← Book details Sheikh Heesham Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 10

Sashe 4

Sheikh Heesham Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaye take saman benen gidan taga motocin na reton shigowa, da gudu ta sauko ƙasa tana kallon Mami ta ce" Mami Sheikh"
Murmushi Mami ta yi ta ce" ai naji ajikina ya dawo tun É—azu" bata rufe baki ba ya shigo parlon É—aukeda sallama, da murmushi afuskarsu suka amsa masa sannan ya zauna kan kujerar yana kallonsu ya ce
"Mami ina yini"
"lpia lao Heesham ya hanya?"
Ya ce"lpia lao Alhamdulillah" da murmushi a fuskarta ta ce" yaya ina yini"
"lpia lao ya karatu?"
Shine abinda ya tambayeta sannan ya miƙe ya ce" zan watsa ruwa" daga haka ya shige apartment ɗinsa.......

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da hancinsa ya shaƙi daddaɗan ƙamshin airfreshner da akayi amfani da'ita a ɗakin, a hankali ya shige bedroom ɗinsa yana jan jiki dan ya gaji sosai........

Zama ya yi gefen royal bed É—in dake É—akin, ko ina tsaf yake gwanin sha'awa kuma yasan babu wanda zaiyi wannan aikin sai Mami dukda yasan wajen a gyare yake amma wannan sabon gyarane, ganin lokaci na shigewa yasa ta tashi yana sakin ajiyar zuciya a karo na babu adadi ya shiga banÉ—akin......

Fitowa ya yi jikinsa yana ɗiga alamun wanka sumar kansa ta zubo har fuskarsa, ga wani faffaɗan ƙirjinsa sai gashi da ya yi luf akai a hankali yake goge jikin nasa kamar wanda kwai ya fashewa ajiki har ya gama sannan ya sanya wasu riga da wando farare sol dasu ya shafawa sumar kansa mai sannan ya tufketa da ribon ta zubo har bayansa, sosai take damunsa kuma ahakama ana rage masa ita, ya taje gemunsa wanda yake dogo kuma atsaye irinna riƙaƙƙun malaman nan.
"Alhamdulillah"
Shine abinda ya furta sannan ya hau kan royal bed É—in nashi ya kwanta nan da nan bacci ya yi awon gaba dashi.........

A hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta waɗanda suka mata nauyi sosai, sosai ta firgita ganin inda take dan bata taɓa ganin makamancin irin wannan waje ba a rayuwarta iya kacin abinda tasani bukka, sai kogi. Yunƙurin tashi tayi amma taji wata irin azaba ta ziyarci kwakwalwarta dole ta haƙura ta cigaba da kwanciya nan take kuma duk inda jikinta ya fara mata ciwo, batasan ina take ba kuma batasan dalilin kawota wajen ba duk zatonta ma ko siyar da'ita su Ammi sukai, wasu hawaye ne suka wanke mata fuskarta babu abinda take tunawa sai irin yanda aka dunga dukanta akan laifin da bata aikata ba, tunanin hakan yasa ta sake fashewa da kuka dan ita kaɗai tasan yanda takeji a zuciyarta......

Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce
"Laaa yaya Bilal sai yau kazo?"

Fuskarsa a sake ya ce" Eh mana ina Sheikh?"

Dariya ta yi ta ce"daman nasan saboda Sheikh kazo wlh Mami tana ta zancenka amma gashi kanaji ance Sheikh ya dawo shine kazo, ai shikenan ina Junior?" Murmushi ya yi yana shafa kansa ya ce "wlh yana gida ina Mamin?"

"batanan taje gidansu Nihal"
Ta bashi amsa gaba ya yi yana cewa " ok ina nan har ta dawo ai".......

Zaune ya same shi yana danna system kana gani kasan abu mai muhimmanci yake yi, zama ya yi kan bedside drawer ɗin yana murmushi ya ce " su Sheikh manya wato shine sai yanzu kaga damar zuwa ƙasar ko?"

Shuru yayi masa kamar bdashi yake ba, girgiza kai Bilal yayi dan yasan hali ya ce

"Wai kai harnima É—aukemin kan ka keyi?"
Shuru Shaikh ya yi kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" amma kana sane da bakayi sallama ba"

Kwaɓe fuska ya yi ya ce" sorry i forget assalamu alaika"
"Wa alaika salam" Shaikh ya amsa masa, murmushi ya yi ya ce" yanzu sai a kulani ko?"

Murmushin sa mai kyau ya yi dan yana matuƙar girmama abotar dake tsakaninsu dukda cewa shiɗin ɗan uwansa ne dan ɗan ƙanwar Mami ne kuma bazai wuce shekara 35 ba dan kusan tare aka haifesu da Sheikh Heesham.........

Hira suka fara yi akan rayuwarsu amma duk rabin hirar Bilal ke yinta dan shi Sheikh sai Umh, un'un, har lokacin kiran sallah ya yi. Miƙewa Shaikh ya yi ya shiga toilet dan ɗauro alwala domin shine yake jan sallar masjid ɗin gidan nasu............

Zaune suka tadda Mami suna taɓa hira da Shareefat, Bilal ya ce "Mami ina yini" harararsa tayi ta ce" yana gidan biki, sai yau kaga damar zuwa?" shafa kansa ya yi yana murmushi ya ce" sorry Mami wlh abubuwane suke riƙeni" ta ce" amma ai dayake ɗan uwanka ya dawo gashi na ganka yanzu babu abinda ya riƙeka kenan" kasa magana ya yi sai sunkuyar da kansa ya ce banda dariya babu abida Shareefat ke yi ta ce

"Toh yanzu ba gashi yazo ba Mami?" ta ce" yimin shuru kina goyan bayan yayanki kawai"

"Sheikh akawo maka abinci?"

Girgiza kai ya yi ya ce "azumi" ta ce" toh Allah ya haÉ—amu a ladan"..........

Shigowa ya yi ya ce" Sir yarinyar ta farka"

"Wace yarinya?"
Mami ta tambaya, tashi Sheikh ya yi yay gaba batareda ya amsa tambayar Mami ba, Bilal ne yabi bayansa yana cewa

"Wai bazaka tsaya niba"

Driver sit ya zauna bakinsa É—aukeda addu'a ya yiwa motar key ya fara tafiya cikin nutsuwa, ganin yanda yake tafe slowly yasa Bilal ya ce" wai dan Allah kayi sauri mana" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" so kake natafi da gudu wani ya mutu?" "wane zai mutu?" murmushi ya yi ya ce" ni mana" da mamaki Bilal ya ce" Eh lallai kaga kuwa bai kamata ka mutu ba bayan baka tara iyaliba, wai yaushe zakayi aure ne?" "sanda Allah ya yi" Sheikh ya bada amsa. Murmushi Bilal ya yi ya ce"wlh inada wata yarinya zan baka ka aura plx" girgaza kai Sheikh ya yi sanda yake parking ya ce" Allah ya tsare" dariya ya yi ya ce" au hakama zakace?" bai ce masa komai ba ya sauka daga motar shima ya fito.........

Tafiya kawai yake amma shi yasan yanda zuciyarsa ke wani irin bugawa ya ce" ya Allahu ya rahmanu" shine abinda yake furtawa har ya kai bakin ƙofar ward ɗin, a hankali kuma ya murɗa kofar bakinsa ɗauke da sallama........

*SHEYKH HEESHAM*

*Paid Book 500#*[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4

*🌹SHEIKH HEESHAM🌹*

*Nanameera*.

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

*AMMEY LAYLERH DETA SERVICES*

*Azo asai DATA kan farashi mai sauqi, cikin rahusa👌🏻🤗*

*Data*
*Available*

*MTN*
*AIRTEL*
*GLO*
*9MOBILE*

*MTN*

500MB-175
1GB -350
2GB - 700
5GB - 1750
10GB -3500

*AIRTEL*

500MB - 175
1GB - 350
2GB - 700
5GB - 1750
10GB - 3500

*GLO*

500MB - 175
1GB - 350
2GB -700
5GB - 1750
10GB - 3500

*9MOBILE*

500 - 175
1GB -350
2GB - 700
5GB - 1750
10GB - 3500

Account number: 3206656358

Account name: Maryam Nasiru first Bank

*MORE Information 08104493215*

Paid book
Free page 4.

Kallonsa kawai take tunda ya shigo, da mamaki Bilal yake kallon yarinyar dan kwata-kwata bai taɓa ganin yarinyar ba kuma baisan inda Sheikh ya samo yarinya mace ba, murmushi ya yi mata ganin yanda take kallonsa ya ce
"Sannu ya jikin naki?"
Tana kallonsa ta ce" da sauƙi" Doctor ne ya shigo yana kallon Sheikh cikeda girmamawa ya ce " Sir za'a iya discharging nata saidai a dinga kula da lafiyarta" jinjina kai kawai Sheikh ya yi sannan ya ce" a fito da'ita ina jiranta " daga haka ya juya ya fita, da kallo kawai Bilal ya bisa har ya fita sannan ya kalli Jiddoh ya ce" taso mu tafi dear" batayi musu ba ta tashi tana tafiya ahankali saboda har sannan jikinta babu wani kwari ta bi bayansa suka fita.........

Zaune suka tadda shi cikin motar yana danna cazbahar hannunsa, kallonsu kawai ya yi har suka shiga motar sannan ya yi mata key ya cillata kan titi............

Murmushi Nihal ta yi ta ce" to ai naga bangansa ba ina ya tafi?" taɓe baki Shareefat ta yi ta ce" wlh dai karki zaƙe dan Sheikh halinsa sai shi" ta ce" nikam ko dukana zai dinga yi inasonsa haka"tashi Shareefat ta yi ta ce "aikuwa zakisha wahala" sannan ta shige toilet.......

Kallon makeken gidan kawai take dan gani take kamar ba'a duniya take ba, dan ko a mafarki bata taɓa ganin abu mai kyau irin wannan gidan ba, lura da hakan yasa Bilal ya yi murmushi ya ce" what's ur name?" kallonsa kawai tayi amma bata bashi amsaba dan batasan abinda ya faɗaba ma, ya ce" nace ya sunanki?" sai a sannan ta sunkuyar da kanta ta ce" Jiddah" murmushi ya yi ya ce "masha Allah Hauwa'u kenan?" gyaɗa masa kai kawai ta yi, girgiza kai kawai Sheikh ya yi ya buɗe ƙofar parlon bakinsa ɗauke da sallama...........

Murmushi É—auke a fuskarsa ta ce" welcome back yaya" ba tareda ya kalleta ba ya ce" thank you", sannan ya zauna kan royal sofa É—in dake zagaye a parlon
"Ya Allahu"
Shine abinda yake faɗa akaro na babu adadi, tsayawa tayi tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Shareefat ta ce" yaya ina kasami ƴar fulani?" shuru ya mata kuma daman tasan bazai amsa mata ba yasa bata wani damu ba. Mami ce ta fito daga part ɗinta hannunta riƙe da waya tana dannawa da alama magana mai muhimmanci take, zama tayi kan kujerar batareda ta kallesu ba ta ɗaga kiran da ake mata.

Murmushi ta yi ta ce"ok kawai ki barta ta kwana gobe sai ta tafi makarantar tanan"
Daga É—aya bangaren ta ce" tom shikenan Allah ya kaimu"
Ta ce" Ameen" sai a sannan ta kallesu kai tsaye kuma idanunta ya sauka akan Jiddarh wacce har sannan bata samu ta zauna ba, da mamaki Mami ta ce
"Wannan yarinyar fa?"
Kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" idan anjima zan miki bayani in sha Allah" yana gama fadin hakan ya miƙe yana sake tattare al-kyabbar jikinsa ya shige ɗaki yana cewa
"Shareefat ki kaita É—akinki ta yi wanka"......
Chapter 4 · 0% Book details