Sashe 41
Rahima Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Hajiya ta kalli Umma "Saurara mata tayi Mana bayani watakila ta fi mu gaskiya.".
Sai a nan Haseeb ya tanka yace "In dai itace yanzun zata kashe miki jiki da lafuzanta ki amince da manufarta ko banza ba Kya ganin laifinta."
Rahima ta kallesa "Shikenan Yaya bari in musu bayani idan basu amince ba wallahi na hakura, amma kafin nan ka fadu hujjojinka na rashin son hadamu din."
Ya gyara zama "Hujjoji?, Halayyen Zuwaira ai ba boye suke ba, kuna nesa da juna ma ban tsira da korafinta na Ina rashin adalci tsakaninku ba, fitinar yau daban ta gobe daban Wanda da ina biye mata da tuni mun rabu."
Rahima tace " Kuna jinsa ko? To ai ni abinda ban son ya faru kenan, da can din ai da halinta baka rabu da ita ba sai bayan aurena? Ko Ni ce zanyi zargin dalilin wata ka rabu dani, daga nan Kuma kulalliyar gaba ta kullu tsakanina da yaranka har abada saboda mai zurfin tunani ne zai gane cewan gajiya kayi da halinta ka Kai makura ne silar rabuwarku, batun danne hakkinta da take yi ma zaman mu a tare zai sa ta gani idan ana zaluntarta din, Kai kuma za a rage maka yawan zirga-zirga tunda iyakinka na natse waje daya hankalinka zai fi kwanciya."
Umma ta daka mata harara "Ai ba dai iya magana ba 'yar ka iya, shi ba wadannan matsalolin suka dame sa ba."
Yace "Ta fa san duk abinda nike gudu Umma."
Hajiya tace "Rahima zaki iya zama da Zuwaira da halayyenta?"
Ta gyara zama tace "Sai maganar halayye muke Hajiya amma bamu tsaya munyi nazarin shin wane irin hali Aunty Zuwaira ke dashi ba kamar yadda masu ilmin sanin halayyan dan Adam suka kasa halayyen mutum har kashi uku.
Na farko akwai halayyen da basu gyaruwa kwata-kwata, misali irin halayyen da mutum ya gada daga iyaye ko aka haifesa dasu, to kowa yasan halayen Aunty Zuwaira ba gado ba ne don kowa ya shaidi martabatar iyayenta da sauran zuriyyarsu, ba kuma wadanda aka haifeta dasu bane.
Na biyu shine halayyen mutum da ake iya gyarawa Amma sai an Sha wahala sosai wajen yin gyaran, irin wadannan halayyen mutum kan tsiri yinsu ne a kan da dole ma'ana wani dalili ya tilasta wajen adopting canza original halinda aka san mutum dashi. Misali irin yanzun da yawancin maza kan bar wa mace takakihun hidimar gida, yau da gobe darajar sa na iya zubewa a idonta, ta daina ganin girmansa sabanin yadda take mutuntashi da can.
Na uku mutum Kan dauki halayyan da ba nasa ba da rana tsaka ko dalilin hulda da abokan banza, ko haka kawai ya halin wani ya rinka burgesa, irin wadannan gyara kawai suke bukata ba kuma za a wahala wajen gyarawan ba.
Ya kada kai yace "To munji mai falsafa cikin wadannan kashin da kika zano da wanne kika danganta Zuwaira dashi har kike shaawar zamanku tare? Kenan kina ganin zaki iya gyara halayyenta?
Rahima ta nisa "Sanin gaibu sai Lillahi, Ina adduar sanadiyyar zaman tare ta canza halayen nata."
Hjy Kaltume tace "Da kyau Rahima haka ake son musulmin kwarai ya sowa kansa abinda yake so wa kansa, kin burgeni."
Umma tace "Hakane Hajiya nima banki naki ba, tashin hankaline nike gudu."
Rahima tayi murmushi "Kamar kin manta da halin diyar taki Umma, fitina ta kan kare ne Kan Wanda ya jawota, Ni dai goyon bayanku nike bukata sannan ku tayamu addua."
Hjy Kaltume tace "Shikenan Allah yai miki albarka ya cika burunki na alkhairi.
Daktan ya wani kalleta yace "Naji duk kun goyi bayanta ne, to ni kam ina nan kan bakana, idan Kuma kun matsa na amince to Kar ayi kuka dani idan wani abu ya taso nan gaba "
Mahaifiyarsa tace "Wannan ne baka isa ba, ka tara 'ya'yan mutane kace ba ruwanka.".
Rahima tace "Rabu dashi Hajiya naji sharadinsa na dauka Allah ya kama mana."
Ya sake kallonta a fusace yace "Yanzun sai ki fadi inda kuke son ku zauna tsakanin Dorayi da Galadancin."
Ta girgiza Kai "Ba ni da wannan matsayin, Kai da Aunty Zuwaira kuyi deciding Ni 'yar amshin shata ce.".
Ya juya gasu Hajiya "Kunji amsar ta ko?"
Hajiya ta gyada Kai "Laifi kake son Dora mata dai amma gaskiya ta fada, tabbas zabi na gareku, ta ba Zuwaira girmanta da Kai kanka."
Da yaga ba zai samu goyon bayan da ya zata ba dai ya amince cike da fargaba.
Yayi deciding kara gyara gidan da Rahima take saboda akwai filin da za a dora wani ginin sosai.
Ba bata lokaci aka fara aikin sake tsara gidan Daktan don zaman iyalinsa.
19/09/2020, 13:57 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA..doc by jami
46
An kammala komi na gidan Dakta har gashi Uwargida Zuwaira da tawagarta sun rakata tarewa a nata bangaren.
Yanuwanta da suka san mutunci sun shiga sun gaisa da Rahima aka taba barkwanci suka musu addua suka tafi, kawayenta kuwa sai shirmen da suka saba, hatta da falon Zuwaira Saida suka leko yanayin tsarin da Rahima ta yiwa nata suka dawo suka kwatanta irinsa, suna yo suna yar da maganganu don dai neman jidali.
Bata kula ba balle tasan Allah yai ruwan tsironsu, to Rahima a banza take miskila?
A wannan ranar Zuwairar ke da maigidan yadda ta shirya saboda Wai ta nunawa Rahimar ita ke da gida da maigidan ma gaba daya, to wace take yi dominta bata san arziki na bori ba.
To idan ba shiririta da neman zubar da aji irin na Zuwaira ba, kowaccensu sashen daban, sai ma kaso sanin halinda yaruwa ke ciki ne zaka leka inda take, sai kuwa idan sun hadu a general parlour na gidan, kowacce tana da masu aikinta to me ye na hana Kai sukuni?
Dawowar su Zuwaira yasa yaranta suka Kara shakuwa sa Rahima saboda tana jansu sosai a jikinta, ta hanyar kulawa da duk bukatocinsu ba gajiyawa, ga kokarin tarbiyyarsu da take yi tareda danta, to jama'a ko yaro yasan mai son shi.
Zuwaira bata kaunar kusancin yaranta da Rahima ko miskala zarratin, da taga tayi kokarin rabasu ya faskara sai ta shaidawa abokiyar shawarar nata. Husaina ta buga kirji tace "Zauna ki saki baki galala kamar wata sauna bayan ta mallake miki mijin ta hada da 'ya'yanki kina zaune sokoko ta mallake zuciyar yaranki tas, an fada miki da bakin hura wuta wannan yarinyar ke zaune a gidan Nan?"
"Da alamun kamshin gaskiya a batunki Husaina, nima zargina kenan don wallahi ko kaffara ba zanyi ba, ba haka kawai Dakta ke rawar jiki da ita ba, ke baki ga yadda take juyashi ba fa, Daktan da bana ganin tsadadden murmushinsa sai na sha ruwan dala amma ko waya yake da ita haka zaki ga yana wani rausayar da Kai Yana zuba murmushi sai kace wani sick lover boy."
Husaina ta kyalkyace da dariya tace "To ai ba murmushinsa kadai ba shi kanshi tsadadden ne Zuwaira, yanzun dai meye shawara?"
"Kinji kuma, ke din dai nike saurare."
Husaina tace "Ya zanyi dake yanzun,kince ke ba zaki shiga malamai ba, to ki zauna ta saki a tafin hannunta ta murza ta juya son ranta, mu dai idan da malamai da bokaye a duniya mun gi karfin tsara balle irin wancan da aka dauko miki, ke Kika yi sake tun farko amma ai ba ajinki ba ce."
Zuwaira taja dogon numfashi "Ai yanzun dole mu san matakin dauka that's why na neme ki."
"Karki samu damuwa 'yaruwa, kin yarda ko wane irin taimako na kawo miki zaki yi amfani dashi ko?"
"Me zai hana kuwa Husaina shakkun me kike?"
Husaina tace "Ai dole in jinjina kar kisa in kashe kudina a banza alhalin kin san samun su da wuya."
Zuwaira tasha mur tace "Ke fa problem dinki kenan in dai batun kudi ya taso alhalin ni Ina kashe miki kowacce irin lalura ba tareda jin kyashin komi ba, ke kuwa in dai za ki yi min Abu sai kiji tamkar naman jikinki zaki diba."
Nan take Husaina 'yar bariki ta share wannan batun cikin dabara tunda tasan gaskiya aminiyarta ta fadi tace "Wasa fa nike miki, amma da gaske kinsaj business din mu yaja baya Kuma mijina ba irin naki bane da yake sakar miki dala kina fantamawa yadda ranki ke so, nasa Dan banzan makon tsiya, hannun nan nasa a dunkule tamkar na "yan dambe."
Zuwaira ta tuntsire da dariya "Oh sharri ma za kiyi masa Kuma? Ai kuwa Yana kokarinsa shima."..
Ta tabe baki. "Me Kika sani game da mugun halinsa, ke ni fa auren ma na gaji har na nemi ya sauwaka min, in gutsire igiyar auren in yi gaba in sami Wanda ya dace dani."
Ta zaro idanu "Ke Husaina ki rufaea kanki asiri, Ina ke Ina wani rabuwa da mijinki yanzun, wa zai wani aureki yanzun bayan ga 'yan matan Nan ma suna yawo a titi a mashinshini?"
Ta gyada Kai "Ai da kika ganni da agenda ta, na riga na shirya komi jiran lokaci nike in gabatar miki.."
"Toh! Al"amarin ba sauki kenan to Allah ya nuna mana alkhairi."
Tace Amin "Bari inyi azama Kar Malam ya fita sai kin ganni."
Tsakanin matan Daktan biyu zama yaki dadi,ta kowanne bangare Zuwaira bata da dama. Matsalar farko da Rahims ta fara karo da ita daga uwargidan nata itace gasa, Zuwaira irin matan nan masu shegen gasa, duk abinda taga Rahimar tayi sai ta kwaikwaya, ko silifas ta lura Rahima ta canza itama saita saya, balle a kaiga su kayan jiki ko na gyaran gida.
Wasan wasa rashin mafadi, gasa idan ba na nuna bajinta wajen bautar Allah bane ya zama shirme.
A ka dawo Kan abinci, a kullum mai aikin Zuwaira na yaeon gulma sa sunan tana zuwa wajen Uwale ne amma su sun San yar leken asirin uwardakinta ne, duk abinda yazo taga ana girkawa a sashen Rahima zata nade taje ta fesawa uwardakinta musamman idan Daktan wajensu yake, ita Kuma ranar nata girkin saita wanke tukunya ta kwaiwayi irin Wanda su Rahimar suka yi ta sake dafawa. Sai ayi rashi dace, Wanda akayi dominshi ba zai ci ba, Zuwaira ta fara bala'in hatta abincin ta ya daina ci sai na Rahima.