← Book details Rainon Soja Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 18

Sashe 4

Rainon Soja Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kallon babba Aliyu yayi kana yace “Babba please Bara na ba Ma'eesha wani abun da zata ci , kaga bata ci komai ba kuma alamu sun....cike da murya ta Basawa Babba yace “Yi sauri”. Nufar fridge Ali yayi cikin sauri yana Buɗewa tare da fiddo da nutri mulki yasan wannan don jidderh ake ajiyewa, Saurin Ɗaukar Glass cup yayi yana cewa “ Mu tafi ” . Bayan gidan suka nufa can ƙarshe inda aka saba hora su duk idan sunyi laifi. A hankali ya sauke ma'eesha yana kallon kyaƙyƙyawar fuskar ta,kana ya fara kokarin aje ta ƙasan wani bishiya mai ƙasa ƙasa don wurin kaman gerdina yake . Buɗe baki Ma'eesha tayi tana fara tsala ihu tare da riƙo hannun Ali haidar tana juyar da kan ta tare da kokarin riko hannun shi irin na yara . Don duka kallon baƙi take yi ma sauran Sojojin. Ganin yanda Aliyu ya ruɗe yasa Babba dan tsagaitawa yana jiran ya rarrashe ta sannan ya bashi horon kaman yanda General yace dashi. Ɗaukar Ma'eesha yayi yana Girgiza ta tare da Buɗe nutri milk din yana fara bata ba bu magana don shi ba gwanin surutu bane ,sai dai yayi mamakin yanda ya iya kula da yarinyar ma haka. Shiru kaji tayi tana amsan madaran tana sha , kusan mintuna Goma kana ta ture bakin ta da kan ta alamun ya ishe ta . Farin hankie yasa yana goge mata bakin ta ,kana ya kalli babba yana cewa " ina jiran ka. Sauke yarinyar ka aje ta can gyefe.

Wani irin kallo Aliyu yayi masa kana cike da haɗe gira ya furta " Naka ka bani horo inda zan aje yarinya wannan Ni ya shafa Yallaɓai ".

Girgiza kai Babba yayi kana ya kalli ma'eesha wanda tausayin yarinyar ya kama shi ,duk da bangare ɗaya na Zuciyar sa yaji zafin kalaman Aliyu. Kallon sa yayi yana cewa "Sit-up zaka yi na awanni biyu daganan sai ka koma Barack . Ɗauke kai Ali yayi yana Maida Ma'eesha wuyan sa tare da fara yin Sit-up ɗin wanda hakan yayi mugun ba da yawa sojojin wurin mamaki . Shi fa yanzu ne ya fara Aikin sojan amma a haka yake sit up da yarinya a wuyar sa babu alamun ya gaji sai dai kawai gumi da sauko masa. Kusan mintuna arba'in ya ɗauka bai huta ko ya tsaya ba ,don yasan yana tsayawa to farko zai dawo , sannan ƙila ma ya amshi wani horon da yafi wannan wuya. Idanun sa sun yi jaaah don yanzu ƙafafun sa sunyi zafi kaman basa jikin sa haka yake jin su ,amma da yake yaro ne namiji sam bai yi yunƙurin dakatawa ba. Hannun Ma'eesha yaji tana wasa da suman kan shi tana gwalon gwalon gwarancin ta na yara , Wannan yasa shi ɗago kai yana zuba mata Lulun idanun sa tare da sakin mata murmushi . Itako sai ta sake Wangale masa baki . A haka ya kammala bai ma san lokacin yayi ba sai da babba ya dakatar dashi sannan . Saɓa Ma'eesha yayi yana ficewa daga cikin gidan tare da komawa NDA a ƙasa .
**

Kai tsaye wurin ƙwanan su ya nufa inda kowa yake da gadon sa kaman zaman hostel . Areef ne cikin sauri ya dirko daga gadon sa yana aje littafin hannun sa tare da bin Ali haidar da kallo yana kuma kallon Ma'eesha da a halin yanzu idanun ta a rufe suke alamu tayi barci. Haidar Wacece Wannan?. Miƙa masa Ma'eesha yayi cike da rashin son magana Aliyu yace “ Ƙwantar da ita Bara naje wurin Major Jibril na sanar masa da dawo wa ta ” . Aliyu kana cikin matsala Major a fusace yake me yasa baka dawo tare da Lawal ba?. Banza Aliyu yayi ma Areef yana ƙoƙarin raɓa sa don ya kwantar da Ma'eesha ne Areef ya kuma riƙo hannun sa yana ƙoƙarin yi masa magana ne Aliyu ya harzuƙa wani irin asharrrr ya danna masa da sai da Sauran mates din nasu dake wurin suka kakkale su . Juyawa Aliyu yayi idanun sa sunyi jah cike da masifa da jaraba ya furta " Ya akayi ne ? Da me wani magana ne ,munafukan banza”! Shiru babu wanda ya tanka sa don sun lura a fusace yake , duk da Wasu dariya suke yi ma Areef ƙasa ƙasa , don yana wulaƙantuwa wurin Aliyu amma kullum yana nan nace dashi. A gadon Areef ya kwantar da ma'eesha yana juyawa tare da ficewa daga Wurin .

“Kaman yanda Areef ya faɗa masa hakan ya faru don ya wahala da horo iri² a wurin Major tun yanayi yana dauriya sai da idanun shi suka fara zubda ƙwallah duk ƙarfin zuciyar sa sannan Major yasa akayi masa ligi-ligi ƙafafun sa sun sha duka da sanda . Da kyar yake iya tafiya don yanzu har 8:pm yayi .

Tun da ya shiga inda suke yake jin sauti kaman na kiɗa tare da ɗan kukan Yarinyar, Muryoyin abokanan sa sojojin yara yana tashi a hankali kaman masu bitan karatu wai nan waƙa suke yi ma ma'eesha😹 . Yana jan ƙafan sa da suka kumbura ga nauyi da jikin sa yayi ya isa inda suke . Gani yayi su kusan shida duka sun zagaye Yarinyar kowa nayi mata Wasa ,Areef na riƙe da ita , Sai Ibrahim dake aikin ƙarƙada Wani roba wai duka don tayi shiru , Sai wasu sun su dake mata waƙar baby girl . Ganin yanda ya shigo yasa su duka jikin su sanyi . Gadon sa ya nufa yana faɗawa ta rigingine kansa na kallon sama . Tun da ya shigo ma'eesha ta gan shi sai ta dakata da ƙananan kukan nata tana gwalon gwalon gwarancin ta . Murmushi Areef yayi yana kallon ta tare da nuna mata inda Aliyu ke kwance yana furta “ Uncle” . Uncle ya dawo. Hannu Ibrahim yasa yana amsan ma'eesha kana ya nufo inda Aliyu ke kwance. Da gudu ta saki zullo tana kuɓcewa daga hannun Ibrahim tare da faɗawa jikin Aliyu tana kwanciya bisa ƙirjin sa tana yin lamo . Sauke Ajiyar zuciya Aliyu yayi tare da ɗaura hannun sa bisa suman kan ta yana shafa mata a..................!

*Littafin Rainon soja na kudine regular group ₦500 vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 .*
*Ga masu buƙatar a tallah masu hajar su zasu iya mun magana sannan kar ku manta wurin yi mun share zuwa masoya baki ɗaya ngd*
[12/15, 1:59 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story .*

Free page 4

________________________
MAMAN TEDDY
Marubuciyar
My Lady boss
Walijaam
Siyasata
Yar maula
Kwaryar sama
The virgin maid
Gidan Ƙwarata
The Sexy Boss
Yar aiki
Bafullatanan Ruga
X world duniyar shahara
Mr romantic
Dijama
Kwarton manya
Yar tsakar gida
Zuma da maɗaci
Sadaka yalla
Yar waye
Taɓarah
________________________
"Da sauran su💃🏻 a yanzu kuma gata ɗauke muku da sabo mai ɗauke da sabon Salo na musamman wato Rainon soja , niko da kaina nace za'a sha duka😹soja da raino ai abun ba'a magana 🤣labarin sai wanda y karanta shi kar ki bari ayi babu ke Hajjaju...labari ne mai tafe da rikirkirteccen Al'amura wanda da fari sai kunce ya abun yake , Gaban yafi farkon🕊️dadi tun a yanzu ina sauraren comments din ku da masu fatan alheri na gode sosai . Sannan masu buƙatar daga farko don Allah kuna rinƙa tambaya ne a wasu groups da kuke ciki , idan kuka biyo Ni ayyukan da hidimomin nawa suna da yawa , bana samun damar turawa ta private 🙏🏻. Gare ku masu buƙatar fara payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake ; Regular group ₦500
Vip group ₦1000
SPC payment ₦1500
Via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 Vtu transfer number 09061466409 Yan Niger zaku turo da katin Airtel 500f .

•••••

Tun da ya shigo ma'eesha ta gan shi sai ta dakata da ƙananan kukan nata tana gwalon gwalon gwarancin ta . Murmushi Areef yayi yana kallon ta tare da nuna mata inda Aliyu ke kwance yana furta “ Uncle” . Uncle ya dawo. Hannu Ibrahim yasa yana amsan ma'eesha kana ya nufo inda Aliyu ke kwance. Da gudu ta saki zullo tana kuɓcewa daga hannun Ibrahim tare da faɗawa jikin Aliyu tana kwanciya bisa ƙirjin sa tana yin lamo . Sauke Ajiyar zuciya Aliyu yayi tare da ɗaura hannun sa bisa suman kan ta yana shafa mata a Hankali. Girgiza ta yake yana ɗan jijjigata da jikin sa , kana ya lumshe Lulun idanun sa ba tare da yace da sauran abokanan nasa komai ba .

Kallon Ibrahim Areef yayi kana ya maida kallon sa ga Aliyu da har a wannan lokacin idanun sa suke a lumshe tamkar mai tunanin wani Abu koma muce babu shakka wani abun yake tunanawa . Sauke Ajiyar zuciya Ibrahim yayi yana zama Gyefen mattress din Aliyu , “Haidar”! Ya ambaci sunan shi tare da mai da kallon sa sosai bisa kan Fuskar Aliyu wanda a yanzu ba tare da ya ware idanun nasa ba sai motsa laɓɓan sa da yayi yana cewa “ Ya akayi?”.
Chapter 4 · 0% Book details