← Book details Tangaras Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 10

Sashe 7

Tangaras Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe maikyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM TAKUCE🥰🥰*

................................✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓

........................

*INAAA KUKE MATA IYAYEN KWALLIYA DA GYARAN JIKI?? INAA MASU BUK'ATAR GYARA FUSKARSU DAMA JIKINSU? SHIN KINASON RAGE GIRMAN CIKINKI TO KU HANZARTO DOMIN SAMUN NAKU KODA KUD'INKA SAIDA RABONKA MAMAN TEEMA AND MORE 08100100821......... INAAA MASU FAMA DA MATSALAR RASHIN HAIHUWA? INA MASU FAMADA ULCER? INA MASU FAMADA K'IBA ANA NEMAN ARAGE? INAMASU JIKI SIRANTAKA ANANEMAN YIN K'IBAR? INAAA MASU FAMADA SIKILA? INAMASU FAMADA CIWON JIKI?? KAI DUK WANI WANI CIWO DA ALLAH YA HALARTA ADUNIYA TO YAYI MAGANINSA DAN HAKA KU HANZARTO AGUJE DOMIN SAMUN NAKU MAGANINMU BASHIDA MATSALA YASAMU KARRAMAWA DOMIN TINDAGA CHANA YAFITO GHT KENAN KABADA KUD'I MUBAKA MAGANIN MATSALARKA IN SHA ALLAH... HAKA MASU NEMAN MAGANIN MATA KO WANNE IRI AKWAI WANDA HARSAIKIN BADA LABARI HUNNNMMM RIGIJI GABJI WASU KAYA SAI AMALA KAWAI KUYI MAZA KIYI MAZA KAYI MAZA HAD'UWA DA MAMAN TEEMA DOMIN SAMUN MAGANIN MATSALARKI KO WACCE IRI 08100100821 ITACE NUMBER TA DOMIN HAD'UWA DANI KUWA NI MARUBUCIYAR LITTAFAI HAUSA KATUNTUB'I WANNNAN 07064904617 MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM)*

```Gamasu buk'atar A tallata musu hajjarsu k'ofa bud'e take zaku iya Aiko tallanku A rubuce nasaka muku cikin shafin littafaina Akan farashi Mai sauk'i, .. Inakuke Y'an kasuwa Kuma kuzo Inayin logo graphics ko wanne iri had'ida cartons Art's design kudai kugarzayo domin mallakar naku cikin sauk'i...... Domin magana dani A WhatsApp 07064904617 OR 07031012948 ✍️ Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 Queen 👸 of Writer's Hausa novels 📚📖📚 And design graphics```

_Sunday 20/4/2025 April_

*FREE PAGE 31 TO 40*

*SECOND THO THE LAST FREE PAGE IN SHA ALLAH*

....................... Dawowa office d'insa yayi Rai b'ace Kiran sallah dayaji yasashi shiga masallacin school D'in yayi sallah baiko Jira Uncle sani yadawo Abunsa hakama lokacin isha yanayi yadawo, biyo bayansa sani yayi samunsa yayi tsaye yana zagayen d'akin

"Wai Abokina meke faruwa ne gaba d'aya daga d'azu zuwa yanzu duk kafice hayyacinka Damuwa tabayya kan fuskarka, shin meke faruwane dakaine daga d'azu Zuwa yanzu,"

Ko kallonsa baiyiba balantana yatankasa Kuma yanajinsa sarai,

"Nifa shine Abunda kesaurin gamani dakai wannan Bak'in miskilancin naka Kanaji Anayimaka magana ka share Mutum da gidan sarauta kafito wallahi da Akwai matsala ga bak'ar Zuciya saikace kuturu wllh ba fata nake Maka ba Amma watarana wannan Halin naka da Zuciyarka saisun sakaka kuka," fuuuuu yafice cikedajin haushinsa

Binsakawai yayi da kallo harya fice zama yayi kan kujeran yana dafe Kansa , Sosai yasani Abunda sani yafad'a masa gaskiya ne to wai meyasa yayiwa sani hakan bayan duk makarantar babu Wanda ke nuna soyayya da kulawa garesa tamakar shi, wai meke damun Zuciyarsa ne, tinawa da hatsarin inda yakai Khady yasashi mik'ewa zumbur kamar Antsikareshi cikin sauri yafice yanufe Gardiner D'in lokacin ko Ina yayi tsittt kowa yalafe Domin sanin makarantar tanada iska shiyasa kowa yake kama kansa idan dare yayi,

Hafsat kuwa ganin babu Queen khady babu labarinta Abun yasoma d'aga Hankalinta kowa tatanbaya saiyace d'azu dai yaganta da Hydar, sanin duk inda Khady take bazatakai magariba wajeba dole tana hostel Hakan yasa cikin Damuwa tajeneman Hydar Saidai Cikin rashin sa'a tasamu labarin Hydar yawuce dama baya kwana hostel Wani sa'in saiko in Exam zasuyi Wani sa'in yakan tsaya Amma ba kullum ba Domin yafi gane yakoma gida. Hydar d'angarin Kano ne HND ne yakawo shi school D'in, tinda ya d'aura idansa kan khady yaji Sonta Ahankali itama harta fara sonshi yanzu kam School D'in bawanda baisanta dashiba, baban Hydar d'an kasuwane Mai k'ud'in gaske wannan yasa Shima yake cikin manyan makarantar saidai k'ud'i Basu Saka Hydar lalacewar ba yanada kamunkasa, cikin tsananin damuwa tadawo hostel d'insu lokacin Anayin sallan magarib ganin batadawo tace"Hajara wai Dan Allah bakuga Koda giftar Queen khady ba Yanzu bayan nafita," kamar zatayi kuka take maganar domin dukta tsorota

Wadda Akakira Hajara tace"Wllh Hafsat Bangantaba wai haryanzu Baki ganta bane,"

Bata samu damar magana ba saboda hawayenda suka soma zubomata,

"To kifad'awa Yayanta mana Uncle Sadeeq,"

"A'a Hajara banson yasani Saboda kinaga bamusan Ina takeba kada mujanyo mata Wani rikicin damacan babu jutuwa tsakaninsu Kuma kinsan dama shi Bai d'aukar nonsense Kinga kada muzama silar faruwar wata matsala kuma,"

"Lalle kam kinada gsky hafsat, Amma kunsan me batareda kowa yasani ba muje cikin school D'in mudubata,"
Cewar nafee

"Idan mudace mudabata ta Ina zamufara,"

"Muduba ko Gardiner ne kinsan ruwan Nan sunk'are duka wai Koda taje D'iba, dama na lura khady Akwai kafiya bata tsoron shiga gurin,"

"Tabbas kuwa Hakan zata iya faruwa Domin tasha cemin muje shan iska nak'i kuma itama na hanata zuwa,"

"To muje kawai,"

"Amma zuwanmu gurin babu matsala kuwa kundaisan da iska Sosai gurin,"

"Nidai wallahi Koda bazakuba ni zani bani buk'atar kowa yasani Saboda kada Uncle Sadeeq yaji," cewar Hafsat tana fita d'akin dagudu tanife Gardiner D'in, Saida suka gayyace wasu suka K'ara yawa kafin sukaje, Hafsat tashiga tana waigege can tahangota, kwance Da sauri tak'arasa gurin ganin halinda take ciki yasata sakin ihu Tareda fad'in "kuzo kutaimaka mana gatanan kwance wallahi,"

Aida sauri suka shiga, d'aukota sukayi sukawuce hostel da ita, kwantar da ita sukayi kan gadon hafsat kuka kawai take,

"Yanzu yaya zamuyi da ita kenan kiduba harda jini A bakinta guma gawani ga goshinta, Anya bazamu kira Uncle Sadeeq ba,"?

"A'a bazamu kirashiba saboda bamusan meya faruba, musaka mata ruwa dai ko sumane tayi," Hafsat tafad'a tana tashi d'auko ruwan Saida tazuba mata Ruwan sosai kafin taja dogon numfashi saidai taka Bud'e idanuwanta saboda ciwonkan da takeji Sosai,

"Queen meke faruwa Dake waya Miki Hakan,"? Tajiyo maganar Hafsat cikin muryan kuka tana kamamata Hannu,

Cikin k'arfin Hali tasoma k'ok'arin Bud'e idanuwanta Amma takasa saboda su kansu zafi suke mata,

"Kingani nace kibari mukira Uncle Sadeeq saboda tanajin jiki sosai,"

Cikin k'arfin hali takama Hannun nafee Tareda girgiza mata Kai Alamar A'a,

"Kingani ba ko ita batason yasani kawai mubari zuwa safiya saimu Kira Hydar" da wannan shawaran sukakai k'arshe..

Uncle Sadeeq Kuwa harda gudunsa ya isa Gardiner D'in saidai Abunda yak'ara tayar masa da Hankali babu ita Anan gaba d'aya Kuma gajini gurin, sosai ya tsorata gashi darene balantana yaduba ko taje hostel cikin fargaba da tsoro yakoma saidai har gari yawaye Sam Bai runtsa ba,

Tinda safen Kuwa Hafsat tashiga Neman Hydar cikin sa'a kuwa yazo school dawuri cikin tashin hankali suka d'auketa zuwa Asibitin, treating d'inta Akayi Tareda Saka mata ruwa dama jini, cewa lakitan yayi k'anwarsa ce K'aramin hatsari tasamu cikin makarantar, Kasancewar Hydar nada k'ud'i Akamasa komai babu dogon bincike Saidai dr D'in yafad'a musu tana buk'atar kulawa Kuma idanta yasoma tab'uwa saidai Abun baiyi tsanani ba Amma zata buk'ace glass saboda lafiyan idan nata, dukansu suna jungun sukayi har 12:00 na safe kafin tafarka Sannu suka shiga mata, Hydar yasiyo Musu Abinci da Abubuwan Amfani da taimakon Hafsat tamik'e tashiga toilet tawanke baki Tareda yin Alwala Saida tayi sallah kafin tad'anci Abincin kad'an koshi Saboda Hydar yamatsa, duk Yarda suka matsa kan suji labarin bata fad'amusu gsky ba kawai k'arya tamusu itadai Hafsat bata Yarda ba, Hydar kuwa yayarda sai faman mata Sannu yake,...

B'angaren Uncle Sadeeq Kuwa kasa hak'uri yayi Saida yaje Nemanta Nan wasu daga Cikin student D'in suke bashi labarin Irin mugun yanayinda Aka sameta Amma suntafi da ita Asibiti,

"Waya tafi kaita,"

"Sunsanshi Hydar"

"Waye shi,"

B'oyemasa Gaskiyar sukayi kawai sukace taimakonsa k'awarta tanema yakaisu Kuma ganin mugun yanayinda take ciki shiyasa sukafice da ita da sauri

Baiyi maganaba yadawo wajen tsaya Zuciyarsa sai tsalle take Domin yanason sanin halinda take ciki,

Acan kuwa bayan tasamu sauk'i suka sallameta, sukanufo school D'in tinda yaga Motar tanufo Hostel d'in yamik'e fitowa sukayi inda sauri Hydar yabud'e mata tafito A hankali tasoma tafiya yana daga bayanta yana mata Sannu Hafsat Kuwa tad'auko sauran kayansu daya Siyamusu, tuntub'e tayi tayi baya zata fad'i cikin Sauri suduka biyun har Uncle Sadeeq D'in yanufosu da gudu saidai Hydar yafi zama kusa shine yasaurin tarota tafad'a Ajikinsa, yana mata Sannu "Kinga Hafsat bani Kayan kitaimaka mata kushiga ciki,

Rik'eta tayi takwanta jikinta tanad'an rufe Ido suka soma tafiyar

Shikuwa ganin Hydar yarik'eta A k'irjinsa jiyaki kamar yasamesa yashak'e wuyansa saiya Mutu, Lokacinda yake mata Sannu gurin kunneta kuwa ganin yayi kamar Wani Abun daban yake fad'a mata,

Dakewa yayi tareda saita natsuwarsa,

"Kinga ga Uncle Sadeeq munshiga Uku mezamu cemasa"

"Kada kitsaya Dani inda yake kada ki kulashi muje kawai barshi,"

Hydra ne kawai yatsaya suka gaisa da k'yar ya iya Ansa gaisuwar tasa, saidai Hafsat ma tagaidashi ya Ansa itakuwa ko kallonsa batayi ba Kuma k'ok'arin tafiyarta kawai take,

Tsaye kawai yayi yana kallonsu har suka isa tad'an jingina Tareda yiwa Hydar godiya Hafsat tak'arb'e kayan shikuwa yadawo inda Uncle Sadeeq yake tsaye Hannu yabasa Alamun sugaisa kamar bazai Ansaba Kuma yabashi, Labarin komai yabashi da kulawanda Dr yace Abata,"Okay thanks" kawai yafad'a yajuya yabarshi sake da Baki, Amma yana zargin da Wani Abu Mai kamada kishi Taredashi,

Saidai yasaita natsuwarsa dakansa yaje yabawa Abokinsa hak'uri suka sake Shiryawa, saidai yamasa nasiha sosai kan Zuciyar tasa,

Duk k'ok'arinsa nason sake ganinta dayin magana da ita Abun yaci tura Domin duk wata hanyar da zata sadasu Saida tarufeta sosai shikuwa yashiga damuwa Musamman daya gano Hydar saurayintane ,
Chapter 7 · 0% Book details