← Book details Nida Shugaban Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 53

Sashe 20

Nida Shugaban Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani bodyguard ne ya shigo ya sanar dasu cewa Mr president na son ganin shuairat tayi shiru bata CE komai bah anti mairo CE ta jawota xuwa daki ta kara fesa mata turarurruka iri2 sannan ta kara powder da lipstick tace mata
"Saura kije kina wani nokewa , feel free mijinki ne"
Murmushi kawai shuairat tayi tana mamaki halaye irin na anti mairo daga nan ta sauka zuwa kasa inda bodyguard din yake jiranta daga nan Suka wuce ckn mota ya kaita bangaren Mr president.
Sau daya ta taba zuwa amma yau taga komai ya canza mata an sake fenti da furniture's da komi a bakin kofa bodyguard din ya tsaya ta karasa.
Bata sameshi a falon farko bah don haka ta wuce personal falonsa ta shigo tare da sallama yana zaune ckn manyan kaya yayi kyau sosai ko don ta kwana2 bata ganshi bane oho ya amsa ba tare da ya daga fuskarsa bah yana danna waya da alama wani yake son kira ta nemi waje ta zauna suna fuskantar juna. Shiru sukayi sai kuma ta tuna cewa ynxu itace kasa dashi nan kuwa a hnkli ta furta

"Ina kwana ur xcelency"
Wani kayataccen murmushi ya sakar mata duk da cewa baya kallonta sannan ya amsa ckn wani salon ji da kai

"My first lady kin tashi lfy"
"Lfy alhamdulillh"
"Hw was ur nite ya bakunta"

"Lfy kalau"
"Daz grt, dama na kiraki ne ina son jin nawa zaa sallami frenz naki"
Shiru kake ji ta rasa me zata gaya masa yaji shirun yayi yawa don haka ya daga ido 😳😳😳 masha Allah haka ya furta a ckn zuciyarsa dama yarinyar nan haka take da kyau? Wow..she luks soo...btiful" carab Suka hada ido a dai dai lokacinda shuairat ta daga kanta , kowannensu yayi saurin dauke kai zuciyoyinsu ne ke harbawa.Mr president ya daure yace

"Kinyi shiru"
"Uhmm...gskiya nima bansani bah just give dem...

"No first lady! I hate dat word "bansani bah" ki gayamin pls"
Nan ma tayi shiru sai kuma ta tashi ya bita da ido har ta kai bakin kofa yace
"Ina zakije kuma muna magana"

"Uhm...zanje gun anti mairo ne"

"Zakije ki tambayeta nawa ya dace ?
Murmushi yayi yana tunani shi kadai cewa lallai akwai yaranta a tattare da ita
"Ok dawo ki zauna tunda baki sani bah lemmi tink on my own" ba gardama ta koma ta zauna yana danna waya can ya kara a kunne yace
"Ka tura sakon da na baka jiya ?
Ok yes ka hada duka ka basu a ckn gida "
Daga nan ya kashe wayar ya maida kallonsa gareta sun kurawa juna ido can shuairat ta kauda fuskarta yana Murmushi sannan ya fara magana

"Aysha ynxu idan aka baki mukamin first lady haka zaki dinga yi?
Ta daga kai ckn rashin fahimta yace

"Yes! Wat I min is dai komi sai kin tambaya ? Bazakiyi on ur own bah?
Ta zumbura baki tace

"Ni...ni nace a bani first lady ne dama"
A hnkli ya taka xuwa gabanta ya sunguna idanunsa a kanta suna fuskntar juna shuairat ta sunkuyar da kai tana wasa da warwaronta yasa hannu ya daga habarta Suka kurawa juna ido yace

" ke matata CE dole zaki koyi yanda zaki gudanar da wasu harkokin on ur own , u have to fight Aysha"
Bash ne tare da wani bodyguard Suka shigo tare da sallama ganin halin da Suka tarar da ogan nasu a ciki ne yasa Suka bar wajen shuairat kuwa kunyane ya kamata haka nan Mr president ma nan da nan ya tashi ya koma kujerar da yake da ya zauna ya dannawa bash kira a waya Suka shigo Suka sanar dashi cewa yayi baki daga England nan ya tashi Suka fita tare shuairat kuwa bodyguard Suka rakata ta koma bangaren ta.

😍😍😍👍🏼😘lov u all
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*46*
By *Reefat yahya*

Ta shigo bangarenta kawayenta suna mata tsiya Hafsat tace
"Ohhh shuairat an kasa hakuri a jira mu koma mana"
Ummi tayi dariya tace

"Gane min hanya dai da ana nokewa wai tsoho zaa aura ba zancen love gashi nan tun baaje ko ina bah an fara lumewa"
Suka fashe da dariya Suka shewa anti mairo ta shigo tana dariya tace

"Rabu dasu baby nah love kam kowa ma yana yi sai Wanda bai samu bah , Ku kuwa Ku tashi Ku tattara mu bar musu gida ynxun nan"

Suna dariya se kuma Suka hau godiya abun arzikin da Mr president ya aiko musu kowacce an bata kaya lace super da kuma Holland se kudi 120k shuairat kam mamaki ne karara a fuskarta sai kuma ta share zancen haka nan su haj mairo ma an basu kudade Masu yawa daga nan ta sake Jan kunnen shuairat akan zaman da zatayi a gidan tare da koya mata wasu dabarun sarrafa miji Wanda ba sai na fada bah😜 nan sukayi sallama shuairat ta fara hawaye haj mairo tace kul..karki bata kwalliyanki daga nan motoci Suka kwace su sai gida aka bar amarya daga ita sai halayenta sai kuma masu aiki.
Sama ta haura sai ynxu ta samu damar karyawa tea ta hada sannan ta Debi chips kadan da kwai ta zauna ta cinye tas sannan ta dawo falo ta kunna TV MBC ta kama tana kallon film din "triple X" yan uwan Mr president ne Suka shigo sun Dan taba hira daga nan Suka shaida mata cewa yau zasu wuce Adamawa wasu kuma Kano wasu kd da kuma Lagos, cin-cin doughnut da cake ta diba musu da turarurruka masu yawa ta basu suna godiya Suka tafi. Haka masu aikin Suka shigo Suka gabatar da Kansu nan ma ta kawo musu abubuwa iri2 suna yaba mata Suka koma bakin aikinsu.

A can bangaren Mr president kuwa wasu turawa ne Suka zo tayashi murnan auren da yayi maza 3 da mata 2 dukkansu manyan mutane ne masu fada a ji a can kasar England daga fadar sarauniya Suka zo don haka Suka nemi ganin amaryar tasa Mr president ya daga waya bayan ya Dan fita daga dakin da aka sauke bakin nasa layin shuairat ya kira ringing 2 ta daga
"Hello ur xcelency"
Wani yarr...yaji a jikinsa dakyar ya saita kansa yace

"Ki shirya baki nayi kuma turawa ne suna son ganinki"

"Eyya...Mr president y not su bari xuwa dare Allah na gaji ynxu bacci zanyi"
Tayi maganan ne ckn wani salon shagwaba murmushi yayi shi kadai yasan ma'anar yace

"Ok sorry ki huta zuwa daren sai ki shirya koh"

"Ok tnk u my dear"
Nan ta kashe wayar ya tsaya Jim...tmkar mai tuna wani Abu sai kuma ya nanata kalamanta na karshe "tnk u my dear" nan ya sake yin murmushi haka nan tun jiya yake jin kansa ckn wani nishadi daga nan ya koma gun bakin nasa ya basu hakuri cewa amaryar tasa tana tare da baki sai zuwa dare zasu gan ta haka Suka cigaba da hirarsu.
Bash da john suna zaune a waje John ya juya ya kalli bash yace
"Aboki Mr president fah ya fada tarkon son yarinyar nan ba kadan bah"

"Me ka gani john?

"Haba ...kana ganin yanda muka samesu dazun"

"Hmmm...next tym zamu hana kowa zuwa bangaren Mr president sai da izininsa cos yanzu yana da iyali bai dace ana shiga anyhw bah"

"Yes haka zamu yi"
Daga nan sukayi shiru shi kansa bash yana mamakin kalan soyayyar kanwar tasa da Mr president hmmm...mata kenan zasu maida tsoho yaro.

Shuairat kuwa tana zaune a falo har bacci yayi awon gaba da ita se bayan azahar ta farka tayi sallah sannan ta fada wanka, wani material pitch color ta saka dinkin buba da zani ta saka danyar gwal mai kyau ta fesa turare se qamshi ke tashi. Dinning ta wuce masu aiki suna tsaye a gefe aka zuba mata rice n chicken ta fara ci a hnkli tmkar bata so sai wani yauki take. wata mata ta shigo tare da wani Dan yaro nan kuwa ta gane sultan ne nan ta sake fuska tana faraa sun karasa falon ta musu tayin abinci matar ta jawo kujera ta zauna shuairat ta rike hannun yaron tace

"Boy zo mu ci tare" ba musu sultan ya karasa gunta ta daurashi a kafa nan ta fara bashi a baki suna ci suna hira masu aiki kam se yaba halayenta suke nan da nan anty khady ma taji son shuairat ya shige ta don ba haka tayi tsammanin ganinta bah ta dauka shuairat irin matan nan ne masu girman kai da wulakanta mutane.sunyi hira sosai bayan anty khady ta damka mata amanar sultan nan kuwa ta karba ckn jin dadi Suka rabu akan anti kadi xata koma yau.

Haka shuairat ta kasance tare da sultan tana biye masa duk abunda yake so shi zatayi sunyi game sunyi kallo sunyi karatu haka Suka kasance har lokacin sallan la'asar nan ma tare sukayi sallar shuairat ta masa wanka ta canza masa kaya sannan Suka tafi bangaren momsi( Maman Mr president )

Love u alll😘😘
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*47*
By *Reefat yahya*
Chapter 20 · 0% Book details