← Book details Surbajo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 26

Sashe 10

Surbajo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sanyi danko kayan fadan kishiya daaka bata batabi takansuba kawayentane suka dau na dauka itama suka zabarmata Wanda zata sa in amfara bikin ********** Surbajo Tunda alameen yatafi yabarta kullum cikin tuno abinda yamata takeyi itade batasan sunan abunba amma in tatuno abun namata dadi har addua take Allah yasa yakara yimata 😀 Ardo sosai yake shiri shima Dan tun ana sauran sati guda bikin kullum se an kwantar da sa anyanka dangin maman surbajo suma baa barsu abayaba sunzo bikin kwansu da kwarkwatarsu suma sunyma surbajo shatara ta arziki *RANAR BIKI* ranar asabar 31-12-2011 dubban jamaa suka shaida daurin auran Zahra Muhammad mahmud (wato surbajo)tare da angonta alameen jibrin sulaiman daurin auran dayasami halattar manyan shuwagabanni da yankasuwa uwauba sojoji manyansu da kanana Ko ina kakai dubanka alummane tako ina ranar garin makarfi bamasaka tsinke sabida yawan alumma ga jiniya takoina natashi kowa mamaki yakeyi me alameen zeyi da surbajo yar kauye kamar haka hakade akagama taron daurin auren jamaa suka fara watsewa Dayake tare zaa wuce da Amarya tuni motocin daukar Amarya sunfara dibar jamaa Inda yawancinsu mutanen kaduna ne sabida ardo yace yana gudun kauyancin yan rigarsa shiyasa masu natsuwar kawai aka dauka Amarya survajo wacce ke nade cikin wata lafaya Medan karan Kyau da tsada se kuka takeyi sabida rabuwa da gida dazatayi ammafa tayi kyau sabida wata yarinyar yayan mamanta me suna Bilkisu dasuka zo daga kaduna itace tayima surbajo Kwalliyar duk da ita surbajon bataso Amman seda akayimata kuma tayi kyau farinta yafito sosai Sumaye tajima Tana yiwa surbajo fada akan zama da miji haka yan uwan mamantama sunmata fadan sabanin ardo da kukan da surbajo takeyi yakeson sashi kuka dakyar yaiya cemata surbajo aure ibadane kiji tsoron Allah.... Hawayen dayake tarewane suka kubce dsauri yabar dakin dabaze iya jure ganin kukan surbajoba dakyar aka ja surbajo zuwa gurin motor dazata dauketa wacce ango alameen yake ciki yana jiranta yayinda Usman ke zaune agaban motar shida driver abaya alameen ke zaune se motoci guda hudu biyu gaba biyu baya sunsa motor atsakiya excode dinshine bayan motor aka budema surbajo tashiga dakyar Tana shiga takifa kanta akan cinyarta tacigaba da kukanta bata lura da alameen dake gefentaba tuni motocin suka fara tafiya ana jiniya Usman dake gaban motar ne yajuyo yana fadin haba amaryarmu aymana afuwa haka munyi laifi Amman aymana afuwa alameen ne yaamshi zancan dacewa sede inkaine kayi laifin Amman baniba wayace taamsa tanason auran kagako tunda taamsa dole tadau naannabawa tunda taga Dan fari me dimples tamakalemishi ita wai me wayo tacuceni ta taba raminko ay ga makomar cutarnan yakarasa zancan yana dariya dasaurin surbajo tadago kanta Tana kallonshi Dan bata dauka yana motarba ido suka hada danshima ita yake kallo dasauri tayi kasa da idonta Dan bazata iya jure irin kallon dayake mataba hannunta yakamo yana kallon zanen lallen dake Zane akan hannun lallen yayi kyau sosai wasa da hannun yashiga Yi tasigar daduk macen daakayiwa setaji dadin hakan jawota yayi jikinshi yarungume yafara yimata magana akunne yace baby waya miki wannan lallen dakyar tabashi amsa da Bilkisu ce tayimata wannan Kwalliyar fa yatambaya duk itace tayimin tabashi amsa kinyi kyau sosai yafadi yana hada bakinshi danata seda yafara kissing seda yaga yana shirin fita daga hayyacinsa sannan yasaketa surbajo wacce bataso yadenaba kwanciya tayi ajikinshi Tunda yasaketa rungumeta yayi yana shakar kamshin jikinta tuni bacci yadauki surbajo gyara Mata kwanciya yayi ajikinsa tayadda bazata wahalaba kamin sukai gida dago idonsa yayi carab suka hada ido da Usman ta mirror yanamasa dariya dan duk abinda yafaru tsakaninsu akan idonsa akayi kunyace takama alameen Amman se ya maze yace to munafiki saidonnaka wato har akan mata da mijiko to thanks God matatace ay yafadi yana hada rai dariyace takwacewa Usman yace ikon Allah inbanda tsarguwa nimekaji nace aynasan zakacene shiyasa natari numfashinka inji alameen dariya Usman yasake yi yace rufamin asiri da kallon mata da miji ni kawai cartoon din Tom and Jerry nake kallo duk yadda alameen yaso daurewa kar yayi dariya Amman yakasa duka yakaiwa Usman yana dariya yace saido de bakyau harsuka iso gida Usman na tsokanar alameen Wanda kunya tahanashi ramawa itako surbajo har suka iso gidan iyayen alameen bacci takeyi hankalinta kwance maman Yusuf [3/18, 14:14] Zahra muhd mahmud💃: 🍀🍀🍀🍀 🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *slm masoya littafin ballagaza to nayi gyara yanzu sunan littafin yatashi daga ballagaza yakoma surbajo duba da akwai littafi mesunan ballagazan inafatan zaku anshi sabon sunan littafin da hannu biyu* *page 27-28* Koda akayi parking aharabar gidan surbajo bata tashi daga baccinba ganin bata tashin bane yasa alameen gyara zamansa a motar Dan cewa Usman yayi da direban su sauka amotar danshide baze fitaba se surbajo ta tashi a bacci sauka sukayi suka barshi Usman yace ah lalle wannan cartoon yana kyau tonide badaniba nashiga ciki inta tashin inajiranka yafadi yanamasa dariya Mommy dasauran dangi masu jiran karasowar Amarya jin ance motar amaryar takarasone yasasu fita domin taryota Sede ga mamakinsu sojoji ne kewaye da motar rike da bindigu cikin shirin kota kwana abun yabasu mamaki Tsayawa sukayi suna jiran abude motar tsawon minti goma baa budeba yasa Momy tambayar daya daga cikin sojojin Kai wai amaren basu isobane ko bawannan bace motar amaryar Cike da girmamawa yace madam Amarya taiso amma oga shima yana cikin motar bande san abinda yahanasu fitowaba sede ko zakije ki gani Murmushi Momy tayi sannan aranta tace dakyau aminullahi wato mu zenunawa yayi Amarya ko zeci uwashi ne dawannan shegen rawar kan munauwara takira tace taje gurin motar tace injita tace aminullahi yafito da Amaryar haka kota sabamasa dagudu munauwara tanufi motar abinnema yasamu Dan ita akwai son Amata irin wannan ayken nurking glass din motar tayi seda tadan jima tana nurking din sannan yasauke glass din motar ganin munauwarace Yana saukewa idonta yasauka kan surbajo dake ta faman bacci kwance ajikinshi Dariya tayi sannan tace Bross kana hutawafa to mommy tace Wlh ranka ze baci inbaka fito da amaryaba tafadi Tana dariya takara dacewa su Bross ko kunya juyawa tayi da gudu zata bar gurin dasauri yarukota yace zaki sani wato ninema mara kunyan ko kwacewa tayi taruga gurin mommy Tana dariya tace mommy Wlh amaryar ma bacci takeyi maybe shine abinda yahanashi fitowa daga motar bata rufe bakiba taga daya daga cikin sojojin yanufi motar yabude kofar Alameen ne yafito sannan yamika hannu yadauko surbajo dake bacci Yanufi su mommy nanfa abokanan wasa suka shiga tsokanarshi masu dauka awaya suna dauka Dan abun koni yaburgeni jin hayaniya da surbajo tayine yasata farkawa ganin abinda kefaruwane yasata Fara kiciniyar kwace kanta Dan gaskiya kunyace takamata sosai Ganin tanason saukane yasa alameen sauketa Lafayar dake jikinta takara ja tarufe fuskarta jikinta se rawa yake sabida kunya mommy ce takarasa ta rungumota tana fadin barka da zuwa cikin zuriata Allah yasadamu da alkhairin dake tattare dake yakawar da sharrin Ameen sauran jamaar suka amsa daganan aka shige da ita cikin gidan falon daddy aka kaita alameen ma yabi bayansu nasiha sosai daddy yamusu inda akarshe yagargadi alameen akan yarike amanar yar mutane kuma yayi adalci atsakaninsu daganan akawuce da surbajo part din mommy domin shiryata zuwa gurin dinner shima part dinshi na gidan yanufa Usman yatarar da wasu abokansa su biyu suna hira dashigarshi suka juyo kanshi suna tsokanarshi babu kamarma Usman harda cewa shi ko alabari betaba jin ango Mara kunya kamar alameenba dariya alameen yayi sannan yace Kai alhdllh nagodewa Allah dayasa nazama nafarko atarihi duka suka kaimasa dukansu suna dariya daganan suka shiga shirin zuwa gurin dinner wacce zaayi a bafra international hotel dake no11b yakubu avenue off alkali road unguwar rimi kaduna Sosai suke shiri inda Amarya mommy tadauko me kwalliya tashiga yimata sosai tayi kyau wedding gown akasamata light blue gaskiya bame kallonta yayi zaton wai shekarunta sha hudune sabida surbajo akwai Kira kuma bame zaton tasan hanyar wani abu waishi kauye bare aje ga ruga ita kanta data Kalli kanta a mirror tantama tashigayi akan anya itace kuwa alameen ma shadda yasa light blue shima yayi kyau sosai yayinda sauran abokansa suka sa farar shadda kawayen munauwara sune suka zama yanmatan Amarya dangama surbajo baazo da kawarta kodayaba suma yanmatan Amarya fararan dogayen riguna sukasa yayinda Suka daura head ja takalmi ja gaskiya sunyi kyau takwas nadare motoci suka fara dibar mutane zuwa gurin taron yayinda uwargida Aisha ma tagama shiryawa cikin wani yellow din material doguwar riga takalminta red head dinta ma red Jakarta ma red ce se mayafin Data Dan yafa shima red itama ba laifi tayi kyau aminanta kuma pink din material suka sa da duk wani Wanda yazo ta bangarenta duk pink sukasa muje zuwa maman Yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Chapter 10 · 0% Book details