← Book details Ni Da Misbah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 10

Sashe 9

Ni Da Misbah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*NIDAI MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 TATTARA Y'AN KAFAFUNA NAYI NAYO WAJE, DAGANAN KUMA NA AJE WAYATA DAN NA HUTA 🤣........ WANNAN KARON FANSSS NABAKU DAMAR D'AUKO WANNAN RAHOTON MUSAMMAN NIDA MISBAH FANSSS GROUP WANNAN NAKUNE......NIDAI NAYI GABA ZAN HUTA.............*

_WANNNAN PAGE D'IN NAMUKU DOGO SOSAI DAN HAKA BAGA COMMENT SOSAI AKANSHI, NICE DAI TAKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚_

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

Or 07031012948

*NI DA MISBAH*
_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya Writers)*

" *We Rule the World of Writing* "

https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK (24), NI DA MISBAH •LOVE STORY• FREE BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *NI DA MISBAH*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*AUGUST %8%*

*Tuesday 15/8/2023 August*

_page 91 to 100_

*Finally Page in Sha Allah*

```Note📝 Wannan littafin Yana d'auke da darasi, kada ka walak'antata Wanda Yake sonka domin idan soyayya tayi yawa takan iya rik'id'a tadawo k'iyayya, Haka Idan k'iyayya Tayi yawa takan iya rik'id'a tadawo soyayya maizafi, to Shawarata Anan kada ka zurfafa k'iyayya tsana ga kowama domin bakasan meye Agaba ba Wanda Allah ya tsara, Sai Kama mutunci Y'ar Uwa duk wuya duk rintsi kada ki sallama mutuncinki ga kowa duk dad'in bakin Namiji kada ki Yarda domin tabo kawai yake son barmiki ya gudu Wllh, A Koda yaushe ki kasance Mai kame Kai da d'abi'ar kirki, kada kibiyewa rud'in duniya da shairin K'awayen banza,, Saikai Wanda b'acewar basira zata Aura kace sai wayayyar macce, ko kice Sai wayayyan Namiji, duk Abunda zaka Samu A dubiya Indai Mai k'yalli ne to Wllh daga baya saiya ya kasance Annoba gareka, duk Abu Mai Kyau indai ba kyan Hali bane to saiya kasance da matsala, KUDAINA MUDAINA Wannan b'acewar basira tacewa sai Macce wayayya ko Namiji wayayye domin mun kauce tsarin Addini Tinda kuwa Aka kauce Fad'ar Allah tofa ba Wanda zaiga daidai, Macce Mai Addini, tafi Haka Namiji Mai Addini yafi gwanda ki zab'e Wanda zaizama WANI HASKE A Rayuwar ki kaima A rayuwar ka,, sai maganar iyaye dama Wanda yak'iji bazai k'i Gani ba, Allah yabamu ikon yiwa iyayenmu biyayya Koda yaushe, Ameen Ameen..... Allah kaimuna Sassaucin rayuwar 🤲 tsadar Nan damuke ciki, Allah kabamu lafiya da Zama lafiya, Allah kaimuna Afuwa rangwame dama Sassauci🤲 Allah kasa mucika da imani, Allah kabiya muna buk'atunmu na Alkhairy, Allah ka tsaremu daga Mugunji dama mugun gani, Allah ka k'aramin baiwar wannan rubutun nawa, Allah kaban lafiyar Ido, Allah ka k'aramin masoya Allah ka nisantani da mak'iya,, Allah ka had'amu da maza nagari duk inda Suke, Allah kabamu maza nagari kamilallu Ameen,, Ina Gdy 🙏 duk Inda kuke Masoyana, Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 takuce har ko yaushe....```

..... Sosai take kuka Domin taji Azaba ba kad'an ba Bak'in cikinta ma baya Sonta shiyasa ya Mata Wannan k'etar,
Zancen Zuciyarta Yafito fili,

Hannu yasa Yana share Mata Hawaye Ahankali yace"Koda bansoki daba yanzu Ina sonki Domin kincancanci na soki my Soulmate,"

D'aga jajayen idanuwanta Tayi ta watsa masa wani kallo Kafin ta kwance jikinta daga nasa, da kyar tamik'e tashige Toilet tarufe,

Ajiyar Zuciya ya sauke Kafin shima yabar d'akin,

Wanka tayi bayan tagasa jikinta tafito Riga da Zane tasa kwantawa tayi Saboda zazzabi daya rufeta nantake,

Bayan yagama wanka da Shirin sa Yafito Domin duk Hankalinsa Yana gurin Amna, har zaiwuce saiya dawo d'akin Jasra ya nufa Abun mamaki still rufe yake, Hakan yanuna Bata Kwana gida ba, to Ina taje takwana? Kasa samun Ansa yayi, Zuciyarsa tabashi Shawarar zuwa gidansu yagani, domin shi yanzu zarginta yake Sosai,

Ficewa yayi da sauri yashiga motarsa yafice,

Jin fitarshi gidan yasa ta rushe da kuka wato yacinma burinsa Shine Kuma zaifita ya barta cikin halin Rashin Lafiya,

Hajiyar sama da Aira ne suka shigo gidan sunata sallama shuru, Hakan Yasa Aira tashiga bedroom d'inta, kwance ta hangeta sai faman rawar d'ari take, da sauri ta k'arsa Inda take Tana Fad'in"Subhanallah Aunty Amna Bakida Lafiya Ina ya MISBAH,"?

Sam takasa magana Saboda zazzab'in ya mata yawa,

Fitowa Aira tayi Cikin damuwa tace"Hajiya Batada lafiya fa kwance take mukaita Asibiti"

Kamata sukayi suka Shiga mota suka wuce Asibiti, Suna zuwa Aka K'arb'e ta,

Bayan gwaje gwajen likitan tafito,
Office d'inta suka zauna,

"Tanada miji ne,"?

"Eh likita"

"Zanso Ganin mijin nata"

"Kinga yarinya muda muka kawota mukeda Y'ancin sanin meke damunta ki fad'a muna," Cewar Hajiyar sama cikin d'aure fuska

Sanin rigimarta yasa tayi murmushi kawai Tace"Bawata babbar matsala bace kawai Dan An shigeta da k'arfi Kuma Bata Saba ba yasa Wannan zazzab'in Kuma Akwai Alamar tana tunani Wanda yanzu Haka jininta yayi k'asa sosai Gaskiya, tana buk'atar kulawa da kwanciyar Hankali, ga Wad'annan magungunnan kusiya Mata"

Aira Tace"yanzu zamu iya ganinta"?

"Eh sosai dama ta farka zaku iya tafiya domin ciwon bawani babba bane Kawai kulawa da hutu take buk'ata,"

"To mungode"

Hajiyar sama tacika Tayi famm da MISBAH,

Har Aka sallamesu ba labarin MISBAH hakan ya k'ara tinzirani Hajiya, Koda suka Koma gida Inda Hajiya ta zauna sosai take samun kulawa ta ko wanne b'angaren Hajiya kuwa Kullum Cikin surfa masifa take, "Yazo ya gama gantalewa da wannan tsohuwar guzumar Matar tasa yasa keki Dan Ina k'aunar ki,"

Amna kuwa batason zancen saki domin tana son mijinta saidai tanajin Ciwon Rashin kulawar tasa,

MISBAH kuwa, Sanda ya isa gidansu tamkar gaidasu Yazo, Yasha mamakin Rashin Samunta gidan, har Abban ta yake "fad'an Wai ya rik'e musu Y'a tin Auren su basu sake ganinta ba,"
Hak'uri Kawai yabasu Yafito, wayoyinta Kuma Duka kashe, Duk inda yake Saran ganin ta ya duba Amma bata,

K'arin tashin Hankalinsa Koda ya dawo gida ba Amna, ba Inda Bai Duba ba cikin gidan Amma bata,

Kiran Aira yayi ya tanbayeta ko Amna tazo gida saidai Aira Tace A'a domin Hajiyar sama tayi gargad'in kowa Kada Yace tana gidan,

Duk inda Hankalin sa yake ya gama tashi, domin ba inda Bai dubata Amma Bata, ga wayarta a gida,.

Komai nasa ya tsaya gashi indai zaiyi waya da Hajiyar sama to zaisha fad'a, hakan Yasa yake tsoron zuwa gidan, Umma kuwa tace duk Inda yasan Amna take yanemota in bahaka ba zata Mugun sab'amasa,

Bayan sati d'aya Yana Zaune komai ya Masa zafi, kwatsam saiga Jasra tashigo Cikin shigar k'ananan Kaya Riga da wando Sunyi matik'ar kamata,

"Ke daga gidan ubanwa kike sati d'aya Baki gida? Kuma kalli shigarki kamar karuwa daga gidan ubanwa kikafito nace,"? Cikin tsawa ya Ida maganar

Duk yawani firgice Mata tsorata da yanayinsa tayi cikin Ina ina tace"Dama naje gida ne,"

"K'arya kike naje har gidan Amma bakinan, fad'amun daga Ina kike,"?

"Kai dalla sauraramin kasani gaba kamar ubana to Ina Ruwanka da Inda naje,"?

"Ni kike fad'awa Hakan ,"

"Eh Anfad'a d'in Kai Waye da baza'a fad'ama ba,"

Belt d'in jikinsa ya ciro tana ganin hakan taruga d'aki ta rufe,

Nan ya k'arace masifarsa Sannan ya wuce,

Gurin Samir Yaje ya fito Suna magana A motarsa,

"Abokina naga kayi Rama Sosai duk yanayinka ya sauya lafiya kuwa,"

"Ina Lafiya Samir dama haka Auren wayayyar Macce yake,? Nikam nayi Dana sanin Aikata Babban kuskure Irin Wannan Kai in shourt Ni zargintama nake Kan tana ma'amala da mazan banza waje, d'ayan gefe kuma gashi Inason kasan cewa da Amna Amma narasa inda take,'"

"Dama ai Wanda Yak'iji bazai k'i Gani ba, ba Irin Shawarar da bamu bakaba Kan wannan k'od'ad'd'iyar Amma kak'i ji, kuma Yanzu inada Yak'inin son Amna kake,"

"Nifa nafara gasgata hakan Amma bansan ta inda Zan Fara ba,"

"Kasan me? Tananan tare da Hajiya in Sha Allah domin da Bata gidan da bazasu share kaba,"

"Kuma fa kanada Gaskiya, yanzu muwuce gidan kawai,"

Tada motar yayi suka nufe gidan

Tana zaune palourn Hajiyar sama tana Gyaran farce, kamar daga sama taji K'amshin turaren Yaya MISBAH,
Bata gama gasgatawa ba kawai saigashi kamar Anjehoshi Ya K'araso gabanta ya duk'a Yana Fad'in"Haba Amna Ya zakimin Haka kinata wahalar Dani kema na Zama Kamar wani mahaukaci ko Ina sai nemanki nake Ashe kina Nan Abun ki, Meyasa Zaki min haka,"

Itadai kallonsa Kawai take, yayi Rama harda Bak'i, duk ya sauya gani k'asumba daya Tara,

"Kimin magana ma My Amna kin zuba min Ido kawai kamar Baki sanni ba,"Ya K'arasa maganar Yana matsa hannunta,

Maimaita sunan kawai take A ranta my Amna, taji dad'in sunan Amma Bata Nuna masa ba,

Fisge hannunta tayi tana Ya mutsa fuska tace"mlm lafiya kazo kawonin takar da tane,"?

"Takarda tame kuma,"

"Tasaki Uku ringis zaka bata tagama idda tasamu Mai Sonta ya Aure ta, indai kasan baka kawo sakin ba to ka koma idan ka kawo saika dawo," Cewar Hajiyar sama dake shigowa palourn

"Saki kuma Hajiya,"? ya fad'a yana rawar baki

"Sosai Abunda kaji shina fad'a dole kasaki Amna ta Aure wani,"

Kalmar ta Aure wani tafi komai d'aga Masa Hankali,

Cikin wani irin Yanayi Yace"wllh Koda sama zata had'e da k'asa bazan tab'a sakin Amna ba Domin Ina son matata wllh,"

"K'arya kake da kana Sonta bazaka Mata Wannan walak'ancin ba, Kuma ma kamanta Nan Agabanmu kake Fad'in baka sonta, Kai MISBAH dole saika sake Amna fa,"
Chapter 9 · 0% Book details