← Book details Ni Da Misbah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 10

Sashe 7

Ni Da Misbah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *NI DA MISBAH*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*AUGUST %8%*

_Sunday 13/8/2023 August_

*Page 61 to 70*

......"Kamar yarda kuka son Y'ar ku kuma kuke son farincikin ta Haka muma mukeson namu, to Atak'aice dai su biyu zai Aura da Y'ar Uwarsa," Cewar Hajiyar sama

Cike da mamaki Abban JASRA Yace"Amma Meyasa kuka b'oye hakan tinin sai Yanzu Dan ku kunyatar Damu yasa kuka tsara hakan,"?

"A'a Alhaji bako d'aya dama Itace Wadda zai Aura tin farko sai Kuma K'addara takawo Y'ar ku, to wannan ba wani Abu bane yin Allah ne kada kaja da Hukuncin Allah,"

Hunmmm"Shikenan Allah Yasa hakan shine Mafi Alkairi"

"Ameen Ameen, Yanzu mukoma can A d'aura dama fara fad'a maka mukayi,"

Bayan Ankammala sallah Aka tsaida mutane

Duk da naso shiga Amma hakan ta faskara,

Can najiyo Mai shela Yana Fad'in"Aure ya d'auru tsakanin MISBAH Hussain da Amna Hassan Akan sadaki dubu 50,0000

Saikuma nagaba MISBAH Hussain da Amaryar Jasra Usman Akan sadaki dubu 50,0000

Tinda Yaji karad'in Fad'in Wai And'aura masa Aure da Amna Yaji komai nasa Ya tsaya cak, bazai iya Fad'ar wane Hali ya tsance kansa ba, duk murnar da Ake tayashi kallon mutane kawai yake, Samir ne Yajashi zuwa gida Domin Daddy Yace Yana son ganinsu palourn Hajiyar sama,

Sosai tasha kuka cikin band'akin sannan tafito ta goge Fuskarta, Jasra tazo"kuka kika kulle kanki kinayi ba? Hunmmm to kukan ya k'are daga yau, zo muje kiji wani Abu Amma dole kimin babbar kyauta,"

Batace ma komai ba Dan ita kawai tasan wane Hali take ciki, Jan hannunta tayi zuwa palourn Hajiyar sama, duk sun taru kowa ya zauna Suma suna zuwa suka Sami guri Suka zauna,

Hajiyar sama tayi Gyaran murya tace"MISBAH kayi Abunda kake so A matsayin ka na d'anmu Kuma munbarka bawai Dan kafi k'arfin mu ba a'a Dan kawai mubaka naka hakkene, to muma munada ikon zartar da Hukunci Akanka hakan yasa Muka d'aura maka Aure da Amna wadda itace Akafara d'aurawa da ita kenan Itace Uwargida, wllh MISBAH idan har kace zakak'i wannan zab'in namu to Ina fad'a maka zakayi mamakin Ni matakin da Zan d'auka kanka,"

Tinda Hajiyar sama tafara magana Amna ta kafeta da ido idan ta fahimta daidai yau su biyu Aka d'aurawa Auren kenan kuma da MISBAH me zatayi farinciki ko me,"?

MISBAH kuwa b'acin Rai ke Damunsa zuciyarsa sai Azazzalarsa take, Wai shi Za'a ma Auren dole Kamar shi MISBAH kuma A rasa dawa Za'a had'a shi sai wadda ya tsana sama da komai, lalle Dole ya d'auke Babban mataki kanta tinda tayi wannan Babban kuskuren, tinaninsa Ya tsaya ne dayaji muryar Umma tana Magana,

"Bazan lallashekaba Son Domin Kai ba Yaro bane, Saidai na gargad'eka da babbar murya, ko bayan raina Inka rabu da Amna to Allah ya is ban yafe maka ba," tana gama maganar tabar wurin,

Haka duk Suka watse Abba ne kawai yake lallashinsa

K'aton gidansa daya Gina Aka Kai Amaren Duka can gate d'aya ne saidai part 2 ne Amma palourn d'aya ne babba wadda Za'a rik'a had'uwa Don cin Abincinsu ko fira, shi Koda ya Gina wannan gidan Dan macce d'aya yayi shi part 2 d'inda yayi nufinsa d'aya na matarsa d'aya nasa Koda zaiyi Bak'i basai zunzo part d'in matarsa ba,

Gidan ya had'u Sosai Kuma ko wacce iyayenta sunsamata kaya bama kamar Amna domin su Hajiyar sama sunkashe naira Sosai,

Bakowa d'akin itace kawai, zaune Kan gado ta rafka uban tagumi

Yau dai gashi Allah ya nufa gata gidan Ya MISBAH A matsayin mata Saidai bola ma tafita Mahimmanci domin tanada Yak'inin ko kallon banza taba isheshi ba balantana Yazo dubata A matsayin Mata, Hawaye tashare ganin zaman dama tinanin ba Abunda zai Amfane ta yasa ta mik'e ta Shiga bathroom ta d'auro Alwala bayan tarage kayan jikinta, tayi sallah sannan tajima tana Rik'on Allah mafita Kan Lamarin sannan tarufe d'akin ta kwanta Abunta cike da tunanuka kala kala bacci ya d'auke ta,,

"Kaga Samir bana buk'atar rakiyar a
Kowa Aiba Auren so bane, Kuma banason Shawara Indai kan Yarinyar Nan ne so Ajiyeni Anan kayi tafiyar ka nagode,"

Tsayawa yayi ya sauka yashige gidansa direct d'akinsa Yawuce Dan Yarda yakejin b'acin Rai bayajin ko Jasra zai iya gani yau, Yana Shiga d'akin sa yasa key ya fad'a bathroom ya sakarwa kansa shower ruwa na sauka kansa Wai ko yaji sauk'in b'acin Ransa, Yajima Sannan ya fito yayi sallah yayi kwanciyar sa,

Jasra kuwa tacika tayi fam domin taga shigowarshi Atinaninta d'akin Amna Yawuce, sai faman masifa take ita kad'ai,

"Wannan ai Iskanci ne, Ya yaudare ni ya Aureta cikin munafunci Kuma shine Yaje d'akin ta ya kwana Dan iskanci ko shigowa inda take baiyi ba ai wllh zai gane dashi har ita zasu gane ko ita wacece," saida tagama fad'an ta sannan tayi kwanciyar ta sallar ma batayi ba............

_TO KOWA DA KOWA DAI NI MATAR MLM INACE MUKU ASSUBAH TAGARI_

_BASEEERATA ITACE😍_

WhatsApp number 07064904617 or 07031012948

*NI DA MISBAH*
_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya Writers)*

" *We Rule the World of Writing* "

https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK (24), NI DA MISBAH •LOVE STORY• FREE BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *NI DA MISBAH*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*AUGUST %8%*

*Page 71 to 80*

..........Tasaba da tashi da Assubah Wannan karon ma Kiran farko ya tasheta Sallah tayi tazauna tafara karanta Qur'ani

Da ciwon Kai yatashi Saboda sakarwa kansa Ruwan da yayi, Kamar yatafi yarsa batare da ya tashesu ba kuma saiya tuna Yanzu hakkensu na kanshi Kuma Wannan b'angaren Addini ne, hakan Yasa Yanufe d'akin ta nocking Yayi tareda murd'a Handle k'ofar Yabud'e Kai tsaye Yashiga da sallama Kamar Wanda Akama dole, Abun mamaki saiya ganta zaune Kan sallaya kana karatun Qur'ani d'an k'ura mata ido yayi ta burgeshi Dan koba komai Bata Wasa da ibada,

D'agowa tayi tareda Ansa sallamar, "Barka da safiya Ya MISBAH"

Had'e fuska yayi kamar baitab'a dariya ba Yace"rik'e gaisuwar ki Sarkin naci bana buk'ata Wai Macce ke nacema Namiji Dan Rashin kunyawa, Kafin nadawo sallah ki tabbata kin had'a muna Abin Kari nida matata kinsan ita Matar so CE shiyasa bazan Bari ta wahala ba," Yana Gama maganar Yawuce Ransa Fess koba komai yasan ya b'ata Mata rai

Sosai kalamansa Suka Mata zafi Dan har kuka Saida tayi, ba Yarda ta iya dole tashiga kitchen tafara dafa Abun Kari d'in,

D'akin Jasra yashiga kwance take tanata sharb'ar bacci Abunta, daga ita sai wata fitinanniyar riga wadda ita da Babu dik d'aya,

D'auke kansa yayi Haka Kawai yaji haushin ta Ace lokacin sallah Amma mutum na bacci,

K'arasawa bakin gadon yayi, k'afar ta yadaka Yana Fad'in"kitashi kiyi sallah"

Mik'ewa zaune tayi cikin takaicin tashinta da yayi tace"Oh Oh Wai bakasan Mahimmancin bacci tare da d'an Adam bane kazo kadameni Wai Ina Ruwanka tinda bakai zanyiwa sallar, haba karabu dani mana," tana gama maganar tasake komawa ta kwanta Had'id'a Jan blanket d'in tarufe jikinta duka,

Mamaki yasashi yayi wani sororo Wai shi macce zatasa gaba da fad'a Dan Yace tayi sallah, ganin Lokaci zai k'ure yasa yabar d'akin

Kusan 8:30 Yadawo gidan Dan bayan Yadawo sallah kayan sports d'in sa yasa Yawuce gudu Dan motsa jiki,

D'akin ta yakoma Abun mamaki har lokacin baccinta kawai take batayi sallah ba,

Cikin hasala ya d'auko ruwan sanyi Ya watsa mata A fuska,

Aikuwa A firgice ta mik'e zaune, zuba masa Ido tayi ganinsa gabanta ya d'aure fuska Yace"Zaki tashi kiyi sallah d'in ne ko saina b'allaki,"? Cikin tsare gida yayi maganar hakan Yasa ta mik'e tana gunguni tashiga bathrooms

Girgiza Kansa kawai Yayi yakoma nasa d'akin Saida kwanciyar sa yayi sai kusan 12:00 ya falka da yunwa sosai hakan Yasa Yafito parlon ba Shiri dagashi sai three-quarter palourn yazo inda darning Nan ya tarar da Jasra tana cikin Abincinta, Zama yayi yasoma bud'e kulolin b'ata fuska yayi ganin Tinna safe ne,

Cikin d'aga murya Yace"Amna! Amna!! Amna!!!"

Fitowar ta bathroom kenan taji Kiran nasa saida cikinta Ya juya Sam Tama manta iya towel ne Kawai jikinta Yasa tafito hakan da sauri har Tana Neman kifewa k'asa Danta tsorata da Kiran nasa,

"Gani Ya MISBAH lafiya"?

Tafad'a cikin rawar jiki dama can ita bamai son tsawa bace, sai duk tarikice,

Zuba Mata ido yayi tindaga sama har k'asa yake kallonta Sam Yakasa yimata masifa wannan shine karo na farko daya tab'a ganinta ba hijab, duk ya shagala da kallonta,

Jasra kuwa tamkar zatayi bindiga tsabar haushi, tinda yazo gurin ko kallon kirki baimata ba Amma Wannan munafukar tana zuwa shine Duka Hankalinsa yakoma gareta,

Itakuwa ganin irin kallonda yake binta dashi yasa tadube jikinta ganin Yarda take yasa tasa K'ara tsabar tsorata saita fad'a jikinsa tana Jan rigar jikinsa Wai takare jikinta da ita,

Jinta cikin jikinsa Yasa komai nasa ya tsaya ko motsi ya kasa yi

Jasra kuwa tamkar zata mutu tsabar Bak'in ciki. ............

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

*NI DA MISBAH*
_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._
Chapter 7 · 0% Book details