← Book details Sheikh Heesham Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 10

Sashe 3

Sheikh Heesham Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsayawa Driven ya yi da tuƙun, ahankali ya ɗago idanunsa daga kan computern hannunsa juya idanunsa ya yi kamar zai yi magana sai kuma ya yi shuru da bakinsa kusan 2mins amma bai ce komai ba cikeda ladabi driven ya ce
"Sheikh motar ta samu matsala kuma gashi dare ya rigada ya yi saidai mu samu wani wajen mu zauna zuwa safiya"
Sai a sannan ya kalleshi da fararen idanunsa kuma manya, sunkuyar da kansa drivern ya yi domin duk rashin kunyarka baka isa ka haÉ—a idanu da Shaikh Heesham ba. A hankali ya buÉ—e bakinsa yana tasbihi ga ubangiji kusan mintuna biyar sannan ya ce cikin tsantar nutsuwar data gama ratsashi
"Allah ya kaimu"
Abinda kawai ya furta kenan bai kuma sake wata maganar ba ya lumshe idanunsa masu kyau. Sheikh Heesham Muhammad kenan babban malami a ƙasar saudia yankin larabawa, ya kasance kyakykyawa dan asalin balarabe ne mahaifinsa Alhaji Muhammd ɗan asalin ƙasar saudia ne amma bai rayu acan ba kasancewar duka danginsa mutanen Nigeria mahaifiyarsa ta haifeshine a ƙasar dalilin zuwa omrah. Sanda aka samu cikin Sheikh Heesham sai mahaifiyarsa Hajiya Amina ta tafi saudia dan rainon cikin jikimta har kuma ta haihu ƙasar hakan yasa shima ya kasance indigin na ƙasar saudia saboda haka sanda ya fara tasawa sai mahaifinsa ya kaishi karatu ƙasar, ya kasance ya rayu a ƙasar tun yana ɗan karamin yaro har girma shiɗin likitane gefe guda kuma babban malami a ƙasar. Wannan shine ƙadan daga tarihin rayuwarsa..

Ganin dare na ƙara yi yasa drivern ya ce
"Sheikh ko zamu samu wani gurin mu zauna?"
Ba zaka taɓa cewa da Sheikh Heesham ake magana ba dan ko kallonsa bai yiba bare ya saka ran zai bashi amsa saima cigaba da danna cazbahar hannusa da yayi..

Hadarine ya haɗo ganga-ganga kuma kana gani kasan ba ƙaramin ruwane zai sauka ba, ɗaya daga cikin securities ɗinsa dake ɗaya motar ne ya fito yana tafiya kamar wani zaki yazo gaban motar ya sunkuyar da kansa ya ce

"Sir wannan hadarin zai iya sakawa ayi ruwa mun samu wani waje zaka je ka zauna saboda lafiyarka"
Sai a sannan Sheikh ya kalleshi amma bai ce komai ba, buɗe masa motar ya yi yana kallonsa. A hankali kuma cikin nutsuwa ya zuro ƙafarsa waje sannan ya fito daga motar yana gyara zaman al-kyabbar jikinsa ya ce
"Ya Allahu"
Shine abinda ya furta yana sake kallon yanda garin ke yin duhu na haÉ—owar hadari sannan ya fara tafiya yana goya hannunsa a bayansa....

Wata bukkah ce suka nuna masa ya sunkuya domin kwata-kwata bukkar batayi rabinsa ba, zama ya yi kan carpet ɗin da suka shimfiɗa masa kamar kuwa jira ake ruwan ya fara sauka da ƙarfinsa...

Ba ƙaramin ruwa akayi a jimeta ba ko'ina ya yi daɗin gwanin ban sha'awa ganyayyaki da shuke-shuke duk sunyi kyau, yanayi ne wanda zai sanyaka cikin nishaɗi da annashuwa haka kuma har Allah ya wayi garinsa.....

Zaune yake inda ya yi sallar domin bai iya bacci ba yana azkar É—insa wani guard ya shigo ya sunkuya cikin girmamawa ya ce
"Barka da safiya Shaikh!"
Ba tareda ya kalleshi ba ya ce
"Barka"
Abinda kawai ya iya furtawa kenan, guard É—in ya ce

"Sir ya kamata mu tafi dan jirgin ya kusa tashi"

Batareda ya yi magana ba ya miƙe yana ambaton sunayen Allah a ransa kamar koda yaushe ya yi waje.....

Sosai take mamakin inda taganta kwance, ahankali ta miƙe zaune tana kallon kusan duk mutanen rugar da suka zagayeta ana ƴan ƙananun maganganu, mai garin ne ya fito yana kallon kowa ya ce

"Ina fatan kowa ya shaida abinda wannan yarinya ta aikata?, saboda haka za'ayi mata hukunci daidai da laifinta saboda kada Æ´an baya suce zasu kwaikwaya " gyaÉ—a kai duk suke alamar gamsuwa da abinda ake faÉ—a d'in ita kuwa sai idanuwa take binsu dashi dan bata gane inda zance ya dosa ba....

Wata zabgegiyar bulala aka É—auko irin wacce suke amfani da'ita idan za'ayi shaÉ—i tasha manshanu sai kyalli take, kallon bulalar kawai take dan batasan me zasuyi da itaba, mai gari ne ya kalli mutumin ya ce

"Zaka yi mata bulala 80 shine hukuncinta da kuma kora daga cikin garin nan".

Karɓar bulalar ya yi yana sake gyara zamanta a hannunsa ya ce"za'a riƙetane saboda kar ta wahalar dani?"

Girgiza kai ya yi ya ce
" Ai bata isaba dole ta tsaya ayi mata hukunci tunda shi ya zama É—an iska"

Allah sarki Jiddah banda kallo babu abinda take amma zuwa lokacin ta gane inda maganar tasu ta dosa, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata ta saka hannunta tana sharewa Allah ya sani bata aikata komai ba kuma batasan ya akayi ta zo wajen nan ba amma wa zata faÉ—awa ya yarda da ita?!, babu..........

Tafiya kawai suke acikin motar, idanunsa a lumshe suke dan wani azabbaben ciwon kai yake ji, ji yayi zuciyarsa tayi wani kyakyawan bugu ya buÉ—e idanuwansa yana kallon garin daidai nan kuma ya hango wasu cuncurundon mutane kuma fulani ya yinda har sannan yake jin bugun zuciyar na sake tsananta.

"Stop the car"

Ya faɗa ba tareda ya kalli drivern ba cak kuwa ya tsaya yana juyowa dan yasan ba ƙaramin abune zai sa Sheikh ya magantuba. Kamar wanda akama tilas haka ya kama murfin motar ya fito, nan take duk guards ɗinsa suka fito kowanne ya yi cirko-cirko dashi...

Tafiya ya fara yi torward direction ɗin da yake hango mutanen, yana kusantar wajen yanajin bugun zuciyar na ƙaruwa fiyeda na baya a haka har ya ƙaraso.....

Ganin balaraben mutum yasa duka suka dare masa hanya, a hankali ya matsa har inda yarinyar ke kwance sai zabga mata bulalar ake, duk jikinta jini ne kana gani kasan ba ƙaramin duka suka mata ba..

Ba tareda ya yi magana ba ya ƙarasa wajenta yana kkallon mutumin, ahankali kuma ya zare bulalar daga hannunsa cikin yanayinsa nason kamewa ya ce

"Ka bari babu kyau zalunci"

Sakar baki sukai dan basu ɗauka ya iya hausaba, mai garin ne ya ƙaraso gabansa wani guard ya daka masa tsawa

"leave that place"

Zabura ya yi Sheikh Heesham ya riƙoshi yana kallonsa ya ce

"Mene?"

Cikin inda-inda ya fara faÉ—in

"Daman..Dama..Daman wannan yaron ya mana laifi ne an kamashi da maza da daddare kuma hukuncinsa shine bulala 80 sannan a koreshi daga garin"

Kamar bazai magana ba sai kuma ya ce

"Ku rabu da'ita"

Girgiza kai ya yi ya ce "ai saidai ka tafi da'ita dan indai tana garin nan to sai angama mata bulalar nan kuma bulala 20 aka mata"

Shuru Sheikh Heesham ya yi sai kuma ya sakeshi ya juya dan komawa mota....

Da gudu arÉ—o ya bishi kafin ya isa motar ya cimma sa cikin magiya ya ce

"Dan Allah dan Annabi yaro ki taimaka ki tafi da Jiddoh ko zata samu rayuwa me kyau zata mutu anan aradu indai suka gama yi mata wannan bulalar to bazata tashi ba, ki taimaka yaro"

Ya ƙarashe maganar yana kuka...

A nutse ya saka tattausan hannunsa ya É—ago arÉ—o yana kallonsa sai kuma ya yi murmushi ya ce

"Shikenan zan kula da'ita"

Ajiyar zuciya arÉ—o ya sauke sannan ya ce

"Amma baza su barka ka tafi da'ita ba har sai ka aureta"

Da sauri ya kalleshi sai kuma ya girgiza kai alamar bai yarda ba.

Tsugunawa arÉ—o ya sakeyi ya ce
"taimakawa zakayi idan kuka bar garin nan sai ka saketa kaji yaro" shuru Heesham ya yi arÉ—o ya ce

"Naga kayi kalar taimako yaro ka taimakawa marainiyar nan batada kowa sai Allah sai kuma kai yanzu"

Bazai iya cewa A'a ba dukda yasan bazai zauna da ita matsayin mata ba amma zai taimaketa yayi jahadi.......

Murmushi ya yi yana kallon ArÉ—o ganin yanda yake kuka da idanunsa ya ce

"Shikenan na amince".......

Kama hannunsa arÉ—o ya yi jikinsa har rawa yake suka koma wajen....

Yana kallon mai gari ya ce

"Zai tafi da'ita"

"Amma yasan saidai ya aureta?"

GyaÉ—a masa kai ya yi ya ce" shikenan"

Anan aka ɗaura auren Sheikh Heesham Muhd da Hauwa'u Ahmad sadakinma zoben hannunsa suka karɓa.......

Kallonsa Ardo ya yi ya ce
"Na yarda dakai yaro nasan zaka kula da rayuwar Hauwa'u kada ka barta ta yi kuka kaji"

Riƙe hannunsa Sheikh ya yi ya ce

"Har ƙarshen rayuwa"

Kwance take dan har sannan bata farfaɗoba ya saka tattausan hannunsa ya ɗauketa yana tafiya har suka isa cikin motar, tsayawa arɗo ya yi yana musu addu'a har suka ɓacewa ganinsa.........

Share it plx.

*Paid book #500.*

*SHEIYK HEESHAM*
[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4

*🌹SHEIKH HEESHAM🌹*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Nanameera.

03.

Tafiya kawai suke inda shi kuma tunaninsa ya ke wani wajen daban,
"Ya Allahu, ya Rahmanu"
Shine kawai abinda bakinsa ke furtawa har suka ƙaraso filin jirgin....

A vip yake ya kishingiɗa da bayan kujera idanunsa a lumshe shi kaɗai yasan iya abunda ke damunsa gashi kuma ciwon kansa nason hargitsashi, ahaka yana wannan tunanin bai san bacci ya ɗaukeshiba dan baccin Sheikh sai dai ɓarawo......

A nutse yake tafiya guards ɗinsa na biye dashi har ya'isa gaban motar suka buɗe masa, zama ya yi yana kiran sunan Allah a cikin ransa kamar koda yaushe. Ganin drivern yaƙi tafiya yasa ya ce
"lpia?"
"Sheikh daman yarinyarce ba'a É—auko ba"
Sai asannan ya tuna dan kwata-kwata ya manta da wata yarinya ya ce" ina take?" tana can kwance har yanzu bata farfado ba za'a saka guard ya É—auketa ya kaita asibiti"
Bai ce komai ba ya sauka daga motar ya bisa da kallo yana daÉ—a jinjina hali irinna Sheikh Heesham.....

Kwance ya tarar da'ita har sannan kuma batada niyyar farfadowa, a hankali ya sanya hannayaensa duka biyun ya É—auketa, ji yayi kamar bai É—auki komai ba saboda rashin nauyinta ni kuwa nace ya za'ayi tayi nauyi??????..

Kai tsaye asibitin Abdullahi wase dake nassarawa ya kaita, sosai sukayi murna ganin babban malami a asibitin cikin mutuntawa kuma suka karɓeta shikuma ya shiga mota dan tafiya gida......
Chapter 3 · 0% Book details