← Book details Nida Shugaban Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 53

Sashe 12

Nida Shugaban Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mr President yana xaune a ofishinsa bayan sun gama ganawa da vice dinsa akwai xasuyi tafiya xuwa China don kula da harkar kasuwanci tsakanin najeriya da china .
Bash ne ya shigo masa da wasu files ya ajiye xe fita
" a moment pls"
Bash ya juya ya dawo a tsaya a gabansa mr President ya nuna masa kujera ya xauna wato alamarin da ya bashi mamaki kenan saboda tunda suke mr President bai taba masa hakan bah.

"Basheer wani taimako nake so ka min"

"Ina jinka mr President"
"Wato lura kusancinka da yata yayi karfi har nake ganin cewa xata Iya aikata duk abunda ka umarceta, basheer ina so ka bawa yata hakuri akan maganata da Aysha bello pls"

"Don't worry mr President xan mata magana insha Allah "

"Nagode" bash ya tashi har ya kai bakin kofa mr President yace

"N I want to know about Aysha bello"

"Ok sir! Ya bashi amsa sannan yasa kai fice.

A falonsu ya sameta da masu aiki suna mata gyaran farce tana waya, ya shigo tare da sallama
Fuskarta ne ya fadada da murmushi nan kuwa ta kashe wayar

"Aboki se yau"
"Yes my kawa" ya maida mata martani sannan ya samu kujera da yake kallon nata ya xauna nan ta sallami masu aikin bayan ta umarcesu da su kawo kayan motsa baki.

"Ya'r gatan dad ya kike"

"Lfy ya aiki"
"Alhamdulillh ya hutawa"

"Ya kadaici dai koh"
Sun Dan taba hira bash yace

"Kawa me yake damun dad naki ne kwanan nan duka naga yana ramewa"

"Oho! Maybe ya bata da budurwarsa"

"No! It can't b ki dai bincika ki gano matsalar he is ur dad after all"
Tayi shiru tana naxarin maganganun nasa kenan dad dinsu ya rame saboda tana fushi da shi? Dama haka ya damu da ita? Lallai bata kyauta masa bah, kamar yadda take fama da kadaici shima hakan yake fama amma meyasa tayi haka?
Hawayene Suka gangaro a fuskarta nan ta sunkuyar da kai kasa ta fara magana

"Laifina ne na daina kulashi ya bani hakuri har ya gaji ban saurareshi bah"
Nan kuwa ta fara kuka tamkar ranta xe fita

"Me kika masa umaima?

"Akan maganar wannan yarinyar "

"Haba umaima a ina kika taba jin anyi fushi da iyaye? Shin baki ganin irin biyayyar da dad dinku yake nunawa iyayensa ne? Meyasa baxakiyi koyi da halayensa ba?
Ta cigaba da kukanta ba kakkautawa bash kuma ya cigaba da magana

"Tabbas kinyi kuskure Amma is not late kije gun mahaifinki ki nemi gafararsa idan har baki son fadawa ga halaka ". Nan ya kwace labarin komi dangane da alakar shuairat da mr President ya gaya mata cki kuwa har batun aurensu jikinta ya mutu sosai ynxu ne ta gane cewa dad bashi da laifi ko kadan.
Bash ya mata nasiha me ratsa jiki sannan ya tashi ya tafi.

Mr President yana xaune ya buga uban tagumi a hnkli aka tura kofar umaima CE ta shigo tamkar barauniya.sum sum ta karasa kusa dashi

"Dad....
Se kuma hawaye sun taru a idanunta .
Hannu ya bude mata ta fada jikinsa tana kuka yana rarrashinta dakyar ta daina kuka tace

"Dad am sorry ka yafe min sharrin shaidan ne"

"Is ok baby, idan har kin fahimceni dai shikenan "

"Dad I understand ba laifinka bane kuma itama taimakonka tayi "

"Am happy dat u know ynxu me kuke bukata cos gobe ko jibi xan tafi China"

"Bana bukatar komi dad Allah ya tsare ka ya dawo da kai lfy"

"Ameen my baby"
Haka Suka kasance suna hira ckn farin ciki da jin dadi ya kalli fuskarta yace

"Baby kodai an samo min suruki ne"

"Laa...dad babu fah"

"Are u sure? Wat of basheer?

"Dad! Ta fada tana dariya bash da yake bakin kofa yayi murmushi sannan ya juya ya bar wajen.

😘😘😘😘to u my fans
[2/21, 2:38 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*28*
By *Reefat yahya*

Karfe 5dai dai bash yayi parking a kofar gidansu na mubi yaran anguwan ne Suka tayasu shigar da kaya ckn gida.
Mama da baba Suka fito ana musu maraba da xuwa tuni shuairat kuwa ta kama hanyar gidan mutuniyar tata ckn xumudi ta shigo tare da sallama.
Inna tana tankade gari shukrah kuwa tana shara aikuwa sun kankame juna ckn jin dadi bayan sun gaisa da inna dakin shukrah Suka shige tare da sauke labule
( ni kuma nace baxaa barni a baya bah ..lolx)
" kai bestie kin ga hasken da kikayi kuwa? Se shining kawai kike yi"

"Ya'r rainin wayo na kaiki ne, ke amarya ce fah ansha gyaran jiki ana ta shinning"
" ya gida ya hanya ya su mama"
"Lfynsu lau ya shirye2"
Shukrah ta harareta ckn tsigar wasa tace
"Wane shirye shirye"
"Oh! Wa yaga su bestie amarya"
"Kya ji dashi ya'r nema"
"Oho dai! Ana so ana kaiwa kasuwa , yawwa baki ban labarin haduwarku da yaya bah kince masa I love u ko ya?

" munafuka ai shuairat kina fama wallhi"
"Lolx muna fama dai"
Haka Suka kasance suna hirar yaushe gamo shukrah ta kawo mata dambun xogale ta ci tayi hamdala har magarib sannan ta tashi ta kama hNyar gida shukrah tana mata rakiya shuairat ta juya ta kalleta tana murmushi tace

"Anti shukrah ki koma se munxo xance to nyt" shukrah ta kai mata duka suna dariya Suka rabu.

Hakan ko akayi bayan sallar isha bash ya shirya ckn kananan kaya se qamshin turare ke tashi a jikinsa yayi sallama ya tafi shuairat ta yi masa tsiya har ta gaji yana dariya ya tafi.
Bayan kwana biyu aka kai lefe jamaa na ta yabawa nan aka fara shirye2n biki ba kama hannun yaro su shuairat kirjin biki itace kan gaba a kowane bangare. babbar kawa kuma kanwar ango, sun shirya xasuyi kauyawa day da walima se kuma kamu night"

**********
A can birnin tarayya kuwa mr President ya tafi China don gudanar da harkokinsa
Umaima kuwa gidan ya mata fadi gashi ta nemi layin bash baya shiga kuma ta tambaya ance mata yayi tafiya sultan ne abokin hirarta se kuma watsap da Facebook, gashi makarantar su ana hutu .
Tana kwance a falonsu yau taji shaawar shiga watsap dinta ta bude kenan mssgs Suka fara shigowa anyi adding dinta a wani grp din *Gidan gyara* mata ne xalla a GRP din, batasan wacece admin din bah kawai ta ynke shawarar yin magana a grp din ta rubuta "salam" ta tura bayan minti2 Meenat da esha Suka amsa mata😊 "wslm"
"Pls wacece tayi adding dina a wannan grp din? Bayan wani Dan lokaci mssg ya shigo from *Reefat* tace "nice nayi add din ki" Mmn Ummul ta tura novel din *tana tare da ni"* kamar da wasa umaima ta fara karanta novel din se kuma taji grp din ya burge tah anata hira a grp din so lively haka, tun tana sharewa har ta fara contributing ta Dan saba da yan grp din har magariba tayi sannan kowacce ta tashi don yin sallah.

Bayan umaima ta idar da sallah ta sake daukan phn din ta shiga grp taga anyi posting din wasu pre-wedin pix kala2 batayi download bah ta cigaba da karanta novel din *yar Riko* da aka tura, chan an sake tura wasu pix din se a kasan aka rubuta

"Matan gidan nan u r invited auren yaya nah gobe kamu night"
Cmnts aka fara aikowa
"Wow couples din sunyi kyau"
Su Rabi Oga da su momi Ummi da zaheeda da sauransu duk sunce xasu je auren.
Haka nan umaima taji tana shaawar bude hotunAn tayi download daya yana buduwa
😳😳😳 dam....dam....xuciyarta ta buga guess wat?
Hoton shukrah CE da basheer sunyi kyau sosai nan take wani jiri ya fara diban umaima
😳toh fah....hmmmm"
Wani xaxxabi ne ya rufeta haka ta kwanta akan sallaya idanunta na fitar da wasu xaxxafan hawaye

😥😥eyya umaima nah...

Lols Ku biyoni

*Reefat*ce😘😘😘😘😘
[2/21, 2:38 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*29*
By *Reefat yahya*

Karfe 7 katon multipurpose hall din Adamawa state university mubi, ta cika makil da jamaa ga yan mata samari manyan mata da dai sauransu can na hango amarya tare da kawayenta dai Kelli suke ansha kyau.
Decoration din hall din ma abin kallo ne anyi decorating da purple n silver se fulawas masu kyau abun dai se Wanda ya gani.
Kawayen amarya na sanye da purple head da material ash colour n silver wyl amarya kuwa ta saka purple material da silver n ash colour head tie sunyi kyau sosai an fara program sannN ango ya shigo da tawagarsa ckn fararen kaya masu kyau sai shinning suke.
Anfara gabatar da taro su shuairat anyi rawa har an gaJi ga abinci da drinks kala kala anci ansha an xuba kudi kamar ba gobe su Rabi Oga tun daga Jada aka tashi aka je auren😜 ga su nan dai matan gidan gyara birjik anyi ta kashe pix xaa canza dp.nima dakyar nasamu nayi pix 2 da amarya da kuma shuairat...
Bayan angama taro aka watse kowa ya kama hanyar gida.

A can Abj kuwa umaima aka kwantar a asibiti in banda kuka ba abunda take a waya aka hadata da mr President tmbayar duniyan nan ya mata Amma Sam tace xaxxabi ne ke damunta...( Kutt...Ashe dama she is in love wit yaya bash eyya poor umaima😥😥....lolx😜)
Bayan an bata magunguna aka sallameta Suka koma gida tare da masu kula da lfyarta, yan uwan mamanta se kira sukeyi suna mata sannu haka nan iyayen mr President ma sun kirata sun gaishe ta.

****†

D next day da yamma su shuairat Suka hada walima na mata xalla anyi nasiha sosai akan hakkin aure shukrah ko har kuka se da tayi shuairat na tsokanRta
BayN wani lokaci Suka raba Qur'an da handfan da kuma memo daga nan aka raba abinci sannan akayi adua aka watse.

Ran jumaa aka daura auren shukrah Abubakar da Basheer Bello maiha daurin auren ya samu jamaa sosai.da dare aka kai amarya gidan mijinta.
D next day akayi fansar amarya da ango sannan da dare aka sallami kawaye shikenan jamaa kowa ya watse.
Chapter 12 · 0% Book details