Sashe 43
Rahima Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Dakta yai shiru yana kallon matarsa yana yaba halinta cikin zuciyarsa.
Hakika yaga canji wajen Zuwaira, tun yana mamaki har ya daina yaci gaba da sa ido yana lura da dabbin dabi'un data bullo dasu, misali gabatar da sallar asubah ba tareda makara ba shine babban canjin da yai masa dadi a ransa,ta rage yawo kusan rabon da tace zata bukin kawa ko aminiya ya manta, business din ma yayi sanyi ba kamar da ba, yaranta suna samun kulawarta sakamakon ganin irin kaunar da Rahima ke yi musu da yi musu tarbiyyar kwarai, shi kansa yasa mata dokar hana kaisu ko'ina da sunan a barsu can, sai dai a kaisu su gaida kakanninsu da yanuwa direba ya dawo dasu. A gaskiya problems din da yake fuskanta da ita sunyi sauki sosai thanks to beloved Rahima, matsalar data rage yanzun shine yadda Zuwaira ta shafawa idonta toka taki amincewa zuciyarta matsayin Rahima na da can da wanda Allah ya kawota a yanzun, sai dai inda yake jin sanyi Rahima ta daure kowanne cin Kashi da Zuwaira ke mata, inda take Burgesa ma duk iya masifar Uwargidanta ba dai kaji bakinta ba, sai dai na Zuwaira wace takan Kara masa gishiri tace anyi alhalin ba ayin ba.
Ta dan bugi hannun kujerar da yake Kai tace "Lafiya kayi shiru haka cikin zurfin tunani?"
Ya juyo ya dau glass dinsa ya manna a fuskarsa ya sakar mata lallsusar murmushinsa yace "Just thinking of how lucky iam to have you in my life."
Tayi dariyarta mai fitar da kyawawan jerin hakoran ta cikin shagwaba ta "Ya Haseeb kenan, godiya nike sosai."
A can cikin dakinta Zuwairan Dakta ta zauna tana cizon yatsarta cikin damuwa domin kissar data shiryawa Rahima kamar kullum bai yi wani tasiri ba. Gaskiya yarinyar akwai dan Karen wayo, duk wani plan data shirya don taga downfall dinta sai dai ya wargaje ko ta wargajesa cikin ruwan sanyi. Gaskiya da sake lale, ba zata zauna ace Rahima ta kwace mata miji ba. To me rage, me yai saura? Matar da babu irin kissa da kisisinar da bata kware a Kai ba, matar data iya hilace miji ta hanyoyi daban-daban?
Sai dai ita kanta ta amince Rahima mace ce Mai matukar ladabi da biyayya halayen da kowanne namiji ke so wurin matarsa, to ko wadannan halaye basu isa su mallaka mata mijinta ba? Ga yadda taji labarinta tun aurenta na farko Rahima bata yiwa mijinta musu, duk abinda yace fari ne zata tas kuwa koda kuwa baki ne za tace yafi nono fari. Bayan haka ko taso ko taki Rahima macece mai hakuri mai son zaman lafiya da kowa bata son tashin hankali sam amma bata daukar raini, to ita yanzun ya zata yi? Tas ta gama amfani da magunguna da Husaina ta kawo mata bata ga wani canji ba, Husaina bata da mutunci ga wata gurguwar shawara da take bata wai ta rabu da Haseeb, hhmmm da ne zuciyarta ta rinka gigin yayo mata wannan mummunar tunanin, but ta rabu dashi ta auri wa? Ina zata sami kamarsa? Ita kuma don sakarci ta rinka daukar shawara...
Zuwaira ta muskuta a gado taci gaba da tunani, to yanzun data gane kuskuren biyewa Husaina wane mataki ya dace ta dauka don mallake zuciyar mijinta irin Rahimar?
Gidan malamai? Ta girgiza kai, no ba ya cikin dabi'a ko tsarinta, tayi saurin kawar da wannan, bata yarda da yawon gidajen bokaye Rahima ta shigewa Haseeb zuciya tayi daram ba, to meye sirrin? Inganta tsabtar jiki da tufafi da muhalli ko kuwa iya sarrafa dadad'an nau'ikan abinci? Kai ah ah wadannan kadai basu isa su mallaka mata zuciyar gwarzon namiji irin mijinta ba. To ko kuwa kamun kai da rike mutuncinta ne silar suka zama silar zama 'yar gaban goshin sa?
Shin Ina zata gano sirrin don itama ta kwatanta taga ko zata ci riba tayi nasara mijinta ya rinka kaffa-kaffa da rawar jiki da matar da a da yake nuna ita din dole ce tasa ya aureta?
Kafin ta samo amsarta ya dace tasan ita macece , tasan martaba, kima da darajar da Allah yai Mata, to idan ta zubar da mutuncin nata tuntuni fa, yanzun ne take son tattaroshi ta kwaso ta zama equal da Rahima fa duk da hausawa sunce mutunci madsra ba a barinsa a kwashe duka?
Nan take hawayen nadama suka fara gangaro mata, tabbas mijinta yai hakurin zama da ita, da wani ne da tuni ya koreta amma ya daure ya riketa duk da yasan illolin dake tattare da masu irin halinta, oh ni Zuwaira Allah ka shiryar dani hanya madaidaiciya ka hana min ci gaba da aikata sabonka,ka yafe min dimbin zunuban dana jibgawa kaina.
Babu wani abinyi yi a gareta illa ta roki mijinta gafara kana taci gaba da istigfari, tsayuwar dare da azumin nafila ko Ubangiji zai ji kanta ya yaye mata matsolinta, ciki harda rokon Allah ya mallaka mata zuciyar mijinta, to bangaren Rahima fa? Ya zan dole ta ajiye duk wani kishi da kyashi da hassadarta su zauna lafiya ko ta Kara samun haske daga gareta wadanda zasu gyara mata al'amurranta.
An dade da fara Kiran sallar magrib kafin ta dawo hayyacinta tayi hanzarin dauro alwala ta gabatar da sallar kana taci gaba da istigfari har aka Kira isha'i, ta mike ta gabatar ta sallame ta yi adduoinnta ta shafa.
Kafin maigidan ya dawo daga masallaci ta shiga wanka ta fito ta canza ado ta fito da kayan abinci, tana harhadawa ya shigo falon tareda su Khalifa harda Abdul, suka zauna suka ci abinci suka kare, bayan sun wanke baki da hannu ta kallesu tace "Kun ga ku tafi sashen Aunty Rahima ku ce Ina gaisheta "
Yara suka dubeta galala Kuma basu tashi ba to basu taba ji tace hakan ba,Saida ta maimaita suka mike cikin farin ciki, Khalifa ya kama hannun Abdul yace "Mama mu kwana a can?"
Ta gyada Kai"Manufata kenan, oya, ku wuce ku bamu wuri "
A guje suka fita sunata murna, shi kuwa yana zaune tamkar baiji diramar da suke yi ba duk da kasancewar yaji dadin furucinta ba zai nuna ba domin gudun ko halin neman maganar ce nata ya taso ko da wata manufar ta aikata hakan.
Ta bude baki zata yi masa magana kenan sallamar Husaina y katseta, kafin ayi mata iznin shiga ta shige, masifar kamshin turarenta mai shegen hawa kai ya da doki hancin Daktan, yai saurin mikewa, ita Kuma ta rusuna cike da ladabi na kissa ta gaishe tana wani kashe murya sai kace karuwa, ya amsa a dakale ya nufi sashen sa.
20/09/2020, 12:08 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA...doc by jami
49
Husaina ta kalli tace "Ni dai da sa'a nike, duk lokacin dana taho sai in tadda Oga na gida."
Takaicin furucinta yasa Zuwaira shan mur, a zahiri kuma ta gaji da irin dirar mikiyar da aminiyar nata ke mata, bata taba zuwa gidanta sai ranar girkinta ta kuma tabbatar da zata sami Daktan a gida me take nufi? Kalli irin shigar data yi ma, har tana wani rausaya murya kasa -kasa don zata gaisheshi....
Husaina ta mike kafafunta ta kalli 'yantsun hannunta da faruttan da suka ci adon jan farce ta yaba da kanta tukunna sannan ta tabo Zuwaira "Meye matsalar naga kinyi shiru fuska a daure"
Zuwaira ta kalleta a shagube "Wace irin matsala bayan kin shigo kin ganni muna zaune lakadan muna hira da mijina!
Ta kura mata ido na dakika guda "Zuwaira kenan ni banga hakan ba yanayin murtuke fuskar da yayi, da kyar fa ya amsa gaisuwata, shine kike ban mamakin rabuwa dashi ki huta tunda ba kanin tsohonki ba ne."
Kalamanta sun yiwa Zuwaira daci amma ta daure tace "Ba zan rabu da mijina ba Husaina tunda Ina son abina."
Tayi wata 'yar shewa irin tasu ta 'yan duniya tace "Aiki ya ci sai ki kawo kudin biyan Malam."
Zuwaira ta tabe baki "Ina ce sai an ga fa'idar abu ake biya?"
"To a cewarki komi normal sai ki biyani."
Zuwaira ta gyara zama ta kalleta daidai ta mika hannu ta dauki cup din da Daktan yasha lemo bai shanye ba shigowarta yasa ya aje cup din ya fita, ta Kai bakinta kenan Zuwaira ta kabe cup ya fadi ya fashe.
A fusace ta zabura "Kan uba! Wane irin iskancine kike ji ne yau?"
Zuwaira ma ta zaburo ta mike a fusace "Ha ki nan babbar 'yar iska da kike neman raina min hankali, ki rasa cup din da zaki sha lemo sai wanda mijina yasha a ciki?"
"Ke din ce babbar 'yar iska har yaushe kika san darajar mijin da kike kuri dashi, yanzun me Kika san mutuncinsa?"
Maimakon amsa mari Zuwaira ta shararawa Husaina..tace ki sake kirana 'yar iska kika yadda zanyi dake...
Husaina ta rike kuncinta ta saki ta dunkula hannu ta sakarwa Zuwaira a ciki, ba sai dambe ya kacame ba, nan Mai aikinta ta saka ihu ta ruga sashen Rahima ta fado mata tana kuka.
Rahima da Uwale suka rugo a guje, inda ta shiga tsakiyar aminan sa idanunsu ya rufe saboda masifa ba su ga zuwanta ba, wani cup din Husaina ta raruma ta wurgi Zuwaira dashi ta kauce bai sameta ba sai Rahima ya yanketa daidai saman girar ta.
Jinin da suka ga yana zuba yasa suka daina masifar, Husaina ta suri Jakarta ta barta gidan a guje, Zuwaira da Uwale suka yo Kan Rahima suna mata sannu, nan take dai aka dauko first Aid kit aka wanke ciwon aka tsaida jinin kana aka rufe da plaster.
Jikin Zuwaira yai sanyi sosai ta shiga cikin damuwar abinda zai faru da zaran maigidan ya dawo.
Rahima ta lura tace "Don Allah ki kwantar da hankalinki tsautsayi ne Wanda ba a sa masa rana."
Ta kalleta cikin jin nauyi sabida irin surutan da Husaina ta rinka barbadawa da gayya kuma tasan Rahimar da yaran gidan ma sunji (masu musu aiki) tace "Don Allah Rahima kiyi hakuri ki yafe min."
Rahima ta kalleta cike da tausayi "Wallahi ban rikeki da komi ba Aunty Allah ya yafe Mana m baki daya ya tsare gaba."
Suka dan zauna na 'yan mintoci kafin ta mike tace "Zamu koma can sabida ba kowa sai yara, mu kwana lafiya."
Zuwaira ta amsa "Nagode a sanyaye."