← Book details nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 31

Chapter 11

nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

____Bayan mun idar da Sallar isha'i wata firar muka cigaba da yi, idan Khadija tayi nata nima sai nayi nawa hakama Umar, yayin da Jiddah ke faman cika tana batsewa tana jan dogon tsaki, ko ita da wa oho,

yanzu haka Umar ne ke bamu labarin wani Almajiri daya shiga bara gidan wata amarya sai mijin ta yace "almajiri kawo kwanon ka". Sai amarya ta leko ta amsa kwano, ta zuba masa abincin, Koda ta miko mai kwano sai ya amsa yatafi zauran gidan yana kuka, sai mijin amaryar yabiyo almajirin, ya tambaye sa meye dalilin kukan nasa "ko abincin ne ba zai isheshi ba?". Sai almajiri ya girgiza kai, sai mijin amaryar yace "to maye kake ma kuka?". Budar bakin Almajiri sai yace "shi ba komai ya sashi wannan kukan ba illah yana tsoran agama aure kyawa wan mata kafin lokacin su yai_

" Idan ke/kaine ya zaki/ka yi", haka ya jefe musu tambaya aikuwa nan sukaita tafka muhawara suna shirme

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Sadeeq kwan ce a kan gadon farook yana cikin Instagram sai kallon hotuna yake, kwatsam idanuwan sa suka sauka akan hotan wata yarinya, acikin zuciyar sa yace "daga ganin ta tanada aji kuma ba zaka ce mata 'karamar yarinya ba domin zata iya kaiwa 25 years old da haihuwa". Kara shiga account dinta yayi nan take hotunan ta da take dorawa suka bayyana sosoi Sadeeq ke kallon hotunan, sunan account din ta ya kalla yaga anyi rubuta kamar haka *Zuby officially*

"Wow" ya fada afili Suna mai dadi Zuby haka yaita maimaita wa bata da wani kyau a fuska kuma bawani haske gareta ba amma dagani ta 'kara daman da yake sa hasken fata, 'kirjin ta cike yake da dukiyar Fulani tana da dirin jiki

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Abuja
Ba muyi wata dinner ba kasan cewar bamu dade da cin abincin ba shayi Momy tasa Suwaiba ta hado mana yaji ni'inal da kayan kamshi, mukai ta kurba kamar wasu larabawa 😂
Bayan mun gama kowa ya watse amma nikam sarkin tsoro d'akin Ummi nayi tana 'ko'karin rufe kofar nai saurin turawa
Da mamaki tace min "sisi yadai?". "Anan zan kwana" na fad'a yayin da nike shigowa ciki, ta maida kofar ta rufe

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Ahaka rayuwa ta cigaba a gidan Momy, tsakanina da Jiddah babu jituwa zan iya cewa tun nazo gidan magana bai shiga tsakanin mu ba, kuma babu Wanda ya lura a gidan saboda tun asali kowa yasan bama wani shiri,
Yau kimanin kwana bakwai kenan da aurena da Sadeeq amma har yau ban sashi a cikin ido naba gashi su Khadija har sun koma makaranta

Muna falo nida Momy a zaune sai Suwaiba dake faman zirga zirga ta kai ta komo tana kokarin hada abincin rana kafin su Khadija su dawo,
"dauko min waya ta a bedroom dina" cikin sauri na mike domin Momy batasan simi simi
Bayan na dawo nace "Momy gashi nasamu wayan ma tana ringing". "Kawo mugani waye ya kirani" ta amsa tana shafa screen d'in wayar sannan ta kara a kunne
"Wa'Alaikumussalam". shi ne abinda naji Momy tace kafin tace "lafiya lau".
Ta kara da cewa "wallahi Sadeeq zan cimaka mutunci fiye da yadda kake zato kasan dai yanzu ba kamar da bane kanada nauyi a kanka amma kayi burus da mu dama gwada ka nayi naga hankalin ka, to maza maza kazo gobe inason magana da kai na fada maka idan kuwa ba haka ba zanyi mummunan saba maka".

Cikin fushi Momy tace "bazan saurare ka ba Sadeeq baka da abinda zaka fada min na yadda, kaima kasani domin bakada wani uzuri kayi abinda nace maka kawai".

Tana gama fadar haka ta kashe wayar

Jim kad'an saiga wani kiran ya sake shigowa daga yadda naga Momy ta daga wayar na gane yaya Mubarak ne d'an yayan ta, na sanshi sosai ya nada mutunci da yana nan ne da zama amma yanzu yatafi India saboda ya karasa karatun sa a can, kallo na tayi kana tace
"bani ruwa mana mara sanyi nasha". "To" nace na mike cikin natsuwa koda na dawo har ta kammala wayan

NI DA YAYA SADEEQ                     
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Chapter 9 · 0% Book details