Sashe 10
Sheikh Heesham Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuru ya yi har Dad ya gama faɗa sannan ya ce "amma Dad.. Dakatarda shi ya yi ta hanyar yi masa alama da hannunsa sannan ya ce " Heesham dolene kayi aure kuma not too long saboda zamanka a haka ba abu bane mai yiwuwa kuma kamar yanda mahaifiyarka ta zaɓa maka mata idan ta hali kana iya aurenta amma ni bazan maka dole ba abinda kake so shi zakayi kana iya zuwa kayi tunani ka yankewa kanka shawara amma tabbas inason kafin nan kafin 2months kayi aure idan kuma baka fito da mata ba kuma baka ɗauke wacce aka zaɓama ba to zaka wayi gari ka tarar an kai maka mata gidanka kuma babu saki, ɗazu munyi waya da Sameer kuma shima abinda ya ce kenan karma kayi tunanin guduwa duk inda kaje zansa a nemoka understood?" gyaɗa masa kai kawai Sheikh ya yi dan ji yake kamar kansa zai rabe biyu saboda tsananin ciwon da yake masa, a daddafe ya haura saman yana shiga ɗakinsa ya shige banɗaki, ruwa ya sakarwa kansa saida yaji hankalinsa ya fara dawowa jikinsa sannan ya yi wanka ya fito. Wata armless ɗin riga ya saka da wadonta ya kwanta nan da nan bacci ya ɗaukesa.
Murmushi ya yi ya ce" wato dai kana jin maganar yaya Sultan ko?" harararsa Ajmal ya yi ya ce" wlh kawai saboda shi zan koma, amma yanzu yaushe zaka zo?" "sai da bikin ka" wani shegen kallo ya yi masa yana rufe trolley ɗin ya ce"kada Allah yasa kazo" murmushi kawai ya yi yazo ya rungumeshi ta baya ya ce" in sha Allah friend nan bada jimawa ba zanzo harda Nabeela" murmushin shima ya yi ya ce" Allah ya sa" dariya sukayi duka sannan ya ce" amma dai please ka ci abinci yau kafin ka tafi" "idan naƙi fa?"
"Sai nasa ayi maka duka dan ni bazan iya dukanka ba" fashewa ya yi da dariya sannan ya yi waje.
Throughout ranar haka ta yini a makaranta tana jinta wani iri bata ce ga exactly abinda yake damunta ba amma jinta take duk wani lonely hatta Hajar basuyi wata hirar arziƙi ba har aka tashi, sosai tayi mamaki ganin yazo ɗaukanta yauma, bayan sun ɗanyi nisa ya kama hannunta batareda ya yi magana ba ya zaro wani diamond ring mai kyau kuma mai matuƙar tsada sai sheƙi yake yi ya zura mata a ɗan yatsanta na tsakiya sosai ring ɗin ya yiwa farar fatarta kyau kamar an dasashi, murmushi tayi ta ce" Abbana ya yi kyau sosai nawane?" gyaɗa mata kai ya yi ya ce" na kine Heeshama promise me bazaki manta dani ba" da sauri ta kalleshi ta ce" Abba meyasa zaka ce haka?" numfasawa ya yi amma bai ce komai ba, ta riƙe gemunsa ta ce " Abbana!" juyowa ya yi taga yanda idanunsa suka rini kamar gauta da sauri kuma cikin tashin hankali ta ce" Abbana bakada lpy?" girgiza mata kai ya yi dan ya gagara yin magana haka kawai taji gabanta yanata faɗuwa har suka isa gidan
Kallonta ya yi ya ce" ki shiga Heeshama zani unguwa?" kallonsa ta yi sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce" Abba zan bika" girgiza mata kai ya yi ya ce" kije gida kinji Allah ya Albarkaci rayuwarki" murmushi ta yi ta ce" Ameen Abba na, Allah ya dawo dakai lafiya" "Ameen" ya furta da kyar, a hankali ta sauka tana tafe tana waigowa taga shima kallonta yake har ta shige parlon.
"Ina zamuje Sir?"
"Airport" Sheikh ya furta yana lumshe idanunsa shi kaÉ—ai yake furta
"Ya Allahu Ya Rahmanu, Ya Zul-Jalalu wal ikhram".
"Mami banfa gansa ba" harararta Mami ta yi ta ce "wlh idan naje na ɗaukoshi sai ranki ya ɓaci" gyaɗa mata kai Shareefa ta yi sannan ta zauna suna hira da Nihal.
Duba sosai Mami ta yi amma bataga gold É—in ba, sosai kuma abun ya É—aure mata kai dan tasan babu kowa a gidan idan ba itaba, Shareefa, Nihal a parlon. Sakkowa ta yi tana kallonsu ta ce" bakuga inda na ajiyesa ba jiya ko na canza masa waje ne?" da mamaki suka ce "wai kema baki ganshiba Mami?" gyaÉ—a musu kai tayi Shareefa ta ce
"Kuma naga babu wanda ya shigo gidan nan jiya"
"Nima abunda yake bani mamaki kenan" Mami ta faÉ—a. Shuru suka yi sai kuma Nihal ta ce
"To ko za'a tambayi Jiddah ne ko ta gansa?" da sauri Shareefa ta ce" a ina Jiddah ta ganshi batama san mene gold ba bare ta É—auka".
"Nifa cewa nayi a tambayeta ko ta ganshi, ko ya kika ce Mami?"
Da sauri Mami ta yi hanyar É—akin Jiddah ba tareda ta sake yiwa koma magana ba.
"Mu koma gida i forget something"
Sheikh ya faÉ—a lokacin sun kusa kaiwa Airport É—in, okay kawai drivern ya ce sannaa ya yiwa sauran motocin umarnin dasu koma suka kama hanyar gida.
Bata cikin É—akin amma ruwa na zuba a banÉ—aki alamar wanka take, dube-dube Mami ta hau yi a É—akin, time É—in Shareefa suka shigo da Nihal da sauri Nihal ta ce" lemme help you Mami" daga nan ta fara bincike duka cikin É—akin ita kuwa Shareefa sai binsu da kallo take.
"Mami i got it"
Nihal ta faɗa da ƙarfi, da sauri duka suka juyo suka kallonta tana riƙeda sarƙar gold ɗin a hannunta, tsabar shock sun kasa rufe bakinsu hatta Shareefa kallon sarƙar take da sauri Mami ta karɓa tana cewa
"Ina kika ganta Nihal?"
Daidai nan Jiddah ta fito daga banÉ—akin tana kallonsu da mamaki
"A cikin wasu kayanta ta ɓoye Mami"
Iyaka ɓacin rai ran Mami ya ɓaci ita kuwa Jiddah kallonsu take da rashin fahimta da sauri Shareefa ta shaƙe mata wuya ta figeta har parlon tana mata wani shegen kallo ta ce
"Æarauniya kawai, kin bani mamaki Jiddah ki rasa me zaki sata sai gold wlh kinyi asara daman ance tsintacciyar mage bata mage, no wonder Mami ta tsaneki ashe É“arauniya ce bamu sani ba wlh kin yi asara banza kawai Æ´ar matsiyata"
Allah sarki Jiddah kallonta kawai take tama kasa magana ko kuka dan batasan akanme take mata magana ba, Mami ce ta fito tana kallonsu ta ce
"Shiyasa tun zuwanta nace bana sonta daman wlh ni nasan tabbas tanada wani mugun hali da take aikatawa yasa naji na tsaneta Heesham ya kawo mana masifa"
Da mamaki ya ce"what's wrong Mami?" kallonsa ta yi sai kawai ta fashe da kuka ta ce" Heesham sanda nake faɗa ai ƙarya kuke ɗauka nace na tsani yarinyar nan amma kuna min kallon mara imani" da rashin fahimta ya ce" Shareefa meya faru?" da sauri ta ce masa "yaya Jiddah ce ta satarwa Mami gold ɗinta data siyo jiya"
"Sata?"
Ya maimata kalmar a fili sai kuma ya kalli Jiddah wacce ta fashe da wani raunataccen kuka dan sai a sannan tak abinda ake zargin ta aikata, girgiza kansa kawai ya yi sai kuma ya juya ya fita daga parlon ta bisa da kallon amma ta kasa magana
Babu irin tijarar dasu Mami da Shareefa basu yimata amma duk wannan abun da ake Nihal bata saka baki ba tayi shuru abinta har suka gama maganarsu suka shige sama.
Zaune ta tarar da ita gefen wata flower sai kuka take kamar ranta zai fita
"Jiddah"
Ta kira sunanta, da sauri Jiddah ta ɗago tana kallonta sai kuma ta sunkuyar da kanta tana share hawayen fuskarta, zama ta yi gefenta ta ce" kiyi haƙuri Jiddah ki ɗauka hakan ƙaddararki ce, amma ina son baki wata shawara"
Da sauri ta kalleta ta ce cikin kuka "dan Allah wace shawara zaki bani?" numfasawa Nihal ta yi sannan ta ce" tunda kikaga Sheikh ya fita bai kula ki ba toh yan sanda zai kirawo su kama ki, kuma yanzu na baro su Mami suna faÉ—awa Dad kuma bai kamata ace Dad ya ganki da wannna laifi ba" hankali Jiddah idan ya yi dubu to ya tashi ta ce" dan Allah ki bani shawara"
"Shawara ɗaya zan baki shine ki gudu kafin su dawo kiyi tafiyar ki garinku" da sauri ta kalleta ta ce" ni bansan hanya ba kuma banida kuɗi" kuɗaɗe ta zaro wajen bandir ɗaya na ƴan dubu ta ce" ungo kiyi tafiyar ki idan kika fita saiki tambayi tasha idan aka kaiki sai ki hau motar garinku" goge hawayen fuskarta ta yi sannan ta ce" nagode" murmushi Nihal tayi mata sannan ta mike jiki a sanyaye ta fara tafiya har ta fita daga cikin gidan daga ita sai hijab har ƙasa ajikinta wata ƙaramar riga ce. Ajiyar zuciya Nihal ta sauke sannan ta tashi ta koma gidan.
Allah sarki rayuwa tafiya kawai Jiddah take yi batareda tasan inda zata ba, murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce" dallah ka daina min ko bakaga tuƙi nake ba?" dariya Ajmal ya yi ya ce" wato bakason ka mutu yaya Sultan bakai aure ba?" kafin ya bashi amsa ya sake kai hannu zai taɓashi da sauri ya kalli gabansa amma kafin ya tsaya har ya rigada ya kaɗeta, cikin tashin hankali suka fito daga motar, kwance suka tadda ita dukda basu wani bigeta sosai ba amma ta suma, ɗukanta Sultan ya yi ya saka a mota suka cigaba da tafiya. Basuda ishashen lokacin da zai ishesu su kaita asibiti anan garin hakan yasa kawai suka hau private jet ɗin da aka kawo musu zuwa garin bauchi.......
*Shin wace irin ƙaddarace ta raba Jiddah da Abbanta?*
*Shin da gaske Jiddah itace wacce ta saci gold É—in ko A'a?*
*Shin da gaske Sheikh yan sanda ya tafi É—ebowa Heeshamarsa?*
*Shin meyasa Jiddah tabar garinsu kuma suwane Ajmal da Sultan?*
*Shin ya Heesham zai ji idan ya dawo ya tarar babu Heeshamarsa?*
*Duka zaku samu amsoshin tambayoyinku a yayinda kuka biya kuÉ—in littafin Sheikh Heesham 500# via 9086030007 evidence via 09086030007 or contact me direct via 09086030007 whatsapp only*
*Taku har kullum Nanameera sai mun haÉ—u a paid group*