Sashe 7
Rainon Soja Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuma malamai duka ku fita Nine zan rinƙa mata wankan ta da koman ta bana buƙatar taimakon kowa , tun da abun ya koma harijanci🙊😹 . Gimtse Dariya su Ibrahim suka yi don yanda joy take kyarma daga taimako sai ta baka dariya . Da sauri ta fice bata ce dashi komai ba . Haka suma suka fita ,suna barin sa daga shi sai Ma'eesha.
Hannun sa yakai yana ɗago Ma'eesha tare da fara cire ƙaramin Pant ɗin jikin ta. A kan ƙafafun sa ya zaunar da ita yana fara Wanke mata jikin ta don yanda ake ma yara wanka bai fa sani ba . Sai da aka gama wanke jikin ne ya fara zuba mata ruwan ɗumin yana mata Wasa da ruwan tana dariya, a haka ruwan da ya ƙarar mata a jiki yafi ƙarfin bokiti babba uku , yanda take dariyar shi yake sanyaya zuciyar sa .
Kallon Areef Ibrahim yayi kana yace " saura mintuna biyar fa mu makara ”. Shiru Areef yayi kana Adam yace “ Leka kace masa yayi sauri ”. A'a kai dai kaje . Hahahahaha....suka fashe ma Areef da dariya . Ibrahim ne yace “ Wai tsoron Ali kake yi ne ?”. A'a bana ce ba ,amma kai zaka iya zuwa ”. Ok ya furta yana kama hanya tare da kutsa kan sa cikin Toilet ɗin . Wasa yaga yana yi mata da ruwan suna dariya , Dariyar da bai taɓa ganin Aliyu yana yin irin shi ba . Shi da ko murmushi ne sai yaso yake yi. Amma yau dariya har da kyakyatawa da ƙaramar yarinya . Aliyu saura mintuna biyar mu makara ”....Wani ɗauke wutaaa Aliyu yayi cikin fushi da ɗan ɗaga murya ya furta “ Dole sai dani zaku tafi , zaku iya tafiyar ku abin ku ”. Jin haka yasa Ibrahim juyawa har yakai ƙofa Yaji Muryar Ali ya katse shi da cewa “ Daga yau kar wanda ya sake shigo mun Toilet indai ina tare da Ma'eesha 🤗 . Saurin kallon sa Ibrahim yayi kamin yayi magana Nan Take Haidar yace “ Yessss haka nace kar wanda ya sake shigowa ko baku ga mace Bace ita , Idan ina mata Wanka kar wanda ya ƙara shigomun ka faɗa masu ”. Sakin baki Ibrahim yayi yana ficewa daga Toilet ɗin tare da isa inda Su Areef suke yana mai labarta masu yanda suka yi da Ali yanzu a Toilet .
Wani irin dariya Areef keyi har da buga ƙafa kana Adam yace “ Ok to shi ba namiji bane kenan, me zamu kalla a wannan jaririyar yarinyar? Kai nifa Ban gane ba ne ma🥴 . Ya furta yana kama ƙwiɓin sa . Fashewa da Dariya Ibrahim yayi kana yace “ Kasan halin Aliyu fitina ce kawai irin nashi yake neman kan wa zai sauke ,kaga kuwa ba Dani ba , Ni nayi na class kuma zaku tsaya ne ko na tafi Ni kaɗai .
A'a mu jira shi ya fito sai mu tafi duka.
Adam ne ya kalli Areef kana yace “ Ok tom mu jira shi kaga ikon Allah yana fitowa zaice mu fita daga waje ya shirya Ma'eesha 🤣 kar a ga mata jiki . Yarinya kaman kazar turawa wata can ƙasa da ita gata fa gijib. Dariya suka saka baki ɗaya cikin sauri suna ficewa tare da nufar inda ajijiwan karatun su yake.
Shi kuwa Aliyu koda ya fito yaga babu su bai damu ba ,don dama ya kuɗurta a ransa indai ya fito ya gansu sai yasa sun fita sannan zai shirya ma'eesha su tafi aji tare ....jama'a kuji mun Bala'i, ta ina zai yi karatu da yarinya abun da ba'a taɓa yi ba kenan.
Kallon ta yayi yana tunanin to wani kaya ma zai sanya mata ? Palmers oil ya shafa mata yana ɗaukar kayan da ya cire mata yana mai da mata . Idan kina buƙatar wani Abu Kice Uncle Zan sha ruwa ? Ko zanci abinci idan fitsari zakiyi sai ki mun magana kinji Ma'eesha? Yayi Maganan yana kallon ta , da itama take bin sa da kallo ganin babu alamun ta gane Hausan nasa ne yasa shi cewa “ Bata ma fahimta ba ,muje ”...ya furta yana kai hannun sa tare da goya ta a bayan sa , hannun sa ɗaya yana ɗaukar jakar bayan sa .
**
Shigar sa ajin yasa duka kowa kallon sa tare da bin bayan sa da kallo ganin kyaƙyƙyawar yarinya tayi lamo kan ta ko hula babu , gashi a warware yanayin tsayin gashin ta da cikar shi kaman yarinyar larabawa yafi komai tafiyar da hankalin su gare ta. Hango Su Ibrahim yayi da Areef Adam a can sama Captain Isma'il yana basu horo , wani kallo Ali yayi masu yana kauda kan sa a Zuciyar sa yana cewa “ Taɓ ashe duk ma saurin da suke yi sun makara ,aikin banza kenan”. Nufar mazaunin sa yayi yana aje Ma'eesha kana ya dawo gaban inda Captain Isma'il yake yana ƙamewa tare da cewa “Morning sir” .
Ya akayi ka zo a makare? Me yasa baka kai yarinyar section ɗin su ba ? . Captain yayi maganan yana kallon Aliyu don a tunanin sa Ma'eesha makarantar yara na cikin NDA ɗin take yi. Magana ce ta fara tashi ƙasa² . Ai ƙanwar Aliyu ce . Joy ne tace “ Eh nima naga suna kama sosai ”. Ɗauke ta ka kaita idan ka dawo kayi joining ɗin abokan naka . Captain Isma'il yayi Maganan tare da kallon ɓangaren da su Areef suke .
Ok sir . Aliyu ya furta yana isa inda Ma'eesha take , taho ma'eesha ”. Hannun sa yakai yana ɗaukar ta tare da ficewa da ga class ɗin.
“Khaleel dake can nesa mamaki yake yi a ina Aliyu ya samu yarinya? Gaba ɗaya kan sa ya kulle , Ya rasa wane zai tambaya ,gashi abokanan sa sai tambayar sa suke yi wai dama bayan Jidderh suna ƙanwa ce? . Shi dai ya kasa basu amsa , zuciyar sa fal tsoro halin Aliyu na damunsa. A jikin sa yake jin da wani Abu dai gami da yarinyar haka kurum Aliyu ba zai goyo yarinya ya taho da ita ba . Shi da ko magana bayayi bare wai ya tsaya bata lokacin sa akan yara .
Bayan Fitan Aliyu kai tsaye section ɗin yara ya nufa da ma'eesha , ba tare da jin tsoro ko abun da zai kai yakawo ba ya kutsa kan sa zuwa class ɗin Anty docas. New comer . Gyaɗa mata kai yayi yana cewa “ eh a bata abinci da duk abin da zata buƙata ”. Cike da kulawa tasa hannu tana amsan ma'eesha kana tace “ Kai ne ka shirya ta ?”. Eh . Ya furta a takaice. Ok bata wanku ba gaskiya, bari a ƙara mata wanka sai na kimtsa taci abinci . Dama haka tsarin wurin yake , yawanci yaran ma'aikata ne kaman dai irin rainon da Mami tayi masu Aliyu,basu da lokacin yaran su , sai na aiki . Anan ake shirya yara ayi masu wanka hatta kaya da Pampers zaka ga anan ake saka masu . Jin maganan Madam docas yasa Aliyu har yayi gaba ya dawo yana kallon Gaba ɗaya yaran da duka sa'oin Ma'eesha ne maza da mata sun kai 15 .
Eh to Madam hakan na da kyau, amma idan za'a yi mata wankan a dan shiga da ita daga ciki kar yaran waiiiiii....yanda ya tsaya yana ƙasa ƙare maganan yasa Madam docas sakin Murmushi don ta fahimci inda ya dosa ...Ok ai privacy ake shiga dasu kar ka damu . Tom godiya nake. Yana furtawa ya juya da sauri tare da komawa can ɓangaren su , tafiya ce na kusan mintuna talatin kana ya kai shi .
**
Kina tsammanin Haidar ya maida yarinyar nan kuwa ? Kin fa san shi da kafiya akan abin da yayi ra'ayi?.
Kallon General Saleh Yelwa Mami tayi kana ta ɗan kalli ɓangaren da Jidderh take , eh ina da yaƙinin hakan , don tun da yake ban taɓa nuna masa fushi irin na ranan ba. Humm banda abun Ali haidar Haka akeyi da ganin yarinya sai ka dauka ka kawota cikin a halin ka yanda rayuwa tayi wuya a yanzu. Shine dai Fa Genar , yaro ne komai nasa kaman bana mutane ba , a wani fahimce yake.
Mami wacce yarinya ce? . Muryar Jidderh ya katse su , cikin sauri Mami tace “ A'a ba zaki fahimci zancen ba Jidderh kin kammala Assignment ɗin naki ki taho muje kiyi barci . Sauke pencil ɗin hannun ta tayi kana ta miƙe tana cewa “Ok Mami mu tafi , Good night Dad” . Tayi maganan tana Rungume General Saleh Wanda ya manna mata sumba yana shafa bayan ta tare da cewa “ Sai da Safe ” . Janye jikin ta tayi tana yin gaba Mami na bin ta a baya suka nufi bedroom ɗin ta ....Niko kayan jikin jidderh kawai nake kallo. Wasu irin tsadaddun haɗaɗun English wears ne na barci masu laushi da salɓi yana kama jiki. Yanayin shigar yarinyar kaɗai zai tabbatar maka da waye iyayen nata . Wandon iya cinya ne sai rigar bata gama rufe mata ko cibi ba . Sai Hular ta .ƙafarta kuma cikin room slippers ɗin ta .....”.
**
Aliyu baka da hankali ne wai abun da nake ji a bakin su Areef da gaske ne , Aliyu magana fa nake yi ka mun shiru...? Khaleel ke maganan cike da nuna damuwarsa da kuma tashin hankali akan babban lamarin da Aliyu ya ɗauko masu.