← Book details Nida Shugaban Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 53

Sashe 9

Nida Shugaban Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" ni xan Baku amsar tambayoyinku... *ni da shugabankasa* mun kasance muna son junanmu tun da dadewa, shi ba mutumin banxa bane kamar yadda kuke zargi shi jarumi ne mai mutunci yana da Amana da rikon gaskiya"

Wancan mutumin ya juya yace
" kina nufin soyayya kuke yi da mr President?

" ehh ...soyayya muke"

" toh meyasa yaki ya fada da bakinsa?
" kunyace kasan Fulani ai"

"Kin tabbata"
"Na tabbata hakan ne" ta gyada kai suna kallon juna ita da mutumin shikam beji dadin xuwanta ba yafi so a CE an cire mr President akan mulkinsa.

Yan jarida Suka rubuta duk abubuwan da yake faruwa a yayinda masu gidan talabijin Suka fara haska nasu a wannan lokacin duk duniya ana kallon abunda yake faruwa.
Mr President ya sunkuyar da kai shikam baiso shuairat ta kawo kanta bah toh meyasa ta ceci rayuwarsa daga zargi da ake masa? Duk da cewa yasan abun ya shafe ta tunda tare aka gansu Amma baiyi tunanin cewa xata hada karya haka don.....
" mr President ko xaka bamu Karin bayani kan abunda ta fada?
Shi bai ma San yan jarida sunxo kusa dashi bah

" babu abunda xan fada a kai" ya basu amsa kai tsaye shuairat ta karasa kusa dashi ta xauna tana kirkiro murmushin dole nan kuwa aka fara daukansu hotuna mr President kam mamakin alamarin yake wai yarinya kamar an turo ta.
An gama meeting lfy bayan an wanke mr President daga xargin da ake masa, suna fita yace a nemo masa shuairat a ckn mota Suka xauna su biyu kawai bayan an rufe musu kofar ya juya yana kallonta yace

"Meyasa kike shiga min rayuwa ? Na gaya miki ki fita sabga ta"

" am sorry mr President but idan ban fito na kashe maganar ba xaka Iya rasa kujerar ...

" shut upp! N so wat idan na rasa shi? Kinsan kuskuren da kika tafka? Kinsan matsalar da kika jefa kanki a ciki? Kinsan balain da kika jefani ciki? Da kinsani da baki aikata hakan bah...Ayshah kinyi kuskure "

" mr President.....
"Shut up! Ban gama bah"
Ya tare nimfashinta yana huci kamar wani xaki

" Aysha meyasa kike shiga rayuwata? Meyasa xaki jawomin matsala a Rayuwa? Meyasa ? Meyasa?

Shuairat ta fashe da kuka tana hawaye tsakaninta da Allah mr President ya gitgizata yana nuna wajen window da Dan yatsa yace
" kinsan matsalar da xafi fuskanta ? Me xaki gayawa wadancan nan gaba? Shin har yaushe xaki cigaba da musu karyar? Shin me xan gayawa iyayena? Tell me!
Ta cigaba da kukanta me ban tausayi yayi shiru kansa ya daga ya kura mata ido dakyar yace
" is ok stop crying"
Bata sauraresa ba ta cigaba da kukanta ya xuba mata ido kawai se kuma ya sake cewa

"Don Allah ki bar kukan ya isa pls"
Ta sunkuyar da kai kasa
"Let's talk pls "wayarsa CE ta fara ringing umaimace ba sai angaya masa bah ya daga kara a kunne

" I hate u dad" daga jin muryarta yasan tana kuka ta kashe wayar yayi shiru jikinsa ya mutu gaba daya duniyar ta masa xafi.
Shuairat CE ta lura da halin da yake ciki bayan ta share fuskarta a hnkli tace

"Mr president ar u ok'
"Am fine I just need to go home"

"Umaima koh?
Ckn mamaki yake kallonta ya akayi ta gane cewa umaima CE? n a ina tasan umaima?
Murmushi shuairat tayi don taga yNa mamaki tace

"Ka lallabata kasan karamace "
Daga nan ta bude mota xata fita

"Ayshah!
Ya kira sunan da wani irin salo ta dakata don jin me zai fada

"I'll c yhu gobe we have alot to talk about"
Daga nan ta fita ba tare tayi magana bah.

*Reefat*CE.....Lov u all😘😘
[2/21, 2:37 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*21*
By *Reefat yahya*

Umaima CE zaune a falonta kuka takeyi tmkar ranta xe fita mr President ya shigo ckn hanzari ya karasa kusa da ita ya kai hannu xe taba ta tayi saurin komawa da baya

"Dad bana son ganinka pls leave"

"Baby am so sorry let me explain pls"

"Explain wat just go"
Babu irin lallarshin duniyan nan da mr President beyi ba Amma firr taki sauraronsa haka ya hakura ya koma bangarensa da damuwa fal a ckn ransa.
Umaima ta aika a kira mata bash an shaida mata baya gari haka ta yini jugum xuciyarta na tafarfasa tana jin kishin wannan yarinyar da ko sunanta bata rike bah.

***************

Shukrah CE tare da bash suna hira ckn kwanciyar hnkli ya tmbayeta irin kayan da take so a saka mata ckn akwatin lefe , an sanya ranan auren nasu nan da wata1 ya kai mata tsarabar turamen zani 2 da lace da kuma gown se sabuwar wayar Samsung galaxy da turaruka da mai da sabulu masu kyau da sadan gaske.

"Nagode sosai yaya Allah ya kara budi"

"Ameen matata"
Ta sunkuyar da kai ckn jin kunya
"Aw kunyata kike ji?
"Nifa bana jin kunyarka"

"Toh ki daga ido ki kalleni"
Murmushi tayi ta sunkuyar da kai hmmm masoya.
Haka Suka kasance suna hirarsu irinta masoya daga karshe Suka rabu ya mata sallama domin gobe xe koma Abj, kamar baxasu rabu bah shukrah har hawaye take 😳😳ahh abun ba sauki an kamu) dakyar ya lallabata ta daina kuka sannan ya koma gida da shirin tafiya.

Tana kwance a falonsu idanunta a lumshe tana tuna kalaman mr President mama CE ta shigo ta xauna a gefenta

"Ya'r baba tashi ki xauna magana zamuyi"

"Ina jinki mama"
"Menene gaskiyan alamarin dangane da magananki da shugabankasa "

"Mama wa ya gaya miki?

"Ina xaune gaban TV na gani da idona kin fito kinyi magana"

"Mama...nifa ba komi tsakaninmu kawai dai..."
Sai kuma tayi shiru ta kasa magana.

"Kawai me? Shuairat kibi a hnkli mutumin nan ba saan aurenki bane mu talakawa masu rufin asiri Muna...

"Pls mama nace miki ba komi tsakaninmu"
Daga nan ta tashi ta koma dakinta ta kwanta ta rasa me ke mata dadi a duniyar ko wane hali mr President yake cki oho! Ko ya zasu kaya da umaima oho! Haka ta kasance har bacci yayi gaba da ita.

A bangaren mr President ma hakan ta kasance ya kwanta yana ta tunane -tunane wayarsa CE ta hau ruri dum ...xuciyarsa ta buga don ganin kiran mahaifinsa

"Dady nah"
"Boy ya kake "
"Alhamdulillh ya gida ya momsi "

"Gata kusa dani lfyanmu kalau, na bugo ne don tabbatar da news da gani"

"Ohh dady is just...
"Son am happy zanzo next week sai ka nuna min gidan iyayenta idan Ya'r gidan mutunci CE sai a fara maganar aurenku koh"

"Damm...dammm! Kirjinsa ta buga innalillahi ya zaiyi da wannan kwamacalan

"Boy kana ji Nah, am so proud of u, kayi tunani mai kyau ai xamanka haka nan ba dadi "

"Dady....
"Don't worry boy na fahimceka momsi tana gaisheka sai anjima takkia of urslf" garam ya kashe wayar
Mr President ya rintse ido yana maimaita innalillahi lallai rayuwarsa tana ckn matsala Allah ne kadai xai fiddashi.ya rufe ido nan ya hango shuairat yana siffanta ta, doguwa CE siririya bata da hasken fata tana da dogon hanci da karamin baki tana da dogon gashi baki wuluk don ko ta daura dankwali rabin gashin nata a waje yake.tana da kyau dai-dai gorgodo toh amma ya zaayi ya aure ta? Babba da shi ? Yasan zai Iya haifanta don koda ta girmi umaima ma baxe wuce da shekara ko 2 xuwa 3.
To Amma wacece ita? A ina ta samu tarihin rayuwarsa? Shin auren nasu zai yiwu? Ya umaima xata yi idan taji xeyi aure? Kodai ya fito ya karyata labarin?
Shin idan yayi haka ya kyauta? Tambayoyin da ya fara jero wa kansa kenan ya kasa samun amsarsu.

Hmmmmmmmmm muje xuwa *Reefat* CE xata amsa muku wadannan tambayoyin..
Drop ur comments Lov u all😘😘😘

Vote: waye jarumi/jarumarka a ckn wannan littafin umaima" mr President" shuairat" basheer" shukrah"
Wane page yafi burgeki/burgeka....sai naji daga gareku
[2/21, 2:38 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*22*
By *Reefat yahya*

Bash ya shigo falon umaima tare da sallama dawowarsa kenan daga Adamawa ya samu sakon nemansa da take tana kwance tayi nisa ckn tunani ya sake maimaita sallama a karo na biyu ta tashi xaune tana ganin bash ta fashe da kuka.
Ckn rudewa bash ya karasa kusa da ita
"Lfy miss umaima?
Ta cigaba da kukan bata saurareshi bah ya rude sosai ya xauna dab da ita yana bata baki dakyar ta tsagaita kukan ta fara magana

"Kai kadai ne ka ragemin a duk fadin garin nan Kaine zan Iya fuskanta in gaya maka duk wata matsalata bani da kowa a ynxu se kai"

"Meke faruwa ? Ina dad naki"
"I hate him bana.

"Shhhh....hannu yasa ya toshe mata baki yana girgiza kai

"Don't ever say dat pls, mahaifinki duk laifin da ya miki he don't deserve dis"
"But bana sonmu ni da Kani Nah baya kulamu yafi son budurwarsa"

"No! Yana sonku kece baki fahimcesa bah kuma wancan yarinyar ba abunda yake tsakaninsu she is a reporter"

"Hmmm basheer kenan! Amma de baka kalli news ba koh? Yarinyar da ta fito da bakinta tace sun Dade suna soyayya"

"Waat? No! No! Umaima I tink...shit! Ya buga kujera da karfi take launin idanunsa sun canza
"Basheer ya na ganka wani iri? Any problem?

"Ba komai kaina ke min ciwo"
"Sorry bari na dauko maka magani"

"No! Am ok" xuciyarsa na tafarfasa shin meyasa shuairat xata yi haka?

"Bash ina kaje an cemin kayi tafiya?

"Uhmm..Adamawa naje wllhi"
"Really ! Dama kai Dan jahar su dad ne, no wonder yake sonka"Murmushi yayi yace

"Haka ne!
"Ehh...dad yana sonka sosai"

"Abunda nake so dake shine ki kwantar da hnklinki nasan dad naki yana sonku sosai batun yafi son wata duk be taso bah , nasan akwai wani boyayyen alamari dangane da yarinyar nan Amma xan bincika da kaina xan gano koma menene"
Chapter 9 · 0% Book details