← Book details Ni Da Misbah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 10

Sashe 1

Ni Da Misbah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*NI DA MISBAH*
_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK (24), NI DA MISBAH •LOVE STORY• FREE BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *NI DA MISBAH*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*AUGUST %8%*

5/8/2023 August

*Page 1 to 5*

.............Tsaye take Gaban wani tangamemen photo ta tsirawa hoton idanuwa batako kifta Idanuwa, Hasko kasancewar ta Matar sa kawai take tana murmushi,

Aunty Amna! Aunty Amna!! Aunty Amna!!! Parlorn Ya karad'e da muryar Aira turus ta tsaya ganin ta Gaban Wannan photon ita A Yanzu ma har haushi nacin Hoton yake bata, Amma ba halin nunawa Domin tana kuskuren Fad'ar Aibunsa yanzu zasu Samu matsala, "Aunty Amna fa kinajina tindaga compound nake kwad'a miki kira har nazo Nan Amma Kika k'i Ansamin why,"? Ta fad'a tanad'an shagwab'e fuska,

Ahankali matashiyar budurwar tajuyo sai A sannan nasamu damar k'are mata kallo, Chocolate kaloce Wadda bazaka kirata fara ba kuma bazaka kirata bak'a, bakin ta K'arami tamkar Anyanka da reza, idanuwan ta matsakaita farare tasss dasu Hancinta ma daidai halintar fuskarta, Kanta na kalla Gashine kwance Kan gadon bayanta Wanda Yasha gyara sai k'yalli Yake, jikinta smooth sanye take da Riga da sket na Atamfa kalar maroon wad'an da sukayi matik'ar dacewa da jikinta, Bari dai nabarku haka reader's kawai ku Hasko irin Yanayin Halittar Amna,

Cikin Sanyin Muryarta tace"Sorry my Aira, banjiki bane Yaya Akayi,"?

"Kinanan inda Kika saba, Hajiyar Sama tana kiranki," tana fad'a Mata hakan tawuce saman parlorn Tana Danna wayarta,

Fita part d'in tayi Duka Ta nufe wani part d'in Ahankali ta tura k'ofar parlorn tashiga da sallama

Zaune taga Hajiyar Hannuwanta d'auke da Newspaper tana karantawa,

Zama tayi kusa da ita Had'id'a d'aura kanta saman kafad'arta Tace"Gani Hajiya"

"Nace Yau bazan samu Wannan tea d'in bane"?

"Yi hak'uri Hajiya natsaya wani Abu ne Bari Yanzu Zan had'a miki,"

"Ko dai kin tsaya photon MISBAH ba," Rufe idanuwanta tayi Alamar Kunya tafad'a kitchen

Dariya Hajiya tayi Had'id'a cewa"Allah ya tabbatar muna, Bari na kirasa Yau bamu gaisa ba,"

**""""""""""""""""""""**

D'akin motsa jiki Yafito d'auke da towels Yana goge gumi, Kyakykyawane Ajin K'arshe Farine dogo fuskar da d'auke da saje, kallo d'aya zaka masa kasan Hutu naira sunsami gurin Zama Ajikinsa, Wayarsa dake cikin Aljihunsa tafara ruri Jin sautin daban Yasa Yad'aga fuskarsa d'auke da murmushi Yace"Allah Yak'ara wa Hajiyar mu lafiya dama Nisan kwana, Allah yabawa Y'ar tsohuwar matata lafiyar k'afafu"

Dariya sukayi dukansu Tace"ja'irin Yaro da bakasan Ina Matar takaba Saida nakira ka,"?

"I'm so sorry Hajiya Wllh munyi off ne dayawa Yau mukayi Zama na musamman muda wasu manyan k'asarnan Kan Wasan da zamu buga gobe, to dik Hankalina nakan Wasan,"

"Hakane Allah yataimaka to, Amma yaushe zaka dawo gida,"

"Kunyi missing d'ina Hajiyata,? Inasaran cikin satinnan Domin gobe Wasan na K'arshe Wanda ya kawoni Nan Canada"

"Sosai mukayi kewarka MISBAH bama kamar Y'ar Uwarka Amna tafi kowa son ganin dawowarka,"

Tamkar ta watsa masa ruwan zafi Haka Yaji, take murmushin fuskarsa ya d'auke wani Irin b'acin Rai ya bayyana,
Aduniya Idan dakwai Abunda ya tsana baiwuce Amna ba balantana suyi maganar Soyayya tsakaninsu, baice komai ba Ya datse kiran tare da kashe wayar duka ya Ajeta Duka gefe,.......... ..........

Nikuwa mamaki Yasani tsaida rubutun nawa Dan nakasa gane lamarin game da Soyayyar Amna da MISBAH

Akwai chakwakiya kenan to mukance tare Kuma cikin littafin NI DA MISBAH.......................

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or 07031012948
*NI DA MISBAH*
_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK (24), NI DA MISBAH •LOVE STORY• FREE BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *NI DA MISBAH*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*AUGUST %8%*

*Page 6 to10*

.......Dogon tsaki Yaja Ya kwanta Ransa na b'aci Dan kawai Anyi masa maganar Amna shifa K'anwa kawai Ya d'auke ta Amma yalura Dukansu sunkasa fahimtar hakan, Shi Koda zaiso Ai bazai yarinyar da takusan tashi gabansa ba, wani tsaki yasake ja,

"Ah Abokina Wai lafiya irin Wannan tsakin Haka? Waima tsaya tukuna me kake tinani haka,? Tinda nashigo naketa magana but shuru kasan fa babuk'atar dogon tinani musamman kasan gobe zaka buga Wasa,"

"Nasani Samir kawai wani Abune Dana tsana Aka tinamin dashi shine yaja gulamin komai wallahi,"

Zama yayi gefensa Cikin kulawa Yace"Meye shi haka? Amma koma meye shi nasan ba k'aramin haushinsa kasa A ranka ba,"

"Haushi? Uhunmnn idan kace haushi katsaya gun k'aramin lamari Ni tsanar Abun nayi Kamar yarda na tsane mutuwata,"

"Amma kasan tsanar Abu irin hakan ba kyau ko, Amma ka fad'amun ko meye mana ko bankai matsayin da zanji damuwar ka bane,"

Mtssswww"bahaka bane wata sister d'ina ce maishegen nacin tsiya wai ita saboda tsabar Rainani da tayi Wai ita Ni takeso, Abunda ke k'ara k'onan rai wllh nasan girman ta ganaba fa,"

Dariya Samir Yayi

"Kagani ko shiyasa Koda ka Yawaita tanbayan damuwana nake b'oyemaka saboda banson Wannan halin naka komai saikamai dariya saikace wani zararre, Haba,"

"Calm down Abokina, Yi hak'uri nadaina kawai Abunda yaban dariya irin yarda ka Raina yarinyar ne, baka San Ba'a Raina girman macce ba,? Kuma ma meye laifinta Dan tasoka? Ai Masoyi Yafi mak'iyi,"?

"Bazaka gane bane samir nidai ba ita nakeso ba"

"To wa kake so? Nidai Iya sanina bansan kanada Wadda kake so, Saidai wad'an da kesonka,"

"To zansami d'aya ne Amma ba itaba Ni wadda zanso daban take Samir ni wllh natsane wannan Dan iskanci Wai harda zuwa tayi zanena da nata ta Rubuta jikin photon Wai NI DA MISBAH, Natsane ta fiye da yarda Zan kwatanta maka, Mtssswww"

Doguwar Ajiyar Zuciya Samir ya sauke Kafin yace" Amma baka ganin kayi kuskuren tsanarta Hakan ba kyau fa tsanar mutum Haka Koda ba Y'ar Uwarka bace balantana jininka,"

"Relax Samir maganar tawuce ta isheni hakan, Yanzu Muje restaurant yunwa nakeji wllh,"

****"""""""""""""*****

Cike da mamaki Hajiya take kallon wayar A hannunta wato shine Dan tayi maganar Amna saiya datse kiran, Amma zatayi tufkar hanci Kan Lamarin,

Fitowa Tayi d'auke da Kofin Shayin na Maganin mura data had'a Mata, Tace"Hajiya har kungama wayar ne,"?

"Eh"

kawai Tace tana k'arb'ar Shayin

D'an nazarin fuskarta tayi,

Tace"Hajiya kinyi masa maganata ko shiyasa Ya datse kiran naki ko,"?Cikin sanyi tayi maganar

Tausayi tabawa Hajiya, cikin k'arfin Hali tayi murmushi Tace"A'a ko d'aya kinsan zumucin ku Ai zaidawo cikin satinnan zaidawo kuma in Sha Allah komai zai wuce kinga idan Yadawo d'in saikiyi k'ok'arin ganin kinsami soyayyar sa,"

Murmushi tayi Had'ida barin part d'in duga,

Girgiza Kai kawai Hajiya tayi cike da tausayin Amna,

_ASALIN DUKA FAMILYN_

Alhaji Hussain da Alhaji Hassan Y'an 2 ne suna matik'ar k'aunar junansu

Hauwa Hajiyar sama kenan Itace Mahaifiyarsu suna kiranta Hajiyar sama ne saboda nata part d'in kusan A sama yake, Kuma da kanta ta zab'a musu Auren matansu Hussain Ya Aure Hafsat inda Hassan ya Aure Aisha bayan wasu watanni da Auren su Matar Hussain ta haife d'a Namiji wato MISBAH Sosai Akayi murna A cikin Ahalin kusan Duka renon MISBAH hannunta Yadawo Sosai take k'aunar shi kulawa kuwa ba irin Wadda Bata bashi,

Saida Akayita shekara 3 Sannan Aisha ta haihu ta haife macce, Amna, sosai Akayi shagali bikin Haifar Amna bai hana Aisha kula da MISBAH, itakuwa mahaifiyarsa kula sosai takebawa Amna, Sanda Amna tacika Shekara 3 A lokacin MISBAH Yacika shekara 5 Kuma Yana ss 2,

Amna tabud'e Ido da MISBAH tana tsananin k'aunar MISBAH shima Yana kulawa da ita Sosai

Bayan Shekara 7 Mahaifiyarta tasamu wani cikin Kuma gurin hafarsa tarasu,

Mutuwar Aisha ta girgiza mutanen gidan Sosai bama kamar MISBAH,

Amna tayi kuka sosai MISBAH shine Mai lallashinta Ganin kulawa da soyayyar sa yasa Amna d'aukar MISBAH yana Sonta,

Bayan wasu shekaru Amna tashiga school tana Ss 1 inda MISBAH kuwa ya tsalka waje Domin can ya cigaba da karatunsa,

Alhaji Hassan yak'ara Aure bisaga matsawar Hajiya, cikin Ikon Allah Bata kasance muguwa ba

Mahaifiyar MISBAH kuwa tasake haifar Yara 3 suka zamo su 4 inda Aira Itace ta Ukun su.............

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or 07031012948

*NI DA MISBAH*
_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._
Chapter 1 · 0% Book details