← Book details Ni Da Misbah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 10

Sashe 5

Ni Da Misbah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin k'warewa MISBAH ke tuk'in sai balala k'amshi yake fuskarsa sai shek'i da murmushi yake,

Samir Yace"Ah Abokina Wai wannan farincikin Haka fa saikace kaciyo wani kofin, waima Ina zaka kaini,"?

Murmushinsa Mai kyau yasaki Kafin Yace"Zan saidaka ne, kawai zamuje inda wadda nakeson Aura, I mean budurwata,"

Da mamaki ya gyara zamansa Yace"budurwarka kuma? Yaushe kayi budurwa Ni bansani ba,"

"Oh kacika surutu samir kaidai zuba Ido idan munje Yanzu kaganta Ai,"

Baisake magana ba Dan shi mamaki kawai yake,

Bakin wani k'aton gida Suka tsaya, Yaciro waya ya Kira ring 2 tad'aga banji me tace ba Yace"Gani bakin gate" kit ya k'atse Kiran,

Aikuwa saigani nayi Anwangale gate suka Shiga Mai gadi Yana gaidasu,

Parking sukayi

Shidai Samir yanata kallon ikon Allah,

Ba'a Jima ba saiga wata matashiyar budurwa tazo da Kayan Y'an Aiki Ajikinta tamusu nocking A motar,

Zuge glass d'in motar yayi Tace"Sannuku da zuwa dama Aunty tace nazo nayi muku jagora zuwa ciki Kafin tazo,"

"Okay badamuwa, Samir muje,"

Shiga sukayi har wani k'aton palour ya k'awatu sosai

"Ku zauna" tace

Cika gabansu tayi da Kayan ciye ciye da drink's,

Bata Jima da fita ba sai Kawai sukaji wani fitinannen k'amshi ya nufo palourn taku take d'aid'ai cike da Nuna ita d'in wayayyar macce ce,

Kallonta Samir yayi sanye take da Riga da sket Wanda sukayi bala'in kamata sun fidda yanayin surar jikinta duka, Kamar inta motsa kayan zasu yage saboda matseta d'in da Sukayi, bakinta d'auke da cingom tana taunawa Yana bada sautin d'as d'as d'as kafafunta sanye da takalmi masu tsini, kanta Yasha kitson Attached har gadon bayanta bako mayafi iya d'an kwali kawai ta d'aura Akanta ,

"Hello I'm so sorry my Hero nabarka kana jira Ina maka kwalliya ne shiyasa" tak'are maganar tana Zama daf dashi kamar zata haye kansa,

Samir kuwa kuwa mamaki takaici sun hanashi Koda dogon motsi Wai MISBAH yarasa wama zaiyi gurin Aure sai wannan sauran shagon, eh Mana sauran shago gata duk bleaching yaci zarafinta daka ganta kasan tarbiya Addini sunyi k'aramci tare da ita Amma Saboda toshewar basira Wai ita Yake so.......................

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or 07031012948

*NI DA MISBAH*
_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya Writers)*

" *We Rule the World of Writing* "

https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK (24), NI DA MISBAH •LOVE STORY• FREE BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *NI DA MISBAH*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*AUGUST %8%*

*Page 41 to 50*

......Shikuwa sai faman Murmushi Yake mata, "Kinyi Kyau My love,"

"Thanks Hero, wannan Abokin kane? Amma bayason magana,"

Sai A lokacin cikin dauriya Yace"Sannu" ya d'auke kansa tare da mik'ewa Yana barin palourn

"Amma baici komai ba ko gaisawa baijira mukayi ba Hero"

"Bayajin Dad'i ne shiyasa, Amma ai Ni naci, nazo muyi magana dake Mai Mahimmanci ne,"

"Inajinka Hero"

"Shin Zaki Aure Ni,"?

Far tayi da ido Cikin tsabar wayewa tace"Wazaice baya son Babban Yaro Handsome guy Kamar ka, kanaji da Kyau Kud'i ilimi gashi kana tashe Aduniyar"

"To zanje nayi magana da iyayena kuma Nan bada jimawa ba nakeson Ayi bikin," Yana Ida maganar ya mik'e

Rakosa tayi suna fira har mota, Shiga yayi sukayi sallama sannan suka wuce,

"Amma banji dad'in Abunda kamin ba Samir"

"To mezan maka MISBAH, yanzu fisabilillahi Wannan fitsararriyar zaka Aura,"?

"Is okay Samir Banda option ne Dan kare kaina daga Wannan mayatacciyar yarinyar yasa dole Zan Amincewa Auren Jasra,"

"Wllh MISBAH bawai Baki nake makaba Amma Akwai Ranar da zakayi kuka da idanuwanka Akan son Amna sannan zakayi Dana sanin duk wani walak'anci daka mata, kuma saikayi Dana sanin zab'ar wannan k'od'ad'd'iya"

"Eh kabari nayi Rayuwata ce ai Bai shafe kaba banason Shawara indai wannan ce ka rik'e Abunka"

Bawanda Yasake magana har ya sauke shi gida,

Kamar Yarda suka saba had'uwa duk weekend Dan tattauna matsalarsu da neman Shawara ne

MISBAH ya gyara zamansa Yace"dama Inason sanar daku cewa Nasami Mata Wadda Zan Aura Yanzu Haka mungama magana dasu kawai Intura iyayena ya rage Kuma da wuri nakeson yin bikin Dan zanfita k'asarnan zuwa buga wani Wasa a calponi'a"

Tinda Yafara maganar taji tamkar Yana saka wutane A zuciyar ta komai nata Ya tsaya cak,

"MISBAH bayan Y'ar Uwarka tana sonka shine zaka fita waje Neman wata Matar,"? Cewar daddyn sa

Wayewa Irin ta MISBAH Sai ya fauze Yace"A'a Daddy bawata soyayya tsakaninmu Kawai shak'uwa ne na Y'an uwantaka itama tafara fahimtar hakan Yanzu, Ni Jasra nakeso Gaskiya"

"Idan Jasra kake so itace zab'inka to mu namu zab'in itace Amna kuma dole kayi Abunda Mukace domin mu muka haifeka bakai ka hafemu ba" Cewar Ummansa

"Umma kuyi hak'uri Ni Wllh banason Amna ita kawai Y'ar uwa tace Amma bawani so tsakaninmu Dan Allah ku janye maganar,"

"Idan kuwa Akace Za'a janye maganar Amna to lalle Za'a janye maganar jasra,"

"Umma ku fahimce Ni Mana Soyayyata Bata kanta kuma yanzu ai Andaina Auran dole ko ga Macce balantana Ni Namiji gsky Ni bazan Aure Amna ba Dan ba ita nake so ba,"

Tas tas tas Umma ta mik'e ciki fushi ta wanke misba da Mari har sau 2 ko wanne gefe tace "MISBAH zaman waje inda turawan shine ya lalata Tarbiyarda na baka har muke magana kana maidamuna kana jayayya damu,"?

Cikin mamaki tsoro yake kallon mahaifiyar sa Domin wannan shine Karo na farko data tab'a dukansa da dai wannan girman nasa, Kuma Wai saboda Amna? Hunmmm lalle Amna zata gane tashiga gonar sa,

'Umma yau marina kikayi fa,"?

"Eh MISBAH na mareka idan zaka Rama ne kuma katashi ka Rama, wllh Aure tsakain ka da Amna ba fashi indai nice na haifeka"

"Kinyi daidai Aisha k'ara masa"

"Innalillahi wa'inna ilaihin Rajuun Wannan wane irin Abu ne kudaina Dan Allah kubarshi hakanan Tinda baya so ba'a dole" Abban Amana yace hakan

Hajiyar sama kuwa kasa magana tayi domin ta hango tsana Sosai cikin idanuwan MISBAH inda cikin idanuwan Amna kuwa Soyayya tagani kwance muraran wannan ya hanata cewa komai

Wasa Wasa Abu ya soma Zama fad'a cikin palourn inda su Daddy suka kafe sai MISBAH ya Aure Amna Abba kuwa ya kafe Akan a'a bazaiyu Saboda farincikin wata ba Ab'ata na wani

Abun yayi matik'ar d'aga Hankalin Amna tinda tazo duniya Bata tab'a ganin Iyayen nasu suna Koda musu bane Amma Yau Saboda k'addarar Soyayyar ta dalilin *NI DA MISBAH* iyayensu suna fad'a,

Mik'ewa tayi tsaye cikin kuka tace"Ya Isa Umma kudaina Dan Allah indai Dan nice na hak'ura na janye soyayyata Dan Allah kudaina wannan musun,"

Numfashi ta taji yasoma sama sama kantayi wani k'ok'ari tuni tayi baya tafad'i kasa A sume,

Cikin tashin Hankali Abbanta yayo kanta dasu Daddy suka d'auke ta zuwa Asibiti................

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

*NI DA MISBAH*
_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya Writers)*

" *We Rule the World of Writing* "

https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK (24), NI DA MISBAH •LOVE STORY• FREE BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *NI DA MISBAH*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*AUGUST %8%*

*Page 41 to 50*

......Shikuwa sai faman Murmushi Yake mata, "Kinyi Kyau My love,"

"Thanks Hero, wannan Abokin kane? Amma bayason magana,"

Sai A lokacin cikin dauriya Yace"Sannu" ya d'auke kansa tare da mik'ewa Yana barin palourn

"Amma baici komai ba ko gaisawa baijira mukayi ba Hero"

"Bayajin Dad'i ne shiyasa, Amma ai Ni naci, nazo muyi magana dake Mai Mahimmanci ne,"

"Inajinka Hero"

"Shin Zaki Aure Ni,"?

Far tayi da ido Cikin tsabar wayewa tace"Wazaice baya son Babban Yaro Handsome guy Kamar ka, kanaji da Kyau Kud'i ilimi gashi kana tashe Aduniyar"

"To zanje nayi magana da iyayena kuma Nan bada jimawa ba nakeson Ayi bikin," Yana Ida maganar ya mik'e

Rakosa tayi suna fira har mota, Shiga yayi sukayi sallama sannan suka wuce,

"Amma banji dad'in Abunda kamin ba Samir"

"To mezan maka MISBAH, yanzu fisabilillahi Wannan fitsararriyar zaka Aura,"?

"Is okay Samir Banda option ne Dan kare kaina daga Wannan mayatacciyar yarinyar yasa dole Zan Amincewa Auren Jasra,"
Chapter 5 · 0% Book details