← Book details Nida Shugaban Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 53

Sashe 14

Nida Shugaban Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"No tell me pls"
Sai kawai ta fashe da kuka nan ya jawota jikinsa ya fara rarrashinta dakyar ta bar kukan Suka xauna a kujera daya ya fara jansu da labari suna kwance a jikinsa.
Duk sanda umaima ta daga kai sai sun hada ido da bash , mr President ya kira iyayensa a waya ya hadasu sun Dade suna hira grandpa ya shaida musu yana nan tafe nan ba da dadewa bah haka Suka Dade a falon yana ta basu labarin China sosai ya cire mata radadin da take ji ya rage mata damuwanta , bash kuwa hnklinsa yayi nisa yana son ya gano matsalar umaima Amma ya kasa tuna komai.
Bayan tsawon lokaci mr President ya musu sallama ya tafi bash kuwa ya xauna yace magana xaiyi da umaima.

"Umaima ki gaya min me yake damunki"

"Babu"

"Umaima look at me"
Ta daga kanta idanunta Suka fada ckn nasa tayi saurin kawar da nata

"Umaima dama baki daukeni a bakin komai ba daz y kike boyemin damuwarki"

"Ba haka bane bash"

"No! Nagane matsayi na tnx"

Yana gama fadin haka ya tashi ya fara tafiya se kuma ta fara kuka cak! Ya tsaya ya juya yana kallonta haka nan sultan ma ita yake kallo "ya ilahi me yake damun yarinyar nan ne"
Ya taka yaxo ya sunguna a gabanta yace

"4Allah's sake umaima ya kike so a miki? Ki fadi matsalarki kin kasa fada kullum se kuka"

Tayi shiru batace komai bah
" pls ki daure ki gaya wa dad dinki tunda ni baxaki iya gayamin bah, kuma ki rage yawan tunani kar ya jawo miki prblm pls"

"Nagode" ta furta a hnkli daga nan bash ya tashi ya tafi tabi bayansa da kallo Allah Sarki bash baisan ma tana yi bah ita kanta takanyi mamakin irin son da takewa bash Wanda bata San yaushe ta fara shi bah haka nan bata San ranar dainawa bah.
Ita dai tayi imanin cewa tana sonshi Amma ko xata mutu ne baxata taba furta mishi bah, kuma bata tunanin cewa xata so wani mahaluki a duniya bayan basheer bah.maybe ita ma auren xumunci xaa mata cos ita kam basheer kawai take so a rayuwarta.

Allah Sarki umaima😥😥

Muje xuwa love u all 😘😘😘
[2/21, 2:38 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*33*
By *Reefat yahya*

Shuairat tana xaune a ofishinsu bodyguards Suka shigo Suka sanar da ita cewa mr President na bukatar ganinta ba tare da bata lokaci ba Suka fice tare.

Yana xaune a dakin hutawarsa ta shigo tare da sallama ya amsa ba tare da kalleta bah yana rike da wani Dan karamin cup black coffee ne a ciki yana sha a hnkli , waje ta samu ta xauna shiru sukayi babu Wanda yayi magana har tsawon minti 10 shuairat CE ta gaji da xaman nasu tace

"Mr president ka aika a kirani ina aiki n u din say anytin"

"My first lady yaushe xaki koyi gaisuwa ne? Ko baki iya respecting magabatanki"

Wani irin kunya ne ya lullubeta amma bata son ya gane hakan tayi gyaran murya tmkar Mara gaskiya tace

"Emm...uhmmm sorry about dat actually...

"Is ok! Neva mind , anyway na kira ne saboda ina son sanin hukuncin da kika yanke ko kuma in CE shawarar da kikayi batun maganar da mukayi som few weeks ago"

Ya tare numfashimta tare da kura mata ido

"Mr president I don't knw wat to say about it"

"Look Ayshah lokaci yana tafiya ya kamata ki fito fili ki gaya min cos my dad is on his way soon kuma xancen auren ne xe kawo shi"

Shiru sukayi kowanne da tunanin da yake yi ckn sanyin murya shuairat tace
"Mr president idan nace baxan aure ka bah wat will b d outcome"
Murmushi yayi yana girgiza kai yace

"Funny girl! Me a ciki ? Kawqi ki fito ki gayawa yan jarida da sauran jamaa cewa karya kikayi tun da can ba abunda yake tsakanin mu kinyi hakan ne....
" mr President ya xakayi da ...

Hannu ya daga mata yace
"Don't worry about me, kawai ki fito ki gaya musu gaskiyan idan xaa cireni akan mulkin ma fine I don't kia n xanyi tunani akan abunda xan sanar wa mahaifina so kada ki sa damuwa a ranki"

Ta rintse ido ya ilahi wannan wace irin jaraba CE? Shin ya xatayi? Ta amince da auren ko kuwa ? Toh idan ta fito ta fadi gskiya tabbas jamaa xasu mata kallon mutuniyar banxa daga ita har mr President yanxu me abun yi? Muryan mr President ne ya katse mata tunani

"Ayshah u don't have to worry about me"

"About u? Mr President dis is about us ya shafeni ka gane koh?
Murmushi yayi yace

"Nasan ma kina son auren kina wani nokewa pls feel free Ayshah"
Ta daga idanunta Suka fada ckn nasa ta murguda masa baki tare da cewa

"Meyasa xan so auren tsoho ? Kawai de kai kafi bukatar auren ba ni bah"
Tana gama fadin haka ta juya tabar masa falon yana murmushi shi kadai.

A waje Suka ci karo da umaima kallon kallo Suka tsaya yi daga karshe shuairat tasa kai xata wuce umaima ta fisge hannunta da karfi
"Ina xaki je munafukar karuwa kawai kin xo kin like wa mahaifina daga ganin arxiki koh"

Wani shuumin murmushi shuairat ta sakar mata tare da cewa
"Karuwancin ma iyawa ne wata idan tayi ta samu kudi wata idan tace xatayi duka xata sha"

Hannu umaima ta daga da niyyar Marin shuairat cas ta cafke hannun tana murmushi ta nunata da yatsa
" yarinya kinyi kadan wannan fuskar ba kowane mahaluki bane xe iya taba shi ba kingane koh, n don't 4get saura kankanin lokaci na xame miki uwa "

"Har abada Baxaki taba xama matsayin uwa a gareni bah"
Nan kuwa umaima ta fara hawayen jin an ambaci sunan uwa ta tuna da mahaifiyarta shuairat ta sake mata hannu ta juya xata tafi umaima ta sake Jan gyalenta da karfi ta juya suna fuskantar juna tace

"Ke umaima kike ko wa ki shiga taitayinki ni ba Saar yinki bane da mahaifinki nake dealing ba da ke ba , so ki kiyaye"
Bash ne ya hangosu ckn Sauri yaxo ya shiga tsakaninsu umaima ta fashe da kuka dai2 nan mr President ya fito don ganin meke faruwa shuairat ta juya ta kakkabe gyalen ta fara tafiya sai kuma ta juya ckn gadara tace

"Mr president I tink ya'r ka bata da tarbiya yana da kyau ka sanar da ita cewa aurenmu yana nan xuwa bada dadewa bah xan dawo gidan nan da xama she shul learn how to respect me "

Mr President da bash baki Suka bude suna kallon shuairat wacce ta wuce direct gun mota aka bude mata ta shiga umaima kuwa ta fashe da sabon kukan bakin ciki dad nata ya juya xai mata magana ta daga masa hannu alamar cewa bata bukatar jin komi daga garesa , wani dogon numfashi yaja sun hada ido da bash ya masa nuni da ido akan yaje ya mata magana hakan kuwa akayi umaima ta koma bangarenta bash yabi ta baya.

😘😘😘lov u all
[2/21, 2:38 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*34*
By *Reefat yahya*

Ta xauna dirshan a kasa wani irin bakin ciki take ji bash ne ya shigo yana mata murmushi ta kawar da fuskarta gefe handkerchief ya fara mika mata ta karba ta share hawayen sannan ya tashi ya bude fridge ya dauko mata ruwa mai sanyi nan ma batayi gardama ba ta karbi goran ta shanye tana sauke numfashi a hnkli nan kuwa taji hnklinta ya kwanta

"Umaima kiyi hakuri I know hw u feel"

"Hakurin me xanyi basheer? Nasan laifi na ne ni nafara nemanta da fada but...
Kuka ta fara yi bash ya cije lebe yana tunani halinsu iri daya da shuairat se saurin hawaye ga Neman magana koda yake mata ma dukkansu suna son kuka

"Bash baxan jure ganin dad da wata bah a matsayin matar da xai aura, it always reminds me of my mom"

"But umaima ya xakiyi? Allah ne ya kaddara hakan y not kiyi hakuri ki xuba musu ido"

"But na kasa bash! I can't baxan jure ganinsu bah wai ma dad har soyayya yake da wannan yarinyar?

"Umaima...
"No bash! Kasan me yake bata min rai? Tun ynxu fah idan ta fadi Abu dad baya tsallakewa idan sunyi aure fah?

"Umaima don't worry kiyi hakuri komi xai daidaita , nide ki rage yawan fushin da kike yi pls kuma ki daina disrespecting din dad naki pls"

"Ok "
"Pls promise me dat baxaki kara fushi da dad bah"

"Ok I promise"
"_gud girl daz y I like u"

Murmushi take ita kadai tasan abunda take ji, haka bash ya xauna yana debe mata kewa daga karshe ya mata sallama ya tafi.waya ta cire ta kira wata yar mamanta bayan sun gaisa take shaida mata cewa dad nasu xeyi aure haka anty kadi ta bata hakuri akan cewa ta kwantar da hnklinta dama dole wata ran xeyi aure ko ba ynxu ba.

***********

Shuairat CE tare da shukrah suna xaune suna hira a falon shukrah ya shigo tare da sallama shukrah ta karbe jakan hannunsa shuairat ma ta masa sannu da dawowa yace

"Baby I don't like wat u did today"

"Yaya ba laifina bane"
"I know but da kin kyaleta kawai"

"Haba yaya ya xaayi...
"Baby kada ki manta aure xakiyi ki koma a gidan bai dace Ku fara samun matsala tun ynxu bah"

"Yaya kasan baxan taba barinta ta mare ni ba koh"

"Yes na sani kuma ki rage nuna gadara da iko a gaban mr President he deserve som respect , duk da bansan limit na soyayyarku bah"
Shiru sukayi suna kallon kallo shukrah CE ta fito daga ckn daki tana kallon halin da suke ciki tace

"Lfy? Meke faruwa?
"Ba komai bash ya bata amsa sannan ya tashi tayi shigewarsa daki ya barsu ta juya gun shuairat tace

"Bestie menene?
Chapter 14 · 0% Book details