Sashe 48
Rahima Complete Hausa Novel.txt · about 9 min read
Duk karshen wata suke haduwa family ana sauke qur'ani a gidan Daktan, in an kare ayi adduoi ga dukkan mamata da masu rayuwar, iyaye, 'ya'ya, 'yanuwa da abokan arziki, jiharsu da kasarsu baki daya. Duk ranar jumma'a za a dafa abinci a rinka rabawa mabukata sadaka duk don neman yardar Ubangiji da neman karin yalwarsa cikin dukkan al'amurran ratuwarsu.
Aikin Dr Haseeb sai dada bunkasa yake, sunansa na dada yaduwa yayinda yaci gaba da bude rassuna jiha-jiha Yana samo kwararrun likitoci Yana zubawa
Gwamnatin tarayya ta yaba da kwazonea kwarai suka bashi mukamin *Minister for health* Yace bai so hidimomi sunyi masa yawa...
Mata da 'yanuwa suka yi masa ca! Bai amince ba saida Hajiyarsa tasa baki tace "Ya Allah zai maka daukaka ka butulce? Hidimomi ba Allah ke taimakonka tafiyar da komi ba ko da karfinka kake?"
Ya amsa da zuciya guda ya fara aiki.
Kamar ba za a sake haihuwa gidan ministan ba domin Saida Ummi ta shekara uku aka samar mata kani, wannan karon sai ga kyakkyawar yaro, ga tsawo ga kiba, babansa zahiri..
Ranar suna Saida kowa yai kwalla da yaji sunansa *Rabiu*
Nauyi kam ya karu kan Daktan, ga na iyalinsa, ga na Mahaifiyarsa, 'yanuwa dana yanuwan Zuwaira ga na jama'an Annabi da suke cin arzikinsa banda na aikinsa, ya zama bai da lokacin kansa.
A ka zo batun komawa Abuja Zuwaira tace sai dai Rahima ta tafi domin ta sakankance ita dince ce *star* din Haseeb, ta kuma hakura da haka duk da cewa ba nuna banbanci yake tsakaninsu a zahiri ba, Rahimar taki yarda da shawarar Aunyn ta domin tsakaninta da ita girmamawa ce.
Da kansa takobin dagan ya raba gardama cewan kowacce zata rinka zuwa wata uku ta dawo dayan ta tafi Kuma, wace lokacin hutu ya shigo cikin turn dinta ta tafi da yara.
Zuwaira ta sake samun 'yar bebinta 'yar caraf kyakkyawa, da ganinta tace wannan ai Rahima ce,kamar yana jiran ta furta, ministan ya rada mata suna *Rahima* suna kiranta Amira.
Zuwaira na murna ita kuwa wace akayi dominta ta korafin me yasa ba a fara sanya sunan Zuwaira ba?
Ya kalleta yace "Banyi gwaninta ba kenan?"
Ta amsa "Wallahi kayi sosai na kuma ji dadi nagode amma kayi min alkawarin idan muddin na haifi mace Zuwaira ce."
Yace "Allah ya kawo cikin, shin ko har an samu?"
To Allah yayi an haihun amma namiji aka samu sai yaya kenan? Ya rada masa suna Habibullah.
Shekaru sun mika kwarai, tuni Dr Abdul Haseeb Junaid ya ajiye aikin gwamnati bayan shekaru takkwas yana bautawa kasarsa a matsayin ministan lafiya.
'Ya'yansu maza sun kare univertsity. Junaid (Khalifa) Engineer ne, Mohammad(Abba) Architect, Abdul Haseeb karami ya bi sahun babansa ya zama likitan kwakwalwa, yana kasar Bulgeria karo ilmi.
'Yan matan Kuma Muhibba ta dage saita zama irin Dr Kausar ta cikin littafin Anti Saliha Zumuncin Zamani, ita din Gynaecologist ce, Ummul Salama Lawyer ce don ita Bartister Tahir ne gwaninta(Son Zuciya) Ummi Habiba sha'awar Boutique din Sufab ya tunzuro ta da yadda ita kanta Surayuar ke tafiyar da business dinta da son taimakon iyayenta yasa ta karanta Business Administration yayinda Amira Rahima ke son zama cikakkiyar malamar makatanta mai zaman kanta irin na Sa'adatun Sagir haka dan autan gidan Daktan yace shi malamin lissafi zai zama, so Habibullah mathematician ne.
Wata rana Daktan ta tara manyan 'ya'yansa lokacin Abdul karami ya kare karatunsa yace lokaci yayi da kowannansu zai fitar da abokiyar rayuwarsa.
Ba bata lokaci Junaid ya nuna Walida diyar Maryam yake so wace ke zuwa hutu wajen Innarta Rahima, Muhammad yace Nabila diyar Uncle Hayatu. Wadannan 'yan Mata duk karatu suke a B.U.K. ne, Walida na karanta Mass Communications tunda a rayuwarta Laila Tahir Mutallib ce role model dinta, Nabils na karanta Economics.
Idan ta bi daga-daga na kurya kan Sha Kashi, Abdul Haseeb junior yayi shiru bai ce komi ba, to shima miskilin ne irin uwarsa da wan uban, to Barewa tayi gudu ne danta yai rarrafe? Baban nasa yaxe ya rubuto sunan wace yake so tunda ba zai furta ba, ya rubuta ya ajiye, yana fita ya dauki takardar ya warware, abinda ya gani yai matukar faranta ransa, ba domin namiji yake ba da yai guda Amma yayi abinda yafi dacewa yayi a irin yanayin, ya daga hannuwansa sama yace "Tsarki ya tabbata gareka ya Allah Ubangijin Al'Arshi mai girma!!!
Ya sake duban takardar da Abdul ya rubuta *Daddy Rahima Amira ce mata ta Insha Allahu*
Ya juya takardar yana mamakin ko ya aka yi yaran suka yi tunanin hada auren zumunci gaba dayansu oho?
23/09/2020, 12:31 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami
54
Iyaye, 'yanuwa da kakanni kama da abokan arziki da sauran jama'ar da suka ji labarin hada wadannan igiyoyin aure sai sha'awa da murna suke.
Kasa-kasa ba inda Daktan bai aika da katin gayyata ba, duk wasu masu hulda da asibitocinsa, abokai da tawagar shugaban kasa da kusoshin gwamnatocin jihohin Arewa sun halarci wannan gayarumin dauren aurarraki.
Da yake al'amarun tuwona Mai na ne shi kansa Daktan ya rasa inda zai fi maida hankali a sha'anin, to kusan shine uban angwaye da amaren baki daya, haka ya wakilta kanninsa da abokan arziki aka taru aka yi komi cikin tsari gwanin sha'awa.
A wajen bukin ne su Ummul Salama suka hadu da masoyansu ita ta hadu da abokin Khalifa, Muhibba dan abokin babanta balarabe nan na Riyadh ke sonta, har sun amincewa juna, sai adduar Allah ya nunawa iyaye lokacin nasu bukin.
Bayan an gama shagalin da wata guda, kura ta lafa, Zuwaira ce da Rahima ke zaune a main parlour suna hira, sai kallon Rahimar take cike da sha'awa tana yaba yadda take tafiyar da al'amurran rayuwarta ta yau da kullum, me zata ce da wannan baiwar Allah? Gaskiya sai godiya da adduar Allah ya saka mata da khairan domin a dalilinta ita kanta da 'ya'yanta sun samu nagartacciyar rayuwa, ta sami kan maigidanta yanzun girmamata yake sabanin da can inda aka fito.....
Karar waya ta dawo da ita daga duniyar tunani, tayi firgigit daidai Rahima ta dauka ta sallama, can taji ta rafka salati ta kalli Zuwaira, ita Kuma a firgice tace "Me ya faru wa Kuma muka rasa?"
Rahima tace "Allah yaiwa Husaina rasuwa sanadiyyar accident.....Zuwaira tayi kasake tsoron Allah ya Kara kamata, duniyar kenan mai halin dan mangwaro, sai ta bari ka saki jiki kana tsotso kana jin zakinta ta subuce maka. Ita yaushe rabonta da ita tun ranar da ta taho gidanta shekarun baya suka rabu baran-baran amma tana da labarin sheke ayar da take abinta har Allah ya amshi ran ta.
Ta nisa oh Allsh na gode maka da ka taro Ni ka dawo dani Kan hanya madaidaiciya, tun lokacin tuba bai kure mata ba.
Basu Kara firguta da al'amarin Ubangiji ba Saida suka ji labarin ya baza gari cewa kasa taking amsar gawar Husaina, duk inda aka tona ko a ga maciji ko kunamu har jamaa suka gaji da watangaririya da gawarta, bata samu hutun da gawar mutum ke matukar bukata ba sai dare da malamai suka taru suka rinka adduar neman gafara da rahamar Ubangiji.
Ya Allah ka shiryemu, ka shirya gaba da bayanmu dama da hauni, kasa mu fi karfin zuciyarmu kar ka kawata mana kyalkyalin duniya, abinda ya faru da Husaina ya zama izna/ishara ga yawancin matan zamani da suka maida aure abin wulakantawa, Allah ya yafe mana dimbin zunubanmu.
Wata rana Rahima na kishingide bisa doguwar kujera cikin shiryayyu falon sabon gidan da suka koma, maigida ya Kira wayarya cewan yana son ganinta.
Ta mike da hanzari ta gyara rigar da ta saka ta wata bugaggiyar shadda coffee and orange colour, anyi mata dinkin boubou da aka gewaye da cord lace gwanin sha'awa, kayan da launin kayan sun amshi jikinta sosai, ta fito dagwas-dagwas take takawa zuwa falonsa, ta sallama ya amsa ta shiga ta zauna.
Tunda ta bullo ya kura mata ido har ta iso ta zauna kusa dashi bai dai na kallonta ba, hakika kwalliyar ta burge wansa aka yita dominsa ko da bai furta ba ta fahimci cikin kwarar idanunsa,ta matsa kusa kamshin man shafarwata (avon) *soft musk* suka daki hancinsa, ya rumtse ido ya bude, tayi kasa da nata idanun saboda kunya tace"Gani, Daktan yana bukatar wani abu ne?"
Ya amsa "Uhhmm uhhmm. Kuma yaci gaba da kallonta dai.
Nan take ta urunce ta fara kaduwa, zuciyarta ta fara harbawa tasa hannu ta danne saitin wajen, cikin makyarkyatar murya tace "Dakta your gaze is so intense, it makes me nervous, don Allah me kake so?"
Kafin ya bata amsarsa ya rungumota cikin sarkakkiyar murya yace "What I want in my life is your love forever, can you give me that much?"
Ta kwantar da kanta a kirjinsa tace *Na dade da mika maka zuciyata cikin so da kaunarka ba don komi ba sai domin ka sanya min nishadi cikin rayuwata tunda ka amince na zama daya bangaren jikinka, ka fahimci bukata ta, ka zama babban aminina, Ya Haseeb na sadaukar da kaina da soyayyata gareka da fatar zamu kasance a haka har abada."
Dakta Haseeb yai murmushinsa mai Kara sakata cikin shaukin kaunarsa yace "Na gode sosai my dear. Nayi murna da farin cikin jin kalamanki, Ina Kara godewa Allah SWT da Kara salati ga Manzon Tsira wanda ya luras damu sai abu hudu sun hadu sannan mutum ke da azikin rayuwar duniya. Na farko mace Saliha ta gari, na biyu makwabci nagartacce, na uku abin hawa lafiyayye sai ma hudu gida mai fadi. Kinga duk Ubangiji sarkin sarauta ya hore min dukkan wadannan, fatana yanzun Allah tasa mu gama da sauran tsoffinmu lafiya, ya bamu ikon ci gaba da sauke hakkokinsu dana iyalina, sannan yai mana kyakkyawar cikawa idan lokacinmu yayi.
Rahima ta amsa "Ameen ya Zuljalali wal ikram, Dakta."
Wadannan dattjai biyu sunci gaba da tafiyar da rayuwarsu cikin so da kaunar juna duk da sun fara manyanta an kai ga fara ajiye jikoki, kullum soyayyarsu Kara tofo take tamkar ana mata ban ruwa daman ance *so* bai tsufa sai dai masoya su tsufa.
A ko yaushe Rahima ta Kan zauna ta rinka kwatanta Haseeb da taurarin littafin Anti Saliha. A miskillancin sa za su zo daya da Faruk, a tsabar kwarjininsa sai dai ta hadashi da Abdul Nasir, wajen sadaukar da Kai wajen aikinsa shi da Tahir suna mata kama, to wajen son zumunci da kaunar 'yanuwansa fa dole ta hada shi da Sagir.
A fagen matan kuwa ta rasa wacce zata kwatanta kanta da it's saboda tun daga Surayyar, Kausar, Laila da Sa'adatun kowaccensu sarauniyya ce Kuma tauraruwar dake haska zuciyar masoyinta don haka data hada ta tace ta tankade ta rairaye bata samu abun zubarwa ba daga mazan har matan domin kowanne naji da abokin rayuwarsa tamkar yadda suke ji da rayukansu.
Sai dai duk a je a komo abubuwan da take ganin sune jigon rayuwar wadannan ma'aurata in ka debe tsantsar so da kaunar juna sune aminci, hakuri, yarda, mutunci, kyautatawa da barin wa Wanda ya hadasu dukkan al'amurransu, baya ga sanya shi a gaba da bayansu tare da yin kyawawan adduoi da kaurara godiyarsu gareshi gwani sarkin Sarakuna.
Har yanzun a iya tunaninta ta rasa shin idan ta kwatanta rayuwar aurenta da nasu, ita dun wace lamba za a bata?
Da yake bai dace ta baiwa kanta amsa ba gudun son kai, ta hakura ta barwa jama'a suyi mata alkalancin.
*SUBHANALLAH WALHAMDULILLAH WA LA ILAHA ILLALAH WAL LAHU AKBAR
WA LAHAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYIL AZEEM.*