cikin Mutane Kuma Agabansa, Ashe Rashin kunyar naki da tsiwa sunanan, ai laifinkane Yanzu daka daina dukanta ai ko Yanzu bata wuce dukanka ba kayimata shegen duka mana, Kai Kuwa kamar yarda ya fad'a Maka Hakanne kayi hak'uri kasamu wata munyi mata Miji ni yayantane Uwa d'aya Uba d'aya kai shi Sadeeq D'in yafini iKon da ita saboda shine ya Haska Rayuwata, Ina k'ara jaddadamaka dakayi hak'uri Allah yabaka wata Amma kafita Hanyar khadjiya,"

Cikin mutuwar jiki Hydar yace"nagode" yajuya nufe motarsa yana k'ok'arin barin gidan, Zuciyarsa tana suya Domin khady tajima dazama *TANGARAS* gareshi

Kuka Khady tasaki da k'arfi tana k'ok'arin bin bayansa Amma uncle Sadeeq yayi saurin rik'ota da k'arfi takasa Zuwa inda Hydar sosai take kuka tana Kiran Hydar tanason k'wacewa daga rik'on dayamata Amma takasa tanaganinsa har yashiga motar yabar gidan,

Wani kukan tasaki da k'arfi tareda k'wace hannunta idanuwanta suna zubda hawaye Sosai, takallesa cikin kuka tace"Natsaneka! Natsaneka!! Natsaneka!!! Wallahi Natsaneka fiyeda yarda natsane mutuwata Kuma ko.....,"

Sake marinta Uncle Aliyu yayi yana fad'in"kasakeni na ba'lla wannan yarinyar shashashar banza dawufi wadda batasan gataba,"

"Eh Uncle bansan gatan ba Kuma banaso indai gata daga gurinsa nace banaso kuma, gaban kowa zan fad'a Natsaneshi mugu Azzalumi Kuma wllah babu Wanda zairaba soyayyata da Hydar,"

Dagudu tayi Cikin gidan tana kuka sosai,

"Kagani ko tagama fitsare k'afarta kabarni namata shegen duka, Kuma bari Abba yadawo wllh indai inada Iko da ita wllh bazata Aureshi ba,"

Dak'yar dai shida sani suka samu ya sauka daga fushin,

Sashensa kawai yanufa tafeda zamewa ya zauna kan kujeran d'aki yana Rintse idanuwansa kukanta yakeji Harcikin ransa kalmar tsanarga gareshi kuwa jiyake kamar tana watsamasa wuta Acikin Zuciyarsa,

"Wllh kanasontane Abokina idan baka Sonta bazakiyimata wannan zazzafan kishinba idan baka Sonta bakazaka damu da saurayintaba idan baka Sonta bazaka shiga lamarintaba Wllhi kayarda kawai kanasonta kawai kakasa fahimtar Hakan ne saboda bakasan so ba, takasance *TANGARAS* gareka,"

"Amma idan kace inasonta to ita Rubai'a fa? Sam Abunda nakeji kan Rubai'a banaji kan wannan yarinyar baso bane kawai k'ok'arin gyara mata Rayuwa ne banason tashiga matsala saboda itad'in Amanace gurina ko kafin mutuwar mahaifinta Saida yabani Amanarta haka itama Mahaifiyarta tanada Saka Rai gamedani ninafi cancantar bata Mijinda Zata Aura,"

"To wai wazaka bata ta Aura D'in kanada Wanda kasan halinsa 100 percent ne? Kanada Wanda kasan bazai cutarda maraicintaba, Sadeeq kadaina yaudaran Kanka duk kalan namijin da kake son bawa khady bakadashi idan kuwa dakwaishi to baiwuce Kaine ba dakai tafi Cancanta,"

Wannan karon zubamasa Ido kawai yayi yakasa magana Domin dai yanada gaskiya bashida Wanda zaice gashi ya Aurata, shikuwa bazai Auretaba domin yanada Wadda yakeso shifa Rubai'a yakeso dolene yayi dogon tunani kan lamarin Kuma bazai tab'a Yarda ta Aure Hydar ba,

"Subhanallah wai meke faruwane khady waya tab'amun ke,"?

"Ba Uncle Sadeeq bane yana daga cikin Dalilin da yasa nabar gidan Nan kika dawo dani dole yanzu gashinan saifaman shiga Rayuwata yake, Kuma shine harda koranmun masoyi yakore Hydar wallahi ni bazan yarda ba bazan k'arb'e zab'in nasaba Domin shi ba Ubanane,"

"Eh lalle shiba Ubanki bane Amma kisani ya isadake wallahi khady muddin kikaci gaba da wannan lafiyar da taurin Kai Wllhi wahala zakici Dan Ubankine,"

Fad'awa d'akinsu tayi tana kuka,

Gaba d'aya ranar bata fito wajeba ko Abincin K'unci tayi kuka kawai take Domin wayar Hydar kashe take,

Meeting na Musamman Abba ya had'a dukansu suka taru harda mamanta dasu uncle d'inta

Gyaran murya Abba yayi tareda cewa"Kai Sadeeq meye hujjarka nakorawa mamana samari bayan Anbashi damar yafito,"

Kansa Ak'asa yace"Abba wallahi baidace da itabane shiyasa yadace Ace Anbata Miji nagari wadda zaisata manta maraicinta Wanda Kuma yasan Mahimmancinta,"

"To wai Saddeeku Ina zamu samu wannan mijin tinda dai har gawanda yakesontan kabari ta Aure Abunta mana kaimafa Nanda sati d'aya Auranka kaidasu Ramla dukanku zakuyi Auren kanme ita zaku barta gidan bayan ga Wanda takeso, saifaman nanata maganar baidace da ita kake ba to wai waya Dace? Kuma Ina zamusoshi Kuma wayeshi Wanda kazab'a mata D'in,"?

Shuru yayi kansa k'asa Domin dai baida Wanda zaibata Amma dai Kuma Hydar baidace ba,

"Kayi magana magana mana kayi Shuru idan bakada Wanda zaka bata Kuma bakada Dalilin hana Auran to wallahi baka isaba," cewar Umma

"A'a Umma bari nagaya muku gaskiyar maganar bawani Wanda yadace face shi Sadeeq D'in shizata Aura Domin shine Daddy yazab'a mata bazan mantaba shine rok'onsa na k'arshe kan Sadeeq ya Aureta Domin shine kawai zai iya tallafan Rayuwata Saboda haka bawani ja Inja shine mijin nata,"

"K'warai kuwa nikaina nasan wannan Domin yasha fad'amun Hakan tinkan ciwon Ajalin yasameshi saboda haka indai nima Uwartace inada iko da ita to Shakka babu jibin dukansu zai aura mata 2 lokaci d'aya Kuma Rana d'aya,"

Gud'a hajiya kaka tarangad'a Tareda fad'in"Alhamdulillah Aikuwa wannan Abun Farinciki ne, Koda Bakiyi rantsuwa ba tinda wasiyar Mahaifintane ai Auren babu fashi, Kaga sai Ayi bikin duka tare,"

Shikanshi Maganar tazo masa Abazata yadaisan basonta yakeba, Kuma bazai iya kasa cika burin Mahaifintaba Koda yana raye balantana yamutu, to Yanzu tayaya zan fuskance Rubai'a da wannan zancen bayan yasan tanada kishi kansa Sosai,

"Kai Sadeeq ka tabbatar Haka lamarin yake,"

"Eh Abba wallahi babu k'arya Aciki"

"To shikenan Allah yakaimu lokacin Kuma kayi k'ok'arin sanarda ita Waccan D'in Tareda danginta da tinfarko nasan da wannan ai dabazan bari Ayi maganar da itaba,"
Chapter 9 · 0% Book details