Sashe 5
Surbajo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
inda yake aurar da yarsa Safiyya yar kimanin shekaru goma shadaya Su surbajo sune kawayen Amarya sabida suma shekarunsu sha dayanne ga alada ta Fulani akwai wani wasa dasukeyi bayan shadi inda maza da yanmatane zasu taru suyi layi layin maza dabam haka namatama zasu fuskanci juna suna wakar Wayyohoro hirobe gadaibe jadu jande wayyo horo hirobe gadaibe jadu jande. Seme kalangu yasa kida to matanne daya bayan daya zasu dunga fitowa su tsaya a tsakiyar filin se tagama kallon samarin Wanda yamata acikinsu shi zataje ta yalo da kafarta yin hakan nanufin tanason yafito suyi rawa kenan kuma yawanci daga wannan rawarne soyayya take shiga tsakani hartakai ga aure to wannan bikinma anshirya irin wannan wasan Danhaka surbajo taruga kowa zuwa gurin sabida tanada gaba sabida basa son arugasu zaban jae sabida a alada irinta wasan duk Wanda kika zaba fita zakuyi tsakiyar filin kuchase sosai to inkuma yaji yanasonki zece kufita afili kusami guri kuyi mgn fili yacika bamazanba ba yanmatanba su kuma mazan kowa burinshi Allah yasa surbajo tazabe shi Dan itama duk yanmatan garin tafi kowa kyau anfara waka inda surbajo ce farkon fitowa tashigo filin tafara rawar Fulani irin wacce ake daga kafa dayannan ana saukewa sannan takarewa mazan kallo can idonta yasauka akan jae yanamata murmushi ayko batayi kasa agwuiwaba ta yaloshi ihu yayi sannan yashigo filin da kwambe suka fara rawa tare inda me kalangu yadunga wasasu dacewa kyakkyawa se kyakkyawa bayan sungamane jae yacewa surbajo Sudan fita afilin ay sauran yanmatan naganin sunfita kowacce haushi yakamata inda sukasha alwashin se summa surbajo dukan tsiya akan yaloshin datayi hakade yanmata da samarin suka ci gaba dawasansu har suka gama itako surbajo tunda jae yace sukebe farinciki yabi yacikata dantasan yau tafi kowa saa a duniya koda suka keben juya mishi baya tayi alamun jin kunya shimade kunyar yakeji Danhaka shima bayan yajuyamata sannan yafara mgn wato surbajo nadade inashonki amma nakasa fadamiki segashi yau Allah yakawo ranar dazan sanar dake danhaka Do Allah do annabijjo kishe kina shona.nide aradu ina shonki kunyace da dadi suka rufeta Dan haka ta ranta anakare takoma gurin arera gudun datayi shiyabashi tabbacin tanasonshi Danhaka agurin yafara rawar cin nasara Dan yasan yama mazan garin nisa maman yusuf [3/18, 11:54] Zahra muhd mahmud💃: 🍀🍀🍀🍀 🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *fans muna barar adduarku yaron da bashida Lafiya Allah yamasa rasuwa to kutayamu da addua Allah yajikansa yasa meceton iyayenshine sukuma iyayenshi Allah yabasu hakurin jure rashin sa ,rest in paradise my baby* *page 10* Tundaga wannan lokaci syy me karfi tashiga tsakanin surbajo da jae ko kadan basa son rabuwa da juna Yauma kamar kullum jae yazo hira gurin surbajo Akan wani ice suka zauna yayinda surbajo tajuyamasa baya sabida kunya Gyada takawomusu da burodi sunaci suna hirar Can jae yace surbajo aradu inna aureki nahaye nasan duk garinnan se andunga hirata saboda na auri sarauniyar mata Dariya tayi tasake rufe fuskarta sannan tace aynima hakanne Dan yanzu haka yanmatan garinnan haushina sukeji Dan rannan munje kiwo nida arera su haulen gidan ku suka tsareni wai sesunmin duka ayko nida arera muka hadu mukaimusu dukan tsiya dariya yayi sannan yace hauka sukeyi nibance inasonkowa acikinsuba shima Baffa cewa yayi inzabi wacce nakeso inde agarinnanne ze auramin nikuma nazabeki Dadine yarufe surbajo harseda sautin dariyarta yafito hakade suka gama hirar wacce yawancinta cin gyadar yafi yawa **************************** Al ameen yanzu yafita harkar Aisha kwatakwata harkar gabanshi kawai yakeyi yayinda mahaifansa zuwa yanzu sunfara bashi shawarar yakara aure kuma yabasu tabbacin ze Kara yana neman wacce yake sone fatan alkhairi suka masa alameen anturashi wani course kasar amurka inda seda yakwashe tsawon shekara guda acan yanzu idonshi yakara budewa ya waye fiye da tunaninku ko maganarshi yanzu tasauya Alameen Kenan Dan kimanin shekaru arbain da haihuwa amma babu me ganinshi yayi zaton yakai hakan Aisha ma yanzu bata da lokacinshi Dan yanzu tazama yar business Dan haka kasuwancinta yafiyemata komai Mahaifiyarta tanasane da irin tsiyar da Aishan take tsulawa agidan miji amma kda wasa bata taba tsawatarmataba sabida gudun kar abin arzikin da Aishan take kawomata tadena Su Ruky suma kullum cikin bata munanan shawara suke inda ahalin yanzu har sata takema alameen din yasan tanamishi satar Amman ko afuska be nunamataba Dan yafuskanci bata da wadataccen hankali *************** surbajo Ankara zama yanmata inda yanzu shekarunta sha biyu da haihuwa Dankaka yanzu sumaye har tallan nono da fura take doramata tabi yanmatan rugar sukai cikin garin makarfin ranar dabata siyarba dukan tsiya take mata shiyasa surbajo bata dawowa gida da wuri matukar tasan bata siyarda nononba Se tara nadare take baro cikin garin kamin tagama keto dajin ta iso rugarsu goma tayi haka baffanta zetamata fada itade sede tai tabashi hkr itakuma sumaye na zugashi da cewa maza tafara bi shiyasa take dare bata dawoba itade surbajo sede kuka wasawasa seda kaiwa dare agurin talla yabi jikin surbajo sabida bata da kan kasuwa Dan wani lokacin setakai laasar baasiya ko na kwaboba gashi nonon yafi Nakowa yawa acikin wainda suke zuwa tallan tare duk sanda ta dawo se baffanta yazaneta sannan yamata fada akan dolene setayi cinikin inbata siyarba ta dawo mana inya tambayi sumaye ko itace take cewa surbajo karta dawo seta siyar munafukar har kuka take sawa tace haba alhaji yazaayi nacemata haka koban haifeta ba ay yatace kuma nasan hatsarin dake tattare da hakan da irin wannan kalaman take Rufe bakinshi insuka koma daki ita da surbajo tashaketa takuma ce wlh inkika kuskura kika dawo gidannan baki siyarba yankaki zanyi itade sede tayi kuka tafadawa Allah jae yasha yimata juyen nonon yabiya kudin Dan kawai tasamu taje gida dawuri to yau da gobe tafi wasa ba koyaushene yake da kudin juyenba seyafara rakata tallan sui ta yawo agari har su samu asiye haka sukeyi sunfi karfin wata guda suna zuwa tallan tare kwatsam rannan se sukayi kwantai basu sayar da wuriba ranar basu dawo gidaba se goman dare lokacin Baffa yafito yabi hanya yagani meyasa bata dawo da wuriba dayake basu San jae narakata tallanba seganinsu yayi tare suna tahowa tsawa yadaka musu yace daga ina kuke cikin darennan tsugunnawa sukayi sannan sukace daga talla wankesu yayi da Mari duka lokaci daya sannan yace nizaku maidar yaro wato dama abinda innarki take fadamin akan maza kikebi Ashe da gaskene to wlh yau zaki gane kurenki kaikuma zanga baffan nakane wawa kawai kekuma munafuka shige mutafi dagudu tamike tayi gaba Tana kuka koda isarsu gidan yaba sumaye labarin abinda yafaru cewa tayi ay gwanda dakagani da idonka Dan Dana fada baka yardaba aygashinan ranar seda yama surbajo jinajina inda yakara da fadin gobema ki kuma kaiwa dare awaje wlh Sena yankaki na huta kuma tallan nono bazaa Dena doramiki ba sabida aladarmuce kowacce yarinya tanayi Danhaka yazama dole kema kiyi daga yanzu in magaruba tamiki awaje ki kuka dakanki haka taci gaba da Kukanta har zuwa washe gari batayi bacciba maman Yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *page 11-12* Alameen yadawo hutu inda yasamu labarin anyi rasuwa akano zasu tafi gaisuwa duka family dinsu Ayko haka suka rankaya gaba dayansu harda matar kabeer da yaransa gabadaya ran alameen ne yabaci ganin batashi matar acikin ayarin Mota biyu sukayi kabeer ke Jan motar da iyalinshi suke ciki yayinda alameen kejan wacce iyayensa da kannansa suke ciki Dan be tafi da excode dinshiba sabida gaisuwa zasu Sun isa kano Lfy sunyi gaisuwa an karbesu cikin mutunci da karramawa Seda laasar suka kamo hanyar dawowa gida Dan ba kwana zasuyiba ************** Surbajo yau dawuri ta shirya ta tafi tallan nono Dan Tana gudun tayi dare kuma tasha alwashin yau intaje talla rokon mutane zata dungayi akan su siya Tayi kwalliyarta cikin kayansu na Fulani inda fuskarta tacikata da digedige duk asunan kwalliya bakinta tacikeshi da bakin kwalli gaba daya dan Tana tunanin rashin yin Kwalliyar ne yasa baa siyan kayanta sallama tayiwa sumayen tadauki kwaryar nonon ta wuce Koda tazo cikin gari jamaa bame bitakanta bare asiya kota rokesu basa siya Dan haka kuka tasa taci gaba da bin mutane akan su siya haka tadunga bi kwararokwararo akan asiyi nonon mutum Hudu ne kawai suka siya ga nonon da uban yawa haduwa tayi da Mari yar rugarsuce ita har ta siyar tambayarta tayi Don Allah Mari ina kike kai nono da furarki asiye Dan Allah kifadamini Murmushi tamata sannan tace aradu da nisa Dan sekin hau mota naira dari zaa kaiki a akori kura Dasauri surbajo tace fadamini Dan Allah aradun Allah zani Tashar yarine tabata amsa daganan tajata takaita inda zata hau motar Godiya sosai surbajo tayi mata tahaye motor akori kuran suka tafi ************** Alameen tafiya suke suna hira cikin nishadi sabida daddy bayason gudu amota shiyasa ahankali yake tafiya sabanin kabeer Wanda yakusa shiga kaduna Dan cewa yayi baze iya tafiyar wahainiya ba suna zuwa tashar yari tayansu Yay faci dole Al ameen yay parking agefen titi dede wani masallaci gurin akwai jamaa sosai kamarde kasuwa fitowa yayi Dan yanemi Mesa iska yasamusu suwuce agefe yaga Mesa iskar Danhaka yace yazo yasamusu dasauri Mesa iskar yasakamusu sabida ganin dankareriyar motor dasuke ciki 1k alameen yabashi mutumin se godiya yake karaf a kan idon surbajo hakan ta faru Dan haka dasauri takaraso inda alameen keshirin shiga yatada motor dasauri tace sannu bawan Allah Don Allah kataimakeni dasauri alameen yajuyo jin zazzakar murya namishi mgn arba yayi da surbajo dauke da kwaryar nono akanta durkusawa tayi tana kuka tace Don Allah kataimakamin kamar yadda Allah yataimakeka kasiyi nonon nan da fura wlh inna koma dashi bansiyarba yankani zaayi kuma inna Dade agurin tallan Baffa yace seya yankani takara rushewa da kuka alameen mamakine yakamashi to inbanda haukar fillo shi mezeyi da fura da nono dahar zata ce yasiya motarshi yashige yana shirin tadawa dagudu surbajo tasha gaban motor tana kuka tace cikin kuka haba bawan Allah Allah fa nahadaka dashi kaji tausayinamana Don Allah hankalin daddy ne yakai gurunta mamakine yakamashi Dan haka dakatar da alameen yayi sannan yabude kofar motor yakirata karasowa tayi jikinta har rawa yakeyi mommy ce tafara mgn dacewa yanmata Lfy cikin harshen fulatanci kasancewarta mommyn bafulatanace cikin Yaren fulatancin surbajo tabata amsa dacewa taimako nake nema akan asiyi nono da fura Dan inna koma gida yankani zatayi inbansiyarba inkuma najima agurin tallan Baffa