← Book details Sheikh Heesham Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 10

Sashe 1

Sheikh Heesham Complete Hausa Novel · about 8 min read

[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰:

*🌹SHEIKH HEESHAM🌹*

*Royal Star Writer's Association*

Nanameera.

01.

Yola/ Jimeta..

Tsugune take bakin kogin tayi shuru kana ganinta kasan tunani take, wata yarinya ce tazo wucewa wacce aƙalla bazata shige shekaru goma sha huɗu ba kallonta ta yi sai kuma ta ce" Jiddoh " wacce aka kirada Jiddon ta juyo sai a sannan na ƙare mata kallo farace tass amma kana ganinta kasan a cikin wahala take bazata huce shekara goma sha biyar ba tana round face da ɗan siririn hanci sai bakinta jajur dashi ganin yanda take kallonta yasa ta buɗe dara-daran idanunta masu matuƙar ɗaukan hankali. Batace mata komai ba ta juya tayi gaba abunta, sunkuyawa tayi ta ɗau ruwan da ta ɗiba sannan ta kama hanyar da ƴar uwartata tabi....

Da gudu ta shiga gidan nasu wanda bukkace kawai tana faɗin "Ammi!! Ammi " fitowa tayi daga wani waje tana kallon ɗiyar tata ta ce" lpia hanne kina yimin irin wannan kiran?" tana riƙe ƙugu ta ce" ba kin aiki Jiddoh ba?, to wlh ganinta nayi tana wasa awajen shanun arɗo bata tafi ba tana ganina ta gudu" bata rufe baki ba Jiddo ta shigo gidan da tulun ruwan akanta, ajiyewa tayi ta tsaya ganin irin kallon da take mata, ƙarasowa wajenta tayi ta murɗe kunnenta tana magana cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce" wato ke ban isa na aike ki kije ba ko?, saboda bani na haifeki ba shiyasa kikemin irin wannan rashin mutuncin ko toh wlh bari baffan naku ya dawo yau saidai ya tsaɓa ko ni ko ke tunda ke kin gaji hali irin na uwarki" tana gama faɗin hakan ta tunkuɗata. Waɗuwa tayi tana kuka dan idan da sabo to tasaba da irin wannan, shigewa cikin bukkar sukai suka barta nan tana kuka.....

Kano State.

Ɗaukan wayarta tayi ƙirar iphone 13pro max ta zauna gefen gadonta a hankali kuma cikin isa ta fara dialing number, ganin har ya katse bai ɗagaba yasa ta ajiye wayar ta tashi ta sanya takalmknta sannan ta fito parlon.

Zaune ta sameta itada wata friend ɗinta wacce kuma daman gidan gidan zuwantane, zama tayi kusada Mami sannan ta ce" Mommy ina yini" murmushi tayi ta ce" lpia loa Shareefat ya gida ya karatun?" tana kwanciya cinyar Mami ta ce" lpia Alhamdulillah ina Nihal?" ta ce" wai yau za'a musu orientation that's why bata biyoni ba" ok tace sannan ta kalli Mami ta ce" Mami nakira Sheikh fa kuma bai ɗauka ba" Mami ta ce "maybe wani abun yake anjima sai ki sake kiran kije kici abinci Shareefat" kwaɓe fuska ta yi ta ce" wlh Mami i'm full saidai anjima" ok Mami ta ce tana kallon Hajiya Zainab ɗin ta ce" yawwa sai akayi me Hajiya?" ta ce" wlh ina baki labari kin san yaron ashe wai hacker ne to ankamashi shine take ta kuka" girgiza kai Mami ta yi ta ce" Allah Sarki Nihal Allah yasa hakane mafi alkhairi" ta ce "Ameen".......

Ganin da tayi rana ta faɗi yasa ta miƙe a hankali ta shiga inda nake zaton shine banɗakinsu, cire kayan fulanin dake jikinta tayi ta ɗebi ruwa ta watsa a jikinta sannan ta ɗaura alwala ta fito. Wata tabarmar kaba ta samu wajen ƙuda sai bi yake ta ɗauka ta shimfiɗa ta tada sallah. Tana idarwa ta tashi a hankali dan da kyar take tafiya saboda tsananin yunwar da takeji ta fita daga cikin bukkar tasu, tafiya kawai take batareda tasan inda zata jeba ita dai tasan yunwa takeji kuma abinci ta fito nema, ji tayi tafiyar na neman gagararta yasa ta nemi wani waje ta zauna ta kifa kanta kan gwuiwoyinta ta fashe da kuka, haka ta zauna wajen mintuna talatin a hankali kuma bacci ya ɗauketa.....

Sanyin asuba ne ya farkar da ita a firgice ta tashi tana kalle-kallen inda ta kwana, jiki babu kwari ta miƙe ta kama hanyar tafiya gidansu. Duk suna cikin bukkah kowa na kwance babu wanda yayi noticing bata kwana gidan ba ta shiga cikin tata bukkar wacce ita ɗaya take kwana, babu komai cikinta sai tabarmar kaba ta kwanta akai tana tunanin rayuwarta bata taɓa samun farinciki ba batasan mene ne jindaɗi ba abunda kawai ta buɗi ido ta tarar shine wahalar rayuwa, tabbas rashin mahaifiya babban giɓine a rayuwa domin da tanada uwa da tasamu sauƙin wani abun amma ita bata tadda tata mahaifiyarba dalili kuwa sanadiyyar haihuwarta Allah ya karɓi ranta dunga sanda aka haifeta har zuwa yanzu babu wani abu mai daɗi cikin labarin rayuwarta, da waɗannan tunanin bacci ya sake awon gaba da'ita.......

Fitowa tayi da shirinta na tafiya makaranta, kallonta Mami ta yi ta ce

"Shareefat kiyi sauri fa karki makara"

Toh ta ce sannan ta ajiye cup É—in tea É—in ta ce "tom Mami bye"

Murmushi Mami ta yi ta ce"bye dear Allah ya tsare" waje tayi tana cewa Ameen....

A firgice ta miƙe tsaye dalilin ruwan sanyin da taji an watsa mata, tsayawa tayi jikinta na kyarmar sanyi domin lokacin weathern sanyi ake tana mata wani shegen kallo ta ce

"zaki zo ki wuce ko saina bigeki" ahankali ta ratsa ta gefenta ta fita jikinta sai É—iga yake, tulun ruwan ta É—auka kawai tayi waje......

Tunda ta fito yake kallonta har ta ƙaraso gabansa sosai yarinyar take bashi tausayi yana kallonta ganin yanda take rawar sanyi yasa ya ce" Jiddo meyasa zaki jiƙa jikinki a wannan sanyin?" sunkuyar da kanta kawai ta yi tana goge hawayen fuskarta, ganin babu mutane dayawa wajen yasa ya ce" ina zakije?" bata kalleshi ba ta ce"

ruwa zan ɗebowa Ammi" girgiza kai ya yi dan tsananin mugunta ce tasaka wannan aiken da sassafe ya ce "toh muje na raka ki" sai a sannan ta ɗago ta kalleshi da idanunta da sukayi Ja ta ce" kabarshi kawai ngd" murmushi ya yi ya ce" karki damu Jiddoh muje" bata kuma magana ba tayi gaba yana binta abaya har suka ƙaraso kogin. Karɓa tulun ya yi ya ɗebi ruwan sannan ya ɗora akafaɗarsa yana mata murmushi ya ce" mu tafi" toh kawai ta ce ya yi gaba tana binsa a baya, tana ganin sun kusa zuwa gidansu ta kalleshi ta ce" kabani kar Haule ta ganka" bai yi mata musuba saboda yana guje mata a doketa ya miƙa mata ruwan ya ce

"kin ci abinci kuwa?" É—aga masa kai ta yi kawai sannan a hankali cikin cool voice É—inta ta ce" nagode Laminu" murmushi ya yi kawai sannan ya juya ta tafi........

Tana shiga ta tararda Baffa tsaye yana tambayarta da gudu ta ƙarasa wajensa ta tsaya tana kallonsa dan rabon da tagansa har ta manta, kallonta ya yi ya ce" Hauwa'u daga ina kike?" tana murmushi ta ce" Baffa na ɗebo ruwane" kallon Ammi ya yi ya ce" yanzu Hanne wannan abun ya dace da sassafe zaki aiketa ɗiban ruwa kuma ita kaɗai ina ita Haulen?" wani kallon sheƙeƙe tamasa sannan ta wani karkace baki cikeda faɗa take faɗin da harshen fulatanci " to bazan aiketa ba naga bacci Haule take kuma ba ƙanwarta bace ai dolene ta taimaka mata, har wani zakace an aiketa da safe idan yawonta ya tashi kasan inda take zuwa" girgiza kai kawai ya yi ya kalleta ya ce" jeki ki zauna" tafiya tayi kamar yanda ya ce mata ta zauna kan tabarma shikuma ya juya ya fita.....

Yana fita yayi hanya wani ɗan ƙaramin garke, yana shiga ya tsuguna jikin wata saniya ya tatsi nononta yana gamawa ya fito. Inda ya barta nan ya sameta amma banda Ammi dan tayi shigewarta bukkah, zama ya yi gefenta yana kallonta ya ce" karɓi kisha kinji" batayi musuba ta karɓa tunda ta ɗaga kanta bata saukeba sai da ta shanye nonon tass sannan ta ajiye kwaryar, kallonta yake cikeda tausayawa yasan batada kwanciyar hankali kwata-kwata kuma haƙiƙa da yasan inda zai kaita da tuntuni ta bar wajen. Kallonsa ta yi ta ce" Baffana" murmushi ya yi mata ya ce" na'am Hauwa'u " ta ce

"Ka bani labarin Ammina Baffa"

Shuru ya yi bai ce mata komai ba ta kwaɓe fuska a hankali ta ce" Baffa me kake tunani?" juyowa ya yi yana kallonta taga hawayen kwance akan idanunsa, sosai hankalinta ya tashi ta shiga goge masa tana cewa

"Dan Allah Baffa kayi haƙuri bazan sake tambayarka ba kaji" hannun da take goge masa ya riƙe yana kallonta sosai taga ya saki murmushi, tsayawa ta yi tana kallonsa dan ba ƙaramin kyau murmushin ya yi masaba kasancewarsa asalin bafulatani, ya ce

"Aduk sanda na kalleki sai naga kamar Hauwa'u ce gabana, domin babu abinda kika manta nata da baki ɗaukoshiba yanda kike da haƙuri haka take koda cutarta kake kuma tasan cutarta kake bazata taɓa nuna makaba, sannan bata riƙo a rayuwarta tana iya yafe laifi duk girmansa na tabbata Hauwa'u ƴar Aljanna ce, inaso ki ɗora daga inda kika tsaya Hauwa'u kisani babu wanda aka taɓa zalunta kuma Allah ya barshi haka ki cigaba da haƙuri kinji watarana sai labari"

Kuka kawai take ta gyaɗa masa kai a hankali ya fara goge mata hawayen yana murmushi yace" Allah ubangiji ya jiƙan Hauwa'u" ta ce" Ameen".....

Wajejen ƙarfe sha biyu tana zaune cikin garken shanun nasu bata damu da yanda jikinta ya ɓaci ba, dan babu inda takejin dadi sai wajen waɗannan dabbobin indai Baffanta bayanan. Fitowa tayi tana kalle-kalle sai kuma ta ƙaraso gabanta tana kallonta ta ce

"Kee Jiddoh kizo inji Ammi" bata jira amsarta ba ta juya ciki abinta. Tashi Jiddah ta yi ta shiga cikin gidan nasu, zaune ta sameta tana dama fura ta tsuguna gabanta cikin ladabi ta ce "Ammi gani" kallonta ta yi ta ce

"Ki tashi kije gidan ArÉ—o Adda zata aikeki" tashi ta yi batareda ta ce komai ba ta fita daga gidan.....

Zaune take kusada Mami tana cin abinci ta ce" toh yanzu kina ganin Sheikh zai amince ya auri Nihal kinfasan halinsa Mami" kallonta Mami ta yi ta ce

"Ai ni ce na haifi Heesham ba shine ya haifi kansaba kuws this time around dole ne ko yana so ko baya so ya yi abinda nace" taɓe baki Shareefat ta yi ta ce
Chapter 1 · 0% Book details