← Book details Rainon Soja Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 18

Sashe 13

Rainon Soja Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami ya katse shi tana caɓe baki tare da danna horn da sauri sojojin dake gadin gidan suka fara buɗe masu Gate na farko tana shigar da moton ta ciki . Cigaba tayi da cewa “ Yayi mata Aure? , Ai babu wanda zai Aura wacce ba'a san Asalin ta ba , ana duba zuri'a ne da asali kamin ayi Aure , kaga kuwa sai dai shi da yaji ya gani ya Aura.!

Allah ya kyauta Mami” , Khaleel ya katse Mami cikin sauri , ai koda zai mutu ba Aure ba zamu haɗa jiɓi da Wannan yarinyar ba , a yau sai nasa Daddy ya raba shi da Wannan yarinyar Mahaukaci! Kana SOJA kana fama da kan ka wani RAINO? saboda bamu isa da shi ba. Ya nuna mana yanzu ya girma . Mami munfi ƙarfin shekara yana gaba dani duk takan yarinyar nan , Shiyasa ma ban miki maganan ta ba , na bari sai yau kwagani idan kika zo .!

Hummmm Na tausaya maka Ali yau na tausaya maka a hannun mahaifin ka , Wannan abun da kayi shine ma ba zan taɓa..........Hannun sa yakai yana buɗe Murfin moton ba tare da yajira jin me mami zata ce ba yana ficewa tare da ɗaukar ma'eesha yana nufar cikin gidan .

Tsayawa Duka suka yi suna sakin baki yayin da Jidderh sai a yanzu ta samu damar magana. Kukan rigima da sarganci tasa tana cewa “ Wayyo Mami kin gani ko ,tun yanzu baya SO na! Wallahi bazaata zauna mana a cikin gida ba....Shiiiii it's Okay ." Ki daina kuka a yau Za'a raba shi da Yarinyar nan , kinji Jidderh?” . Ok Ya Khaleel ka tabbatar Bata kwana a cikin gidan nan ba . Gyada mata kai yayi yana ɗaga mata gira tare da sakin murmushi yana mai cewa “ yau zata bar gidan nan , kinyi farin ciki ?”💃🏻... Murmushi tayi sosai kana ta ce “yes Ya Khalil " . Ok Let's go in”. Yayi maganan yana kai hannun sa tare da bude ɓangaren ta tana fita shima ya fito . Ita ko mami ta dau mintuna biyu ta kasa fitowa don ta rasa me wannan al'amarin ke nufi?” . Sukam Khalil da jidderh bayan Haidar suka biyo .

A hankali Mami ta furta “ Wallahi ban taɓa ganin mutum irin Aliyu ba , Ni sam ba haka zuciya ta take ba da Ganar yake cewa Ni ya biyo, nasa halin da banbanci . Idan ya biyo halin zuriyar mu da zafin ran su na shiga uku”! Hannu tasa tana goge gumin da ya sauko mata . Tana furta “ Ƙanwata akan SO da wani matsiyacin ɗan ƙauye ta gummaci tabar arzikin tabar komai nata danginta tayi nisa damu duka akan fushi ne irin na Aliyu.....!!! Ta yi maganan da ƙarfi tana Furta " Ya ilahi ya ALLAH! Danne wani Abu tayi a zuciyar ta tana sauko da ƙafarta tare da wuce Sojojin da suke aikin mata Barka da dawowa. amma sam bata ta kan su kai tsaye Falourn ta ta wuce ......

Barka da dawowa Hajiya”. Uwani ina yaran nan suke ? . Ɗan ƙasa da murya Uwani tayi kana tace “ Naga sun nufi direct inner room ɗin ki . Hummmm.....Jan numfashi Mami tayi tana saukewa kana tace “ Ok an gama haɗa masu Abincin nasu ?. Eh Ranki yade an gama” . Girgiza kai Mami tayi babu walwala ta kutsa ixuwa karamin falon ta inda daga nan zai kai ta zuwa Bedroom .

Tsaitsaye ta gansu , Khaleel da jidderh wannan yasa Mami dan kallon su tana cewa “ Meke faruwa? Ba ku isa Bedroom din ku ba ,ku watsa ruwa ku fito kuyi lunch " . Mami ke maganan muyi wanka muci Abinci kike yi , while shi Ya Haidar gashi nan a Bedroom ɗin ki yafa ƙwantar da yarinyar ? Tuurusss...!!! Mami tayi . Tabbas Ali da Abin da yake nufi . Ta furta hakan a Zuciyar ta .

Ok ku tafi ai Daddy na nan yanzu zaku gan shi kuje ku shirya .

A'ahhh....Sojoji na Sojoji na da an ganku an ga Marshal Khalil da Marshal Haidar ? Ina zakin nawa ? . Muryar General Saleh Yelwa ya katse su wanda yake shigowa tsakiyar falon .

Cike da Tsiwa Jidder da masifa ta fara cewa “ gwarzo kuma Daddy , ai yanzu Ya haidar bata soja yake yi ba , ta raino yake yi . Kaga kuwa mu da ganin ya zama soja ƙila sai dai a wata Duniyar domin Yarinyar da kuka korasa da ita ashe rainon ta kawai yaje yana yi a NDA .

Ɗan haɗe fuska Ganar yayi kamin yace “ Wa zai mun bayani yanda zan fahimta , saboda jidderh ƙarama ce ban gane me take nufi ba .

A hankali Khalil ya fara labarta masa Komai kana ya kare da cewa “ Amma Daddy ya maida hankali a karatun sa sosai , don duka termer 1 shine zaƙwaƙurin ɗaliban soja da yafi kowa , Rainon bai hanasa yin abun da ya dace ba. Kullum yana zuwa trainin........What? Ali....??? General Saleh Yelwa ya kira sunan Aliyu a wani hasale. Nufar Bedroom din Mami yayi ba tare da ya tsaya sauraren su ba duka .

Dariya ya same su suna yi Ma'eesha har da ƙyaƙyatawa tana riƙe da hannun Aliyu ta kifa kan ta bisa taffan sa . Yanzu kiyi barci idan kin tashi nayi Miki wanka kici Abinci ko? . Eh Ina mama na to? . Kai Aliyu....Haidar.....!!! Muryar Daddy ya katse su wanda nan take ƙirjin ma'eesha ya buga da ƙarfi bata taɓa ganin mutum namijin zaki irin Saleh Yelwa ba , fushin sa ya danne na Aliyu . Kamin tayi wani magana tuni taga da hannu ɗaya ya damƙo wuyar Aliyu yana buga shi da bangon Bedroom din sai da yayi kaman zai zube . Wani irin bahagon mari na soja yake sauke masa ....Wanda hakan yasa Ma'eesha gigicewa tana sauko da gudu daga gadon tare da nufo inda Daddy yake dukan Aliyu tana shigewa jikin Haidar......Damƙar ta Ganar yayi yana miƙa mawa Khalil tare da cewa “ Maza fice mun da ita daga cikin gidan nan , ka tabbatar Ali shi da ganin ta har Abada....!

A'a Daddy ..!! Muryar Haidar ya katse su ɗago idanun sa yayi wanda saman giran sa jini ke zuba saboda dukan da Daddy yake masa da hadasa da Bangon da yayi . Daddy kar ku fara..!! Mu kake ba command???? Aliyu....???? Ni soja ne Mahaifiyar ka police ce. Kai kuma yaron soja ne. Daddy yayi Maganan a wani irin fushi . Yau zan kashe da duka har sai kai da bakin ka kace ka tsane yarinyar nan a fitar maka da ita a Rayuwar ka ...Khalil ɗauko mun rodi duka ne zan maka irin na soja ...kasan wani irin duka ake yi ma soja idan yace zai bar aikin sa? Duka ne ake yi masa na wata kila rayuwa ko mutuwa . Yau da bakin ka Sai kace a bar da yarinyar nan Rayuwar ka saboda izayar da zaka shaaaaa. Kauuuuuu... Kaji ya dauke fuskar haidar da mari mai tartatsi. ihu ma'eesha keyi wanda nan take ta sume gauuuu numfashin na ɗaukewa a hannun khalil,Daddy kuwa baya takan su duka ne yake ma Aliyu irin na soja. Yayin da Jidder ke kuka iya ƙarfin ta tana cewa “ Mami Daddy zai kashe mun boo miee...zai kashe mun ya Haidar! Daddy kayi haƙuri ka rabu da ya Haidar .....ba zan rabu da Haidar ba sai da bakin sa yace yace a fitar da yarinyar nan daga Rayuwar sa . Kuka mami ita kan ta keyi , don tasan dukan ganar bana lafiya bane ba.

HAIDAR kayi magana kace a tafi da Ma'eesha tabar rayuwar ka .

Hummmm jan numfashi yayi da kyar kana a galabaice yace “ Mami a da baya tausayin ta ne ya sani na dauke ta don na raine ta,amma a yanzu ji nake zan mutu sau ɗari saboda ita ta rayu ,ba zan taɓa rabuwa babu Ma'eesha ba . Ko mutuwa nayi zan dawo....! Ok Ganar ya furta yana ɗagasa sama yana buga shi da ƙasa ƙashin bayan sa na Buguwa da tiles . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una furucin da mami tayi kenan tana rushewa da kuka tare da cewa “ Ganar baya Numfashi...Ganar Haidar ɗina zai mutu , baba na zai mutu Haidarrrrrrrrrrrr..............!
*Labarin fa har yanzu bamu fara komai ba 😻💃🏻 daɗin wannan ɗanɗano ne ongan yana a gaba . Kar ku manta littafin RAINON SOJA na kuɗi ne regular group ₦500 kacal Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932© Ayshatou Mamanteddy.*

*Buxuwa Empire🐪08126535394*
Tanayin ayyukan gyara sunna masu yawan gaske haka ƴammata , zawarawa masu shirin aure suna iya yi mun magana , sannan kina zuwa ki faɗi buƙatar ki kwai zamu baki amsa mutane sunyi yawa ne kuyi haƙuri don Allah...

💥 Muna aikin rufe na miji a kwalba sai kin tabbatar da idan miji ki baya da hali karki zo mu rufe bawan Allah .

💥 Muna aikin mallaka na Baƙin ruwa wannan muna ma saurayi da yaƙi fitowa ayi mgnn aure ko miji mara kyauta...

💥 Muna kiranye ko mallaka na ramin tururuwa Hajiya ta idan kinason kiga mijinki yaƙi zaune yaƙi tsaye kula da tattali ya zame masa dole to don Allah kiyi aiki ramin tururuwa kiga yanda ake yi

💥Muna aikin kwai mai rubutu a jiki wa macen da takusa aure ko auren da yakai shekara goma ..

💥 Muna aikin zuciya mai allurai a jikin zuciya baki ɗaya ki tambayi meye aikin da akace maki da zuciya za'a yi shi muna kiranyen sa , muna mallakar sa akan koma meye koda kinga wanda kk so ne inshallah indai ba zakiyi mugunta ko wani nufi a kansa ba kina iya Wannan aikin .sai dai aikin mu babu kauce hanya .

💥 Mallkar tumfafiya da ganyen tumfafiya na turare aiki gagare ga wanda ta shirya.

💥 Mallaka da kiranye na kan rago mai laya guda 84 kinga aikinnan bayanin sa bazai daɗi ba ...aikin mu babu kauce hanya.

💥 Aikin kifi da ake ratsawa a bushiyar Rimi
Chapter 13 · 0% Book details