← Book details Rahima Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 10 OF 48

Sashe 10

Rahima Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Bata tafin ba sai wajen sati na uku bayan tayi sarai ta koma tamkar bata taba wani shayarwa ba. Tana isa gidansu Hayatu ta kara tabbatar da ba abinda yafi zama lfy da kwanciyar hankali, yanayin gidan ya canza, maigidan ya Kara gyara ko'ina tsaf, mata da yara sunyi shar, shima yayi fes har kiba yayi ya fara teba. Ta kasa boye sha' awarsu cikin hira tace musu "Nifa kun burgeni, Ina mamakin canzawarku, wani shahararren malami yai muku waazi ya shige ko Yaya?
Suka kalli juna suna murmushin fahimta kafin Jamila ta fara magana "Alamarun Allah ne, kinsan idan yaso mutum da shiriya, ba abinda myuke yanzun sai godiyar Allah da ya ganar damu."
Haulatu ta karba "Wallahi mun fahimci ba abinda ke jawo tsiya irin tashin hankali da masifa."
Hayatu yace "Nima kullum cikin godiyar Allah nike, da har fargabar shigowa gidana nike, dana doso kofar gidan sai gabana ya Fadi don ban San bala'in da zan shigo in taras ba, Ina kuwa shigowa abinda nike gudun zan taras, kiji harshensu na tashi kamar zasu dafa naman junansu, inyi -inyi su bari ko kallo ban ishesu ba sabida sun riga sun hau dokin shaidan Yana sukuwa dasu.
"To kuma meye na tashin tashina, kuskure ne munyumi, mun gane mun tuba mun dawi hanya. Jamila ta koro jawabin...
Haulatu tace "Rabu dashi dai Hajiya to waye bai kuskure?.
Rahima tayi dariya "Kwarai dukkan Dan Adam ajizi ne dole a samemu da aikata kura-kurai yau da kullum shiyasa ake son mutum ya rinka rokon Allah ya shiryar damu hanya madaidaiciya ya Kuma ganar damu ya bamu ikon bin tafarkin gaskiya, kana ya yafe Mana zunubanmu na biye da sarari, wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba.Amma Ina ganin fa tun farko laifinka ne Ya Hayatu."..
Ya kalleta cikin mamaki "Kamar yaya? Alhalin kullum Ina kokarin yin adalci tsakaninsu, fitina ce kawai amma da suka ga ba riba sun sauke.".
"Au Kuma haka zaka ce?" Suka tara Fadi
Rahima tace "Ni dai na fahimci bala'in son Yaya kuke shi ya jawo muku bakin kishin Nan."

Ya sosa keys "Haka ake so? Ina ce in har son ne competition din kyautata min ya dace suyi ba rigima da juna dani kullum kaina dana aje su ba, tsaya kiji wani sirrin kanwata wallahi da sunci gaba da shirmensu ko da yanzun na Kara aure din har na kusa gama shirya komi, Kuma banyi niyyar hadasu gida guda ba, in. Koma can in tare hankalina kwance su kuwa suci tsiyarsu nan inga karyar kishi."

"Allah ya tona maka asiri, ashe amanar mu kaso ci muna zaune tun baka da komi daka samu shine zaka dauko wata taci arzikin? Da wallahi kun gane kurenku data gwammace bata aureka ba."
Rahima ta dafe kai tana dariya tace "Wai ni kaina Ya Hayatu ka yarda da batuna, Kuma na baka goyon baya muddin suka ci gaba da halinsu ka aikata abinda kace daga nan a ga wacce tafi sonka.".

Suka taso kamar zasu cinyeta danya dyk da sun san wasa take, Saida ta basu hakuri tace ai ba sauran batun wata amarya tunda kun hada Kai Kunji ance zama lafiya yafi zama dan sarki, muddin za ayi hakurin zama da juna sai kuga Allah na taimakanku, wadata ya sameku, maigida yaji dadin kyautata muku, yaranku su tashi cikin ingantacciyar tarbiyya da kyakkyawar hadin Kai da zumunci da son junansu ga kwanciyar hankali da samun natsuwa."..
Suka ce wallahi mun gane kanwarmu Allah ya ganar da sauran mata Ina alfanun mugun zama, mun gode da shawarwarinki, Allah ya kawo mana suruki nagari."

Nan da nan ta bata fuska "Anya zaku same shi da wuri?"
Hayatu yace "To aure dai sunnar manzo ne nasan kinsan hakan, mu ba zamu so ki zauna ba aure bayan rasuwar Rabiu ba sai a rinka zargin wani abu."

Ta nisa "Ai ba cewa nayi ba zanyi ba, Kai kasan zaman da mukayi da kaninka, Ina zan samu Mai kwatankwacin halayensa?"

Jamila tace "Su din dangin gujiya ce, sai an fasa ake sanin na kwarai, ki fasa ki gani Mana."

"Na tabbata zata sami Mai gari kuwa, mu dai mun kosa mu sha buki."

Tace "Tsokanata ma kuke, bari in shige gidanmu.
Ta koma gida tana tunanin hirarsu dasu Hayatu. Aure? Ita har tsoro kalmar ke bata ba don komi ba sai domin rashin cikakken kwanciyar hankalin zabin wanda zai zama abokin rayuwarta da tunanin yadda zata Kara sake koyo kaunar wani da namiji tunda har lokacin bata sami Wanda ma ya kwanta mata a rai ba ko jininsu ya hadu balle a kai ga batun aure..

Maganar abokin marigayin ma bata taso ba don a ganinta da zata aureshin ma taci amanar marigayin kenan duk da ba addini ne ya hana ba, a daya bangaren surutun jama'a fa kasancewarsa saurayi Wanda bai taba aure ba, ita kuwa harta haihu, shin zata iya daure gutsuri tsoman daka iya yiwa auren dabaibayi? Ina batun danginsa, shin zasu karbeta ba tareda wata tsangwama ba,? Ajiye batunsa a gefe shine alkhairi,to Alh. Suraj fa dake da magoya baya irinsu Maryam harda Umma da ta fara shiga ciki, idan bata yi taka tsantsan ba sarkin yawa yafi sarkin karfi lalle suna iya taruwa sufi karfinta, ta tsaya tayi nazarin Alh Surajo lalle yes mutum kamili sai dai ba nan gizo ke sakar ba ta kwatanta kaunarsa a zuciyarta abu ya faskara in ba hakuri zata yi ta auresa hakan Nan ba ta koyi so da kaunarsa yadda tayi na Rabiu amma idan tayi hakan shikenan bata da ranar jin dandanon zakin zumar soyayyar da Maryam ta kwadaita mata kenan? Oh oh Allah gani gareka, kayi min zabin abinda yafi zama alkhairi a rayuwata.

Wasa-wasa watanni sun Mika sunyi nisa har ana neman hada shekara da rasuwar mijinta, amma ba amo ba labari ba alamar zata fidda miji cikin masoyanta da suka kasa rabuwa da ita suyi fushi.
. Abdul karami har ya shiga nursery, mamansa kuwa ta Kara sadaukar da kanta ne a aikinta, lokacinta na yaran da take koyarwa ne Wanda Allah ya dorawa lalurori iri daban-daban, kullum tausayinsu karuwa yake, kusancinta dasu ya fiye mata komi don haka ta manta shaf da wani batun aure, tunanin zama da wani ya shafe ya goge a ranta.
04/09/2020, 23:29 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by Jami

13

Akai-akai take zuwa gaida tsohuwar sarakuwarta, duk sati ta Kai Abdul yai mata hutun karshen mako, su da kansu dangin uban suka raba yadda yaron zai rinka ziyaryar ko'ina don ya saba da sauran 'yanuwansa.
Ko yaushe Rahima ta ziyarci Hajiya saita yi mata fadan kin yin aure, a gida ma tun iyayen nayi sun gaji sun saka mata ido, yaruwarta Maryam ma na irin nata kokarin don ta ciwo kanta su zama matan abokai duk tayi kunnin uwar shegu.

Wannan satin Abdul gidan takwaransa yai weekend, ya daukosa ya maido gidan Hjy don mamansa nan zata taho daukarsa kasancewar Zuwaira bata gari. Tunda suka shiga gidan Abdul ke manne da Haseeb yaki yarda ya sauka daga cinyarsa balle yaje wajen kakar Saida tayi masa dabara aka samu da kyar mairo mai aikinta ta goyasa suka nufi wake sannan ya gaisa da mahaifiyarta..
Hajiya tace "Yaron Nan ya shaku da Kai Kwarai da gaske."..
Ya amsa "Haka kowa ke Fadi, gashi yana jin maganata ko rigimar banzan sa ya fara yaki sauraren kowa Ina masa magana zai daina."

Tayi shuru cikin tunani kafin ta furta "Daman Rabi'u yace danka ne dole yaji maganarka."

Yace "Dalili kenan da in har ya gama nursery mamansa bata yi aure ba zan karbi dans kawai tunda daman an bar mata shi bisa yarjejeniyar zamu amshi abinmu ne idan zata sake aure to tunda ba alamun hakan gara mu karbeshi kawai."

Ta zaro ido " Zaka tayar mata da hankali, da wanne zata ji, yaron nan shi take gani tana jin sanyi, idan an nuna mata fun karfi a kansa zaku dau hakkin yarinyar Nan."

Ya bata fuska "Ai munyi mata Kara Hajiya, Ni ke, 'yanuwanta ita kanta da sauran jamaa sun san haka sai dai in za aki gaskiya."
Ta daga masa hannu "Naji, naji meye hujjarka na son amsar sa?"

Ya gyara zama "Hujjata ya dawo cikin 'yanuwansa ya zauna gaba days ba a rinka yawo da hankalinsa ba, Kuma ke da kike wannan magana da zaran ita iwar tasa ta sami miji ba dawo mana dashi za a ayi ba?"

Ta dade Bata ce dashi komi ba zuwa can tace "Hakane na amince da batunka amma Ina ganin da abinda za ayi a magance wannan matsalar ta bangarenmu da na uwar yaron saurara:

Ni a hakikanin gaskiya tunda Allah ya amshi ran danuwanka nike tunanin baka shawarar auren Rahima....

Bai bari ta karisa bs ya buga kirji ya zabura kamar zai tashi tsaye ya koma ya tsugunna jikinsa ba inda baya rawa, ya kama kansa da hannu biyu ya rinka jinjina maganar a ransa, nan take idanunsa suka rikide suka canza launi maimakon farare sol, ya bude baki yai magana kalmar ta kasa fitowa ya koma ya zauna yaraf saboda matukar sanyin da jikinsa yayi sai kace Wanda ya kwana ya yini Yana aikin wahala ba ci ba Sha.
Ta dauki tsawon lokaci kafin ta kallesa da kyau tace "Maganar da nai maka na auren ne ya firgita ka har ka fita hayyacinka?"

Yaja dogon numfashi ya saki ajiyar zuciya, sannan ya dago Kai a hankali ya kalli mahaifiyarta yace "Hajiya idan ma auren zan kara in rasa wace zan aura sai matar kanina da ya rasu, ki tuna yadda muke dashi fa, idan anyi hakan ba a kyauta ba."

Ta danyi murmushi saboda tayi niyyar hada auren nan ikon Allah ne kadai zai hana yuwwarsa. Tace "Ni kuwa a nawa tunanin yadda kuke da danuwan naka ne zaisa ka amince a kulla wannan abu don kaji dadin rike amanar da ya damka maka?"
Ya girgiza Kai "Kayya ba sai na kaiga hakan ba duk inda take zanyi kokarin taimaka mata gwargwadon zarafina, yaro kuwa dama namu duk da haka ba Zan tauye mata hakkinta matsayinta na uwa ba dole zamu bata damar kulawa da al'amuran danta a duk lokacin da bukata ta taso."
Chapter 10 · 0% Book details