← Book details Ni Da Misbah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 10

Sashe 10

Ni Da Misbah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gurin Amna Yanufa Yana rik'e hannayenta duka cikin rawar murya Yace,"ki fad'a Mata kinason cigaba da Zama da mijinki, Amna wllh Ina sonki bansan cewa Ina sonki ba Saida kikayi nisa dani Dan Allah ku janye kalmar saki wllh idan bake Amna mutuwa zanyi,"

Cikin k'arfin hali ta kwace hannunta cikin kuka tace"Ba Gaskiya kake fad'amun ba Ya MISBAH kasha fad'amun baka sona Kuma bazaka tab'a sona ba nasan dalilinka Nadawo yanzu kace kana sona, Ni kuma A Yanzu bana sonka bana sonka!!!!," Da gudu tabar wurin,

K'afafunsa Suka soma rawa take suka kasa d'aukar sa fad'uwa k'asa Zaune Yayi komai ya tsaya Masa cak yaji zafin kalmar Bata sonshi data fad'a mishi kallamar gwanda ta yanke Naman jikinsa, dama Haka kaso ba'a sonka yake?

Tsaki Kawai Hajiya taja tabar palourn,

Da taimakon Samir ya mik'e gida ya maida shi,

Wata d'aya Yana zarya gidan Amma Yanzu ko Ganin Amna yadaina duk ya rame yayi Bak'i kuma yayi Dana sanin Abunda yamata Abaya,

Wayarsa ce keta ringing Kamar bazai d'auka ba kuma saiya d'aga bak'uwar Number ce

"Ina magana da MISBAH Hussain mijin Jasra,"?

"Eh shine,"

"Kazo Ni'ima hotel room 36 zakaga Abunda matarka Jasra ke Aikatawa," tinkan Yayi magana Aka datse kiran

Cike da mamaki yatashi Yashiga mota yanufe can

Cikin sa'a kuwa d'akin bud'e yake kawai saiya tura Kai Ciki

Abunda yagani ne yasa Numfashinsa Yatafi yawon wucen gadi saidaga baya Yadawo,

Jasra yagani Da wani k'aton suna Aikata Zina

Runtse idanuwansa Yayi wasu Hawaye Suka soma silalo masa Tabbas cutar da yama Amna itace take fita A Yanzu,

Kasa magana Jasra tayi, Jan bargo kawai tayi ta rufe jikinta,

"Bazance muku komai ba kawai kuje kuda Allah, sannan na sakeki saki 3," Yana Gama maganar Yawuce Ransa b'ace..

Sosai take Zazzab'i da ciwon Kai hakan Yasa suka nufe Asibiti gwajin farko Akace tanada ciki ne, zoga murna gun Ahlin duka, bayan Ansallamota suka dawo gida,

Yana Zaune Yana sak'awa da kwancewa kawai Yaga gwanda yaje Yasami Abban Amna kawai Amma da kunya Saidai baida wata mafita sai gareshi,

Tafiya kuwa yayi har office d'insa ya samesa yamasa maganar

Abba yaji dad'i Amma Saida yamasa fad'a da nasiha sannan

Dukansu An had'u Babban palourn harda MISBAH d'in Abba yake basu hak'uri Kan subari Amna Takoma tinda ya gano kuskuren sa,

Saida su Hajiyar sama sukayi Masa fad'a Sosai Sannan suka bari Suka koma, Koda Yasami labarin cikin murna ba'a magana,

Soyayya kulawa tattali sukewa junansu..

Yau Aka fara bikin Aira da Samir tinda Aka Fara dukansu sukayi busy ko had'uwa Suka daina yi saida Aka gaba bikin duka,

Zaune take k'asa ta mik'e k'afafu cikinta ya girma Yashiga watan Haihuwa sai faman shagwab'a take masa Shikuwa sai biyeta yake, Yana tausa Mata k'afafu A Yanzu ya d'auke hutu ne gun wasansa,

"Ashe Akwai Ranar da zansamu kulawa da gareka Honey,"?

"Oh my dear kada kituna baya Kawai lokacin bana cikin Hankalina ne, natuba Amin Aikin gafara,"

Dariya kawai tayi tana Jin dad'in ganin wanna Ranar,

Waaaashhhhhh

"Meye,"

"Cikina"

"Subhanallah tashi muje Asibiti,"

Ganin takasa tashi yasa sungumeta sai mota suka nufe Asibiti

Suna zuwa Aka K'arb'e ta d'akin Haihuwa Aka shiga da ita,

Safa da marwa kawai Yake waje duk Hankalin sa yatashi Saidaga baya Yasamu Kiran iyayensu ya fad'a,

Take kuwa sukazo suna zuwa Ana fitowa bada Labarin Amna ta sauka Yara 2 Macce da Namiji, ai cikin sauri Ya fad'a d'akin

Rungumeta yayi Yana kissing d'in goshinta

"Nagode my Amna Ina sonki wllh sama da sonda nakema kaina"

"Nima Haka mijina Ina sonka"

"To marasa kunya saiku saurara hakanan ko,"Cewar Hajiyar sama

Dariya kawai sukayi

Batajin Ciwon komai hakan Yasa Aka sallamosu

Kulawa sosai suke samu itada baby

Ran suna Yaran suka ci sunan Amal Amir maccen sunan mahaifiyar Amna Namijin kuwa sunan Daddy

Anyi shagali Sosai

BAYAN SHEKARA D'AYA,

Acikin shekarun Nan komai ya faru masu Dad'i dama marasa dad'i

Marasa dad'in kuwa shine rasuwar Hajiyar sama sunyi kuka Sosai bama kamar Amna

Masu dad'in kuwa haihuwar Aira inda ta haife yara 2

Amna kuwa Yanzu yaranta 4 harda Takwara Tama Hajiyar sama

"Allah Mai iko yanzu nice da Ansa sunan Mrs MISBAH, Ashe Ranar zata zo Wadda zata kasance NI DA MISBAH,"

"Sosai kuwa ba iya ke kawai ba nikaina banyi tsammanin hakan ba Amma komai daga Allah ne Ina k'aunar ki Amna fiye da Yarda Zan fad'a ki fahimta,"

Rungume juna sukayi cike da k'aunar juna...

Jasra kuwa SAURAYIN Nata ya damfareta duk wasu Kud'i data tara daga K'arshe ya barta, bayan yasa Mata cutar H.i.v tayi kuka tayi Dana sani taso Ganin MISBAH Amma hakan Bata yuba daga K'arshe Dai CUTAR tazama silar mutuwar ta,

Hakama SAURAYIN Nata garin tsallaka titi Aka mota tabi takansa Kuma wanda yatakashi yatsere...

Koda su MISBAH suka Sami labarin fatan Samun Rahamar Ubangiji Kawai Suka musu, su dai yanzu DUNIYA tamusu Dad'i soyayyar su Kawai suke gudanarwa..................

ALHAMDULILLAH ANAN KAWO K'ARSHEN LITTAFIN NAN NAWA INDA NAYI KUSKURE ALLAH KA YAFEMIN INDA NAYI DAIDAI ALLAH KABAN LADA, INA K'AUNAR KU MASOYANA.................

(SHAWARA)

Idan kina sonshi baya sonki, kana Sonta bata sonka, to kanemi kusanci da ita Koda yaushe kada kibada tazara kullum ki nemi Abunda zaisa ya tuna ki wanna zaisa ya soki ta soka in Sha Allah Domin kulawa itace soyayya...........

Kuyi hak'uri ganin najima ban kammla Wannan buk d'in ba Wllh bada lafiya ne shiyasa.....

Thursday 17/8/2023 August

_BASEERATA ITACE ARZIKINA_

Whatsapp number 07064903617
Chapter 10 · 0% Book details