← Book details Nida Shugaban Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 53

Sashe 48

Nida Shugaban Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Haba kinfi kowa sanin irin son da uncle bash yake min..ni nasan ba lfy bah...
"Dallah malama..ki ci abinci ki tashi ki shirya"
Tana kumbure2* haka tasha farfesun don bata ga alamar wasa a fuskar shuairat.
Bayan ta gama ta shiga bayi ta Dade kwance ckn jacuzzi tana lumshe idanunta hoton fuskan bash kawai take gani nan hawaye ya cika mata ido ta dauki tsawon minti 40 tana kwance , shuairat ce ta kira sunanta daga waje nan ta fara wanka daga bisani ta fito.
3:10pm an shiryata tayi kyau sosai ckn wasu dankareren leshi mai kyawun gaske umaima tayi kyau kamar a saceta a gudu a harabar gidan aka fito da ita masu daukar hotuna ne birjik ga nan yan uwa da abokan arxiki ma ga yan gayyan sodi irinsu Reefat😆😆 ga masu watsa labarai daga gidan telebijin da yan jarida , gidan de a cike makil da jamaa umaima de daurewa take tana kokarin boye halin da take cki shuairat ansha kyau ta xama tauraruwa sha kallo ga salman da sultan ma haka, abun de gwanin burgewa.
Momsi ta fito Suka fara daukar hotuna sunyi family pix kala2* dakyar na samu na dau kala 3nida shuairat da amarya se kuma Wanda mukayi tare da salman da sultan😜😜😜.
Horn muka ji a bakin gate take maigadi ya wangale kofar motoci ne birjik har na kasa tantance ko guda nawa ne, securities na fara gani ckn bakaken suits nace ah abun na manya ne☹☹..Nigerian president ne a gefen mr president (dad) ga Chinese President daga barin hagu se kuma new faces da bansan ko su wanene bah daga gani dai kasan shuwagabannin kasacen duniya ne don daga irin shigar kayansu da masu tsaron dake xagaye dasu xaka gane hakan.ga can daddy a baya tare da abokanansa manyan mutane se kuma ismaeel na hNgo fuskarsa dauke da murmushi sai kuma bash daga can gefe yana ta gaisawa da mutane yNa dariya fuskarsa kamar gonar audugA..haaa..am confused🙄🙄 ya naga bash haka?? ..uhmmm.
Dakyar mr president tare da tawagarsa Suka samu hanyar shiga ckn gidan saboda jamaa sunyi yawa babu masaka tsinke. A can babban falon gidan Suka xauna daddy kuma yana dayan falon tare da tawagarsa , abinci da na sha aka ajiye musu suna ci suna taba hira ana dariya daga bisani yan jarida Suka fara daukan hotuna don yadawa a gidan labarai, shuairat da umaima sun shigo falon anyi hotunan tare dasu ana tayasu murna.har 5pm ana abu guda dakyar shuairat ta jawo umaima Suka koma bangarensu a daki Suka xauna shuairat tace
"Ki shirya anjima xaa ne dinner"
Idanunta sun cika da kwalla tace
"Allah na gaji baxan iya xuwa bah"
"Shikenan bari naje na sanar da dad "
Ckn Sauri tace

"Ah'ah pls kiyi hkri xan shirya ynxu"
Murmushi shuairat tayi sannan tace
"Kije falona babu kowa a can angon yana son ganin ki"
"Eyya mom..Allah na gaji sosai"
"Ok bari na kirashi yaxo ya sameki "
Bata jira amsa bah tayi waje dama su 2 ne kawai a ckn dakin sauran jama'an suna can kasa suna faman daukan hotuna. Umaima ta hada kanta da guiwa ta fara rusa kuka..shikenan yau ta xama matar wani !
Kofar dakin aka bude ta cigaba da kukan da take ba tare da ta daga kai bah..a hnkli ya xauna kusa da ita ya jawota a jikinsa , qamshin turaren da har abada baxata manta dashi bah ckn Sauri ta daga ido tare da cewa
"Uncle bash😳😳
Murmushi ya sakar mata mai sanyaya xuciya , nan kuwa ta turesa gefe tana hawaye tace

"Kasan de ynxu na xama matar wani"
"Har abada Ke matata CE mutuwa CE xata rabamu"
Wani murmushi mai ciwo tayi tana girgixa kai tare da cewa
"Kana magana tmkar baka San yau an daura aurena bah"
"Yes ofcoz an daura auren ki but da masoyinki aka daura auren"
Ya karasa magana tare da lakuce masa hanci ckn rashin fahimta tace

"Bangane bah"
"Yes umaima Allah ya cika mana burin mu an daura mana aure n...
Bai samu damar karasa maganar ba ta fada jikinsa ta rungumesa gam hawaye wani na bin wani..murmushi bash yayi tare da daura hannayensa shima ya rungumeta 😍😍😍
Sun kasance ckn wannan hali har na lokaci mai tsaho sannan umaima ta xame jikinta sai kuma kunya ya kamata tasa tafin hannu ta rufe fuska wai ita kunya🙄🙄🙄 daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa...😬😬😜.

Toh ya akayi abun ya juya aka daura da basheer???
🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
Fans ..just ignore d typing errors cos bana editin
[2/21, 2:42 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*95*
By *Reefat yahya*

Fuskokin nasu dauke da Murmushi suna kallon juna ..a hnkli bash ya jawota ya rike mata hannu tare da kura mata ido yace
"Baby no more kunya pls..kin xama matata u r mine n am urs murna xakiyi ki godewa Allah da ya cika mana burin mu"
ta daga kai tace
" but Bb ya akayi hakan ta faru har daddy ya amince aka daura mana aure"
"Ni zan baki amsa"
Shuairat ce ta shigo fuskarta dauke da murmushi ta cigaba da cewa
"Yau da safe na samu labarin but naki na gaya miki cos I want 2 surprise u"
Nan kuwa umaima ta ruga a guje ta rungumi shuairat tana dariya tace
"Tnk u so much mom..nasan da taimakon ki akayi wannan auren Nagode sosai Allah ne kadai zai biyaki tnx a lot"
"Mention not dia "
"Toh mom ki ban labarin ya akayi ..am waiting"
"Umaima hoo..irin xumudi haka"
Kunyace ya rufe ta nan ta koma gefen gado ta xauna bash kam se kallonta yake kamar wani tsohon maye ta birkita masa kwakwalwa ta kara kyau ba kadan bah..shuairat CE ta fara magana
"Jiya daddy yaje gun baba tare da dad naki sun dade suna hira har daddy xai dawo sai yake tambayan ina yaya don tunda yaxo be ganshi bah, aka ce masa yaya bashi da lfy yana bacci daga nan Suka dawo gida.yau da safe naje gun daddy bayan mun gaisa yake tmbyta ya me jiki ckn rashin fahimta nace masa waye ba lfy? Ckn mmki shima yace baki san yynki bashi da lfy bah? Nan hawaye ya cika idanu na hnklin daddy ya tashi ya fara bani hkri yace da yasan baa gayamin da baxai tmbyeni ba gashi ya dga min hnkli, nace masa ba batun rashin lfyn ne Ke sani kuka bah illa tausayin halin da yaya xai shiga nan gaba..daga nan na xayyana masa komai.fada yake ta inda yake shiga ba ta nan yake fita bah wai akan wane dalili xaa boye masa wannan lamarin, nace tun farko naso sanar da kai but baka saurareni bah daga nan ya kira baba nan ma fada yake akan cewa meyasa baba be sanar dashi bah.a takaice de haka ya kira ismaeel da babansa ya basu hakuri ya nuna musu yarinya bata so , haka Suka hakura har xuwa lokaci daurin auren ko shi yaya bai San cewa dashi xaa daura auren bah.toh kinji de yanda abun ya faru"

Wani dogon numfashi umaima ta sauke tare da cewa
"Ikon Allah kenan..tabbas wani baya auren matan wani, matar mutum kabarinsa hakika rabo in ya rantse babu mai hanawa don nikam tuni na fidda ran sake haduwa da Bb..Allah Nagode maka da ka cika min burina , mom Nagode miki da kokarin da kikayi kuma daddy ma dole na gode masa"
"Kai umaima ko Ya'r kunyan nan babu"
ta rufe fuska tana dariya shuairat ta tashi tsaye tare da cewa
"Ki shirya ynxu masu makeup suna nan tafe kinsan akwai dinner nima na tafi idan nayi sallah xan fara shiri na"
Basheer yayi murmushi yace

"Wait..sisy kina nufin kema xaki he?bayan kece mmn amarya"
Harara ta watsa masa tace
"Toh bari kaji har mijina ma sai yaje don abun tuwo na maina ne ...kuma a ckn gidan nan xaayi"
ta juya gun umaima tace
"Ke kuma ki xauna ki biye masa har lokaci ya kure Ku gaku nan romeo n Juliet , an de daura auren xamu gani ko xaku hadiye junanku"
Dariya sosai suke shuairat ta yi hanyar kofa bash yayi saurin cewa
"Kixo gidan mu ki ga yanda xaa hadiye juna ...ki xo na koya miki Lov yarinya"
"Ahaaff...wllhi karyan mutum yace xai koya min soyayya , duk kalan Lov da xakuyi de wasu sun Riga sun gama ..toh wai ma wane darene jemage bai gani bah"
"Daren goma sha hudu"
Ya fada yana dariya tsaki shuairat ta ja ta bar dakin umaima ta hararesa ckn salon so tace
"Mom ce fah..she is ur in law u have 2 learn hw to respect her"
"Lol..babu mai shiga tsakanina da baby so ki xuba mana ido kawai"
"Ni baby ! Ita baby! So which 1...gskiya ka xabi daya"
😳😳😳😳☹☹uhmm ni Reefat nace toh fah...umaima tun ynxu🙄🙄🙄🙄Dakyar bash ya fita ya barta ba don yana so bah nan ta fada wanka.
Chapter 48 · 0% Book details