← Book details Rainon Soja Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Rainon Soja Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ina kuke masoyana💃🏻 nasan yawan ku kun haura irin billions ɗin nan😹 kuyi mun share page ɗin nan ga mutanen ku nasan ƙaranci yanda nake da jama'a billions haka kuma ƙaranci 1 million people😹. Ga masu buƙatar na tallah masu hajar su ƙofa a buɗe take zaki zanzare kuɗin aljihun ki ayi Miki tallah don samun customers sai ki tuntuɓeni ta WhatsApp ga nombibina nan a daga ƙasa*

*Labarin RAINON SOJA na kudi ne kar ki fara karantawa tun fari idan kin san baki da kuɗin saya don Allah... Book 1 free ne shine wannan ,idan mun gama shi book 2 na kuɗi ne kar azo ana ayi haƙuri da sauran su , Sannan group din littafin guda uku ne 3 , muna da na ƙasa shine ₦500 (regular group) sannan aƙwai yan tsakiya shine ₦1000 (Vip group)sannan aƙwai na sama shine ₦1500 (Special payment)...Zaki iya payment din ki ta wannan account number 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank shaidar biya ko katin MTN ta wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne ga MTN numbern da zaki tura tanan 09061466409 zaku iya fara payment naku tun yanzu don na samu damar sakaki group da wuri kamin mutane suyi yawa kunsan hidimomin da yawa ...to hajiya ta wannan salon tafiyar ta daban ce kar ki bari ayi babu ke a barki a baya .labari ne mai ɗauke da darussa 😹💃🏻✨yanda yazo a ƙarshen shekara haka daɗin sa ya kasance na musamman kun san alƙalamin mmnteddy baya rubuta labari mara ma'ana ato.*

*Anty Aysha Mamanteddy*
[12/15, 1:59 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and sympathetic story.*

_Book 1_
_Free page 2_

*Littafin rainon soja book 1 free ne , book 2 na kuɗi ne regular group ₦500 Vip group ₦1000 special payment ₦1500 .*
*Zaki turo da kuɗin ki ta wannan account number 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932. Idan Vtu transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409 ku fara payment da wuri a page 10 Free page zai ƙare*

Maman Teddy.
Marubuciyar
My Lady boss
Yar tsakar gida
Bafullatanan Ruga
Walijaam
The sexy Boss
Gidan Ƙwarata
Siyasata
The virgin maid
Habibi da'iman
Mr romantic
Duniyar shahara x world
Yar Aiki
Dijama yar Fulani
Zuma da maɗaci
Kwarton manya
Da sauran su .

Yayin da Major Jibril cikin Tsawa yace " Kai ba yaƙi aka ce zaka tafi ba , You Are under punishment...shine har kake tambayar Helmet da Armor rigar kariyar harbi? , Amfanin mene Helmet zai maka ? Ruwa kuma ba zaka sha shi ba har kuje ku dawo ban yarda ko Hutawa kayi ba . Cike da ɗaga murya tamkar saukar Aradu Aliyu ya ƙame tare da furta " Yessss sir ". Yana furta hakan ya fara cika umarnin Major Jibril yayin da Wani soja dake gaba dasu ɗan ND 3 yake bin bayan Aliyu haidar da ya fara gudun sassarfa kaman yanda Major yace dashi . Tun daga jaji yake gudu a wani irin tartsatsin rana gashi ba hulan su ta soja wanda yake tare dukan Rana ,ko ruwa kuma ba'a yarda mishi yasha ba .

**
A hankali take bin bord ɗin da kallo , tana sakin Murmushi tare da kai laɓɓanta tana kissing ɗin zanen fuskar Aliyuu Haidar . I love You Booo mie. Ta furta tana shafan giran sa wanda yake a tattare ya haɗe kaman hadari. Ƙamshin turaren da taji ne yasa ta saurin juyowa tana kallon inda Mami ke saukowa cas-cas-cas cikin shigar suit ƙafarta tasa cover irin na mata , Fuskar ta cikin baƙar gilashi da gani kasan no respect ba zaka taɓa cewa itace ke da yara uku maza biyu mace ɗaya ba wato jidderh, Khaleel da kuma iyayen kafiya da naci wato Aliyu haidar. Mami....! Ƙaramin Muryar Jidderh ya katse Ni cike da yarinta tana sakin mawa Mahaifiyar nata fara'a . Cikin sauri Mami ta nufo inda take tana rage tsawon ta tare da hugging ɗin jidderh tana cewa " Morning my baby love". Ana nan kina kallon Khaleel da Aliyu ? . Yes mami i really miss Booo mie da kuma Ya Khaleel . "Hummmmmm" Hajiya Nafisat ta sauke Sanyayyar ajiyar zuciya kana ta kai hannun ta tana shafa kan Jidderh cikin sanyi da Muryar rarrashi ta furta " Sorry my lav zasu dawo nan kusa bada jimawa ba '.

Gyaɗa ma Mami kai jidderh tayi tana sakin Murmushi haƙoranta da wawulo na bayyana wannan yasa Mami dariya tana cewa"Alright muje kiyi breakfast sai na kai ki school daga nan Ni na wuce Office . Hannunta ta kama suna nufar Dinning room.....yanda Mami ke tafiya kadai zaka fahimci zaman gidan Na sojoji ne masu kaki komai oya-oya ake yin shi babu shauƙi irin na mata , tun tasowar yaran nasu a haka cikin gidan ya kasance, Daddy Soja Mami Police yar sanda 🫡 . Haka suka taso basu san suga iyayen su kullum a tare ba ,idan yau Daddy yana hutu to gobe Mami zakaji an sauya mata wurin aiki ko bata gari , dukan su yaran sun taso cikin horan sojoji ne ,don gidan baki ɗaya har ta masu girki cook sojoji ne , masu kulawa dasu sojoji masu kai su school sojoji Wannan yasa duk horo suke shan baƙar wahala , gashi General Saleh Yelwa ya ƙudurci son ganin yaran nashi sun zama tamkar shi Wato Sojoji . Wanda a yanzu a lokaci guda Duka su biyun suka fara NDA . A yanzu Aliyuu Haidar shekarunsa sha shida ne Bama ce ya cika ba ,sai Khaleel babba shine gaba da Haidar shi kuma shekarun sa 17-18 don tazaran su ba nesa bane shiyasa kan su yake daya ,sau tari wanda basu sani ba ma kiran tagwaye suke yi masu .

Sai dai Khaleel na fama da shan Wahalar Aliyu saboda Neman magana irin nasa ga kafiya da fusata ga saurin ƙufula da zuciya, a haka kuma yake zafin son Ƙanin nasa . Wannan shine taƙaitaccen labarin Gidan General Saleh Yelwa da iyalan sa . Bari mu Jah gaba muji wani hali Aliyu yake ciki a yanzu .

**

Tafiya ce suka yi ta mai dogon zango yayin da Ali ya haɗa gumi iya gumi a wannan lokacin har sun kai wuraren Gwargwaje sannan suka kuma juyowa zuwa jeji. A tsakiyar wani ƙaramar jeji ne kan hanya idanun Aliyu da Yaron Captain Lawal suka sauka kan Wata moto da tayi ƙwatsa ƙwatsa a titin wuta na tashi ta sama da ƙasanta . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kalmar da Lawal yayi kenan yayin da Haidar ya cigaba da Gudun sassarfa yana ƙoƙarin wuce moton . Amma kai baka da Hankali Wani irin mara imani ne kai Ali ? Wucewa zaka yi kana ganin halin da Mutanen moton ke ciki . Tsayawa Haidar yayi yana ƙamewa tare da seniority ya furta " I'm under punishment Sir ".

Kama kai Lawal yayi kana yace " Mu ceci mutanen nan ka dakata da Wannan Gudun da kake yi haka nan ,idan mun koma xanyi ma Major bayani . Ok sir . Aliyu ya furta yana saurin ƙarikowa inda moton yake hannun sa yasa duk da ƙarfen da tayi zafi ga moto ba karama ba . Tura moton suka yi da ƙarfin na sojoji suna ɗaga ta , Saurin rufe ido Ali yayi don wannan shine karon shi na farko da ya fara ganin gawa ido da ido a rayuwar sa . A takaice gaba ɗaya moton babu wanda ya shura dukan su sun zama gawa, gashi mutuwar wahala abun ba dadin faɗi da gani sai ka zubda masu da Hawaye jini ne kawai ke malala.....Hu'uhhhhmmmmmmm Suka ji wani jan iska da karfi anyi tare da fara tsala ihu irin na yara jarirai . Hasbunallahu wani'imal wakeel ". Lawal ya furta da sauri yana kai hannun sa yana fuzgo yarinyar da take maƙale jikin mahaifiyar ta , har ta fara sanƙarewa.

Aliyu Ruwa ruwa Aliyu Ruwa kawo ruwa .! Yana maganan hankalin sa a tashe da kuma yanda yarinyar ke ihu iya ƙarfin ta numfashin ta na kokarin ɗaukewa.

Kallon Sa Aliyu yayi kana yace " Ai Major yace ba zan taho da ruwa ba ko ka manta ne ? .

Ba tare da ya tsaya ba Aliyu amsa ba ya fara gudu da yarinyar a hannun sa ,hakan yasa Aliyu shima bin bayan sa don su nemi ruwa su bata a wannan falfalan hanyar jejin da babu gida babu gida baya ,itako yarinya ƙiwuya ne yayi mata yawa ganin bata san fuskokin ba. Wannan yasa ta take kuka har da shirin riɗewa . Sir Lawal ka daka ta gudun nan , wannan ihun yarinyar yayi yawa kaman mun sato ta? . Cak Lawal ya dakata da gudun yana kallon Aliyu kamin ya juya yana kallon kyaƙyƙyawar fuskar yar lukutar yarinyar wanda nan take ya furta " Laaa Aliyu kalla? Kai take kallo tayi shiru Aliyuu kalli dariya ma take yi maka yanzu . Ɗaga gira Aliyu yayi yana zuba ma yarinyar Manyan idanun sa da suke warwaje na rashin tsoro , Ganin yanda take Wangale masa baki kaman ba itace mai kukan ba ko kuma ta san shi yasa shima jin wani irin yanayi lokaci ɗaya na shigar sa gami da yarinyar . Amshe ta Ali zata yi shiru a hannun ka yanzu . Ba musu Aliyuu ya miƙa hannun sa yana amsan Yarinyar da take ta Wangale bakin nata tana dariya tare da miƙa masa hannayen ta duka na yara . Lawal ne ya bude baki zai masa magana da nuna masa yanda zai riƙe yarinyar don ya lura bai ma iya daukar yara ba , Kawai caraf yaga ya ɗaga yarinyar yana ɗaura ta bisa wuyan sa tare da riƙe hannayen ta a sama . Zamu iya tafiya Yallaɓai.! Yayi mganan cike da amsa kuwa da ƙamewa , cikin sauri Lawal yace " Kai Ali mu aje wannan duk abin a gyefe yanzu ina zamu kai yarinyar nan. ?

Shiru Aliyu yayi masa yayin da Lawal ya cigaba da cewa " mu tafi Barack da ita. Mu sanar mawa Major.
Chapter 2 · 0% Book details