← Book details Rahima Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 2 OF 48

Sashe 2

Rahima Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

Haseeb yai gyaran murya "Ni ban kiraku gardama ba, shawara na taraku muyi, Kai Hayatu hakuri za muyi ayi abinda ya dace, Hjy ma na goyin bayansa. Amma Kai Rabi'u Ina son kasan cewan wallahi ba da son raina za ayi auren nan ba, na amince ne gudun bacin ran mahaifiyarmu Kuma bamu san alkhairin dake ciki ba so karka damu ba zaka ji kunya ba in Allah yaso. Yanzun su waye ne iyayenta, wace unguwa take?"
Baki yaki rufuwa saboda murna, Hayatu ya kallesa ya bushe da dariya yace "Ka daina wani murna in har munji bata da usuli batun aure ya tashi ehe, uhhmmm Kai muke saurare:
03/09/2020, 10:52 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by Jami
2
Dr Haseeb yai murmushi bayan jin kalaman tsohuwarsa yace "Tuni na amince da batunki Hajiya shiyasa na sayo miki wadannan kayan masarufin yadda kika bukata bisa yarjejeniyar aunarwa za ki rinka yi ba ki zauna kina irin wahalar nan ba."
Itama tayi 'yar dariya " Ina wahala a nan? Ku fa likitoci kuka ce mutum ya rinka motsa jininsa, Kuma idan kace sai tiya ko mudu zan rinka sayarwa kenan sana'ar tawa bata talaka ba ce, in kuwa hakane to ci gabanmu ragagge ne domin talaka shine jigon kowacce irin sana'a, ni don Allah ka bar wannan zancen, Kai kenan kullum kazo gidannan da sabon tsirkun da zaka kirkiro alhali ni din nan ban gaza ba da sauran karfina, to Wai ma Ina wahalar take? Mai aiki fa ka ajiye min musamman babu abinda ni keyi kullum sai dai in wanke goma in tsoma biyar, inci mai kyau, insha mai kyau, in daura zanin da wata yarinyar macen bata daura na, inyi barci na ya isheni, in bautawa Ubangijina gwargwadon karfina, bani da sauran buri a duniya da ya wuce illa inga auren Dan autana, baya ga shi sai rokon cikawa da imani. Haba wace wahala, lokacin da akayi ta can da anyi yanzun kuwa albrkacinku sai godiyar Allah da fatar Allah ya baku masu yi muku fiye da yadda kuke yi mana."
Ya amsa "Ameen Hajiya, shikenan ba zan kara magana kan hidimar sana'arki ba Allah ya bada sa'a, amma don Allah ki rinka samun isashshen hutu, bayan haka nace ki tambayeni duk abinda kike so cikin ikon Allah ba zai gagara ba."

Hjy. Kaltume ta tattara kayan gabanta ta ture gefe tace "Bari dai in tsaya muyi maganar nan sosai don na fahimci hira kake ji yau, shin me yasa kake son maida hannun agogo baya ne? Na fada maka Kai kadai, na gaya maka tare da 'yanuwanka, yau ma zan Kara fada maka ni ban raina hidimar da kake min ba, iyaka nafi amincewa da in nemi nawa na kaina, ba sai na jiraka ba balle 'yanuwanka da basu da hali. Ranar da Allah ya hore maka kayi inyi murna da farin ciki, ranar da baka dashi sai inyi amfani da nawan da kuke rainawa, kaga na rufawa kaina asiri na rufa muku, banda wannan yau da gobe bata bar komi ba, koda nike mahaifiyarku ba lale Allah ya tara min duk masu jin kaina ba, idan Kuma har na samu hakan nasan irin matan da zaku auro? Wata matar ita ke hana da ya kula da iyayensa yadda ya kamata duk da ni alhamdulillah matanku na kwatanta min da'a. To idan duk muka ture wannan batun, ka duba kaga kaine babba, Allah bai ba 'yanuwanka rufin asiri irin naka ba, kai kake dawainiya dani, kayi dasu da dangina, ka taimaki dangin mahaifinka, Ina tausaya maka kwarai da gaske don ka zama hannu guda ba wani mai tallafa maka, ga iyali ka fara tarawa dole in rinka taimakonka, misali ko haihuwa matarka tayi na baka gudumuwar zanin goyo ban taimaka maka ba?"
Dole yayi murmushin da har kyawawan hakoransa suka bayyana yace "Wallahi Hjy kin ban dariya, amma insha Allah ba zan sake shishishigi cikin hidimominki ba, Allah Kuma ya kara taimakawa."

"Yauwa yanzun naji batu, to tunda naga ka saki ranka yanzun sai muyi maganar dalilin nemanka."
Ya amsa "Ina saurarenki, Allah yasa lafiya."
" Lafiya kalau, batun kaninka Rabi'u ne, kasan na fara yi maka bayanin neman auren da ta fara kwanaki ko? To shine jiya ya taho min da maganar cewan wai iyayen yarinyar sunce inda gaske yake ya fito."

Haseeb yai kasake na wani lokaci kafin ya furta "Har yanzun yana nan yana shirmen nasa kenan?"
Tace "Wane irin shirme Kuma, yaro na neman raya sunnar manzo?"
"Hmmmm hjy Rabi'un guda nawa yake ne? Ni fa karatu na turasa makaranta yayi ba soyayya ba, don Allah Ina zai kai mata yanzun?"

"Ban gane ina zai kai mata ba, bai isa auren bane ko yaya?" Ko kuwa don ka turashi karatu sai yaki aure, maza da mata nawa ke yin auren su ci gaba da karatun nasu?"
Ya kada Kai "Kwarai ana yi amma ga Wanda ya shirya, yana da muhallin da zai aje matar yanada kamu sayar domin ciyar da ita da daukar sauran lalurorin yau da kullum na shi kansa da ita matar da ya aje. Rabi'u karatu yake Hajiya, duka -duka 200 level yake a jami'a, me zai hana ya hakura ya kare sauran shekara dayan, ya samu abinyi kafin muyi wani batun aure?"

Ta fara harzuka "Da yawan yajin aikin da ake yi a jami'oi ne zai gama karatun nan da shekara gudan? To naji, yanzun ya kake son ayi da iyayen yarinyar, me zamu ce dasu?"

Ya amsa "Ace musu bai shirya ba sai ya gama karatunsa tukunna."
Tace "To ita Kuma yarinyar da aka ce za a aurar da ita yanzun ne fa?"
Ya bata amsa da "Ta nemi wani ta aura tunda iyayenta sun matsu su aurar da ita, shi Kuma Allah ya bashi wata nan gaba idan lokacin auren nasa yayi."

Ta fusata "Na fahimci ka shiryawa kowacce tambaya zanyi maka, kawai ka fito fili kace ba zaka taimakawa danuwanka hidimar aurensa ba fakat."

Ya Kara ladabtar da kansa "Ko kusa ba haka bane Ni a ko yaushe shirye nike in yiwa 'yanuwana kowanne irin taimako suka bukata daga gareni. Ba wai baba son Rabi'u yai aure bane, tunanina mene na gaugawa,hanzari ba nasa bane, ya bi a hankali mana har Allah ya bashi daidai shi."

Hjy Kaltu ta juya masa baya "Kai kake da lokacin surutu, da kake gaya min wannan zancen wofin kaninka da kuke uba daya nawa suka yi aure? Gaba dayansu babu Wanda ya haura shekaru ashirin a cikinsu, me yasa baka hanasu ba, wane irin gudumuwa ce baka basu ba, sai yanzun yaro ya Kai shekaru da biyar a duniya ya isa aure kace zaka tauye masa hakkinsa?"

Yace Yi hakuri ban tari numfashinki ba, wadanda kike magana na amince musu ne saboda kowannansu nada shago a kasuwa, sunada abinyi,tunda sun nuna su kasuwancin suke so fiye da karatun, na tabbatar Kuma zasu iya daukar takalihun matansu, amma Kya hada da wannan ahi ba karatun ba, shi ba aiki ko wata katamammiyar sana'a ba? Idan Kuma kina ganin banyi magana Kan auren su Hamisu ba na Hayatu shima na hana shi ai amma shima don rashin sanin ciwon Kai matar shekararta biyu ya sake auro wata, gasu nan banda tashin hankali me suke yi?"

Ta juyo a fusace "Ka rufa min bakinka kaji, ai fa tunda ba Kai ya shafa ba yanzun zaka rinka kawo min kabli da ba'di, to shima da ya auri mata biyun ai ance matar mutum kabarinsa da yaje yana neman na banza a waje ai gara ya tara cikin gidansa. Kai wai ya za ayi daman ra'ayin rikau dinka ya zama irin na kowa? Naji ta bakinka, tashi jeka, kaga kyaun sana'ar da kake mita, ni zan tsaya, Allah kuma zai taimakemu ayi wannan auren da yardar Allah autana ba zai kunyata ba, idan ba zaka jagoranci harkar auren ba ai ba Kai kadai bane, kaninka na Nan, Allah dai na gani na baka hakkinka na kasancewa babba."

Da ya tabbatar da al'amarin yai nisa gashi bai son bacin ranta ko kadan har dai in ya tuna can inda aka fito da can dole ya fara lallashi yana bata hakuri yace "Tunda abin ya zama haka ba komi Hajiya, daman ni naso ace ya kara sanin ciwon kansa ne yasan wahalar ya nemi na sa yadda idan yai auren zai fi rike matar da daraja da mutunci amma tunda an matsa insha Allahu ba damuwa za ayi yadda kika ce cikin yardar Allah. Zan nemi Hayatu mu tafi gidan iyayen yarinyar cikin satin nan in yaso duk yadda muka yi dasu Kya ji, anjima ki turo min Rabi'un yai min bayanin unguwar, Allah yasa mana hannu."

Dadi ya rufeta cikin murna tace "Insha Allah yau dinnan zaka ganshi yana dawowa gida zan turo maka shi, Allah yai maka albarka."
Chapter 2 · 0% Book details