← Book details Rahima Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 9 OF 48

Sashe 9

Rahima Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Mutuwa kenan, daci Mai kore Zaki, Mai raba da da mahaifi, Mai raba Mata da miji, Mai raba danuwa da danuwa, Mai raba masoyi da masoyi, Allah yasa mu cika da imani.
Duk da cewa Ubangiji yace bai halicci wani don wani ba, a ko yaushe muka yi rashin daya daga cikinmu al'amarin Kan zama sabo, bamu iya dauriya dole muyi juyayin rashi da tausayin kanmu tare da fargaba da tunanin cewan muma fa komin dadewa wata rana sai mun tafi lahira. Allah yasa mu cika da imani
Maganar halinda yanuwa da abokan arzikin marigayi Rabi'u suka kasance bata ko taso ba balle matarsa Rahima, Hajiyarsu kawai Allah ya saukarwa dauriyya ta dake ita ke baiwa jamaa hakuri

Bayan kwana bakwai kowa ya watse sai wasu daga cikin dangin uban Rabiu da kanun Hjy Kaltume Mata biyu don suci gaba da debe musu kewa. Hayatu ma Kan kawo matansa su yini. Wani ikon Allah rasuwar Rabiu ne ko shiriyar Ubangiji ne yasa yasa su natsuwa da kama kansu har jamaa na mamakinsu oho. Shima Haseeb matarsa na zuwa ta koma da laasar, Maryam ma na tafe duk bayan kwana biyu, jamaa kowa nata kokarin ganin an debe mata kewa.

Ita kuwa sai kallonsu take, hawaye sunki kafewa a idanunta musamman idan ta dauki Abdul tana bashi nono. To tun hawayen na zuba har sun kafe ta fara kukan zucci. Idan ta tuno rayuwar da suka yi, watau haka Allah ya kaddari rabon Abdul ne yasa akayi aurensu a gaggauce, rabuwar ma Allah ya kawo kwatankwacin hakan. Oh Allah ka jikan Rabiu ka sanyaya masa, hakika sunyi rayuwar auren daya dace, rayuwa mai cike da nishadi da farin ciki abin shaawa fa kowa, da karshen tazo Allah yasa shakuwa tsakaninsu bayan so da kaunarsa da suka fara tasiri a zuciyarta, Ashe Wai ba za akai ko Ina ba, Ashe rayuwar tazo karshe.... Hawaye masu zafin gaske suka gangaro zuwa kumatunta suka diga kirjin Abdul, ya saka kuka, ta lallasheshi, ita tama manta Yana bisa cinyarta, da Hjy Kaltume ta lura ta shiga yi Mata fada, ta dawo tayi nasiha taci gaba da lallashi, maimakon tayi shuru hawaye sai Kara fitowa suke Saida ita kanta Hajiyar da sauran mutane suka koka.
04/09/2020, 17:24 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami
11
Kafin ta gama takaba 'yanuwa, iyayenta da dangin mijinta kaf sun nuna mata gata Kuma ita wata ce a gare su don Haseeb ma ba a batun dawainiyar da yake musu ita da danta Abdul karami, tun bai saba da wan uban nasa ba har yai sabo dashi kwarai saboda yawan dauka da fita dashi yawo da yake in baida aiki sosai a asibiti...
Kwanci tashi ba wuya Rahima ta gama takaba, ta Kara sati guda da kyar kana ta tattara kayanta tace gidansu zata koma. Wani sabon tashin hankalin, ranar Abu ya koma sabo to amman barin gida ya zama dole don ci gaba da harkokin rayuwa.

Bisa yarjejeniyar ba zasu amshi Abdul ba sai ta sami wani mijin ta goya danta suka koma inda tafi wayo, gidan Alh. Mamman.
Makarantar da take koyarwa basu saketa ba ko bayan gama bautar kasarta nan suka dauketa aiki taci gaba da koyarwanta.
Gama takabarta keda wuya masoya suka ce sallamu alaikum, harda wani abokin Rabiu da suka kare school tare, wani ikon Allah saurayine shi ko auren fari bai yi ba, ya kasa dumfararta da kansa sai letter ya tura mata Wai Yana jin nauyi, yadda bata saurare shi ba haka taki sauraren kowa cikin zawarawan dake mata Kara kaina tun daga wajen aiki har gida, da ma wani abokin Alh Abbas mijin Maryam Wanda uwargidansa ce ta rasu ta bar diya biyu, Yana son suyi aure ya rike Mata da ta rike masa nashi, shima bata cewa Abbas din tana yi ko ah ah ba, kusan duk Wanda ya nemi kusanci sai tace a bata lokaci tayi shawara, a zahiri kuwa ra'ayin sake auren ne bashi a zuciyarta, a nata tunanin ma da za a barta haka zata yi zamanta din tasan zata iya tsare mutuncin kanta dana iyayenta tunda Allah bai halicceta kharija ba, wai don a matsa mata da batun auren ne taki yaye Abdul da ya Kai kusan shekaru biyu. Umman tayi-tayi ta gaji tasa mata ido, gara bata son bacin ran Rahima daidai da kwayar zarra, suka ci gaba da lelen Dan da yake gudu koina, wani burgewa ma sai ya gama yawonsa ya dawo ya zauna yace 'Mami zan Sha mama'
Irin sangarcewar da yayi Maryam ta taho ta gani ta fara masifa, Umma ta fara kakkare Rahima, ita din ma tace Umma karki kula surkulenta, shin don ta yaye Walida sai tace sai na yaye Abdul?"

Umma tace "itama ba yayen Allah tayi ba ciki ya sa akayi saurin hanata nonon.".
Rahima tayi dariya "Ah to gane min hanya Umma na makaho da yaso tsegumi. Kin ganni ni ba miji ba, Ni ba wani kwakwkwaran bazawari ba mene nawa na hanzarin cire yaro a bakin nono, Maryam ko tausayin Abdul ma ba kya ji."

Taja tsaki "Ke da Umma ke ban tausayi sabida ga gaskiya kiri-kiru Kun take, shun Umma kin kalli diyar taki da kyau Kinga yadda ta kode tana kanjamewa?"

Cikin damuwa tace "Na lura sosai, nima ramar nata har tsoro take bani, yarinya taki sakin ranta ta hakura, wallahi kullum fadar da nike mata safe da yamma kan ta fauwalawa Allah rashin da muka yi shi Kuma Allah yasa yana cikin rahamar Ubangiji.'

Maryam ta gyara zama daman gangara take nema tace "Umma ban tari numfashinki ba, ya za ayi ta samu natsuwar hankali tana zaune muku haka kawai. Ni a ganina duk halinda data shiga laifinku ne, baku matsa mata ta samu miji tayi aure? Kawai Kun Kyaleta sai biye mata kuke, har kin yayen nan don kar a sami kafar mata batun aurene."

Rahima ta harari Maryam "Umma ki daina saurarenta kinsan halinta da zuga."
Umma ta nisa "Wannan karon Kam gaskiya take Fadi na Kuma gano kamshinta bari Baffanku ya dawo."

Ta sunkuyar da Kai ta dafa Umma "Don Allah karki hadani da Baffa Umma nayi alkawarin yayesa cikin satin nan.".
Maryam tayi Mata gwalo tukunna kafin taci gaba "Ai ba yayen ba ta fitar da miji shine batu, tayi alkawarin zata amince ba zata kara kin sauraren wani abu har Allah ya zaba mata mijin."

Rahima ta rike haba. "Oh ni na shiga uku, Maryam hala kudin kanfen Alh Surajo ya Baki?"..
Umma ta kallesu "Wani ne Kuma haka?"

Maryam ta gyada Kai "Kyaleta Umma da 'yar halas take magana, amma ba za aji mutuwar uwar sarki a bakina ba, ta fada miki ko waye shi."

Baki dai shi kan yanka wuya, dole ta yaye Abdul din ranar jumma'a bayan an aikawa kakarsa. .
Kaji, zabbi,madara dasu bornvita da sauran tarkace banda sabbin tufafi aka tarkato, banda buhun shinkafa da jarkar Mai, matan Hayatu suke takewa Hjy Kaltume baya wajen zuwa diba Dan yaye, shima wan baban nasa kudi ya bashi matansa kuma crates din kwai.
Rahima na gida bata futa aiki ba saboda zazzabin da ciwon nono ya sa Mata, ganin bakin yasa ta tashi ta zauna.

Bayan an gaisa Abdul ya dare bisa cinyar kakarsa yana baje sabbin kayansa.
Umma nata zubawa su Hjy Kaltume godiya.
Hajiya tace "Duk aikin iyayensa tawa tukunyar farfesun na gida sai ya taho zai ci.
Umma ta kalli su Hayatu "Madallah Allah ya baku ladan zumunci."
Yace "Ba komi Umma Abdul danmu ne koda Rabi'u na nan balle yanzun da kasa ta rufe idanunsa."
Tun dai Rahima na dauriyyar Kar suga kwallan da take kokarin maidawa har ta bara sai nishin kukanta suka, hankalin kowa ya tashi din sun san ba shakka uban Dan ta tuna.

Ana haka Baffa ya shigo cikin sauri ya tsugunna suka gaisa da bakin kana ya fara rarrashun diyarsa cikin kalamai masu taushi har hankalinta ya koma jikinta ya kara yin godiya ya fita..
04/09/2020, 21:15 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA...doc by jami

12

Sun dade suna taba hira tun Rahima bata saki jiki ba ta warware a nan ne Jamila ke ce Mata "Kiri-kiri kin guji gidanmu Rahima."
Haulatu ta kalli uwargidanta tace "Ke dai bari Yaya nima abinda ke zuciyata kenan."
Rahima tayi murmushi tace "Aikine yai min yawa a school amma kuyi hakuri Ina nan zuwa."

Hayatu ya kalli matansa cike da jin dadin ganin yadda suke tafiyar da al'amurransu yanzun sabanin da, yayi murmushi yace "Idan baki taho don komi ba Kya zo mana murnan tafiya sauke farali ko don Allah yayi bana za muyi arfa Ni da Jamila."

Tace "Iye! Shine baku Fadi ba tun zuwanku, laifinki nan wannan Aunty amarya."

Haulatu tace "Yi hakuri wallahi labarin dana kunso in fada miki suna da yawa ganinki haka yasa nayi sanyi, da gaske Ya Haseeb ya biyawa Maigidan da Uwargida kujerar hajj bana."

Jamila ta amshe "Itama amaryar anyi mata alkawarin badi da ita insha Allahu."

Umma ta kalli Hjy Kaltume tace "Masha Allah Kai Allah yai wa wannan yaro albarka, shi dai dukiyarsa ta dawainiya da jama'a ce, kunga hidimar da yake yiwa su Abdul kuwa?"
Hjy Kaltume tace "Don Allah ki bar wannan maganar Habiba, kula dasu ya zama dole."
Rahima ta kalli su Hayatu tace "Naji dadin jin labarin nan, Allah ya nuna mana anje an dawi lafiya, shi Kuma Allah yai masa sakayya yasa muji na Aunty amarya haka badi idan muna raye."

Daga nan sukayi sallamar tafiya, Rahima ta rakosu kofar gida tayi musu alkawarin ziyartarsu wani satin.
Chapter 9 · 0% Book details