Chapter 09
nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
_______Na shiga uku ni Siddi'ka Suleiman, anya su Daddy suna 'kauna ta nasan kaf duniya babu wacce Sadeeq ya tsana kamar ni, amman wai yau ni ce zan zama matarshi
"Kutashi kutafi Allah yayi muku albarka".
Daddy ne ya fad'a haka
Sadeeq yariga ni tashi saboda ni jikina babu kuzari
"kai Sadeeq" Daddy yace "ka kira abokanan ka na kusa a waya ka shaida musu".
Murya acan cikin ma'ko garo Sadeeq ya cewa Daddy "ba sai sun shaida ba". Yana gama fad'ar haka ya fice
A masal-lacin juma'an dake garin buruku aka d'aura auran SADEEQ ALIYU MAI GORO da amaryar sa SIDDI'KA SULEIMAN d'umbin jama'a sun shaida d'aurin auren duk da kasan cewar babu ango da abokanan sa, Daddy ne yayi wakil cin Siddi'ka, inda d'aya daga cikin abokan Daddy da suka hallar ci taran, mai suna Alhaji Imran yayi wakilcin Sadeeq, auren da aka d'aura abisa sadaki dubu tamanin, lakadan ba ajalan ba, yayin da Alhaji Imran ne ya biya sadakin
A kwai 'yan 'kauyen Dande da dama, dasu ka samu halartar zuwa masallacin, saboda su gabatar da sallar juma'a da yawan su mamaki suke saboda kowa yasan tsamar dake tsaka nin Sadeeq da Siddeeqah amma wai yau ya zama mijin ta ko da shike daman ance idan zaka yi 'kiyayya kada ka tsanan ta haka ma soyayyar.
Da haka taro ya watse koda Daddy ya dawo gida anne mi Sadeeq anra sa kuma an kira wayar sa a kashe
Siddi'ka kuwa tun sanda ta shiga d'aki take raira kuka, rarrashin duniya anyi mata amma ta'ki barin kukan kamar ma dad'a zuga ta suke yi, haka suka gaji da lal-lashin ta suka zuba mata ido, saida Daddy yafa d'awa su Inna zai shigo dasu Alhaji Imran Sannan yaje ya shigo dasu, a falon Hajiya Inna suka zauna daman su Hajiya Inna sun girka shinkafa da miya Khadija ce keta hidama da ba'kin Daddy Sai da suka ci suka sha sannan Inna tazo suka gaisa
Suka yi mata Allah yasanya alkairi anan Daddy yayi mata sallama yace "su zasu wuce Abuja a can jirgin su zai tashi izuwa lagos
"To bari na kira maka Aisha d'in ko". Inna ta fad'a tana 'ko'karin mi'ke wa
cikin sosa kai Daddy yace "ai na sallame su suma nan bada jimawa ba zasu wuce" mamaki ne yakama Inna saboda ita dai bataga sanda 'karami yayi magana da Aisha ba
Hajiya Dady ya kira sunan ta "da mai sunan manya zasu tafi nayi maganar yar aikin za a nemo miki nanda kwana biyu".
"Wace yar aiki! 'karami duk yaran dake ci'kin Dande basu isa ba har sai an nemi wata, ai ko Ladiyo 'kawar Siddi'ka na yiwa iya-yen ta magana tunda yarinyar ta iya aiki, kuma ta ma girmi Siddi'ka d'in,
Nasan baza ta 'ki ba, sai ta dunga zuwa tana tayani d'an wanke wanke da shara tama dunga d'ebe min kewar Siddeeqah d'in, idan wata yayi kana yima ta d'an ihsani".
"babu damuwa" Daddy yace yana mai ciro kud'i daga aljihun sa masu tarin yawa, 'yan dubu dubu ya mi'ka mata
"q'Karami kud'in wancen watan ma daka bani suna nan ban taba suba saboda duk abinda nike so akwai a gidan nan da ka bar shi kawai a gurin ka Allah yama albarka".
Hannun ta Daddy ya kamo yasa ka yan bandir d'in 1000 guda biyu "haba hajiya ki karba koda sadaka ne kinayi dasu idan ki ka ga mai buka ta".
Godiya Inna tai ta kwara rowa 'Karami tanayi mai addu'ar Allah yatsare
"Ina mai sunan manyan take ne Hajiya?". Daddy ya tambaya
"ai tun sanda ka fita ta shiga d'aki tana rusa kuka mun gaji da lal-lashi ne muma".
"Wani d'akin?".
"na can karshe". Ta bashi amsa
Tashi yayi ya cewa abokan sa "minti biyar".
A kan gado ya same ni kwance nayi rufda ciki
Siddi'ka Daddy ya kira suna na cikin sas-sanyar murya
Inaso kisan duk abinda ha'Kuri bai bawa bawa ba a rayuwa rashin sa ma ba zai ba da ba, kuma wannan shine burin mahaifiyar ki, tin sanda aka haife ki tace "idan Allah ya raya ki d'an ta Sadeeq shine mijin ki ko bayan baran ta mu cika burin ta, A halin yanzu bamu san awani hali Amina maman ki take ciki ba, zai iya yuyuwa tana nan a raye nesa damu, zai kuma iya yuyuwa Allah ya d'auki ranta, amma muna nan muna addu'a idan har Amina tana a raye Allah ya bayyana mana ita, nayi hakanne a yanzu saboda bani da tabbacin zan 'kara wasu shekarun a raye, nasan ko bayan babu raina na cikawa kanwa ta burin ta za tayi alfahari dani, kiyi mana biyayya amatsayin mu na iyayen ki bazamu taba cutar da ke ba zakiga ribar abun nan gaba".
Duk maganar da Daddy yayi na kasa d'ago kaina, Ko motsin kirki na kasa ina nan a yadda ya shigo ya sameni, jin shirun da nayi ne naji ajiki na ya fita daga d'akin, kaina na d'ago ina 'karewa d'akin kallo Bansan mai nike nazari ba amma inajin kamar raina zai fita
Umar ne yashigo hannun sa d'auke da kular abinci har kan gadon ya hau yace "aunty Siddeeqah please kada kicemin a a don soyayyar da kikewa goggo Amina ki tashi kici abincin nan nasan dai kina mutu'kar santa kuma duk 'yar da aka ce tayi abu dan iyayen ta to indai tana son su za tayi".
Jin Umar ya ambaci mahaifiya ta na tashi zaune saboda babu 'yar da zata'ki mamar ta "mi 'komin kular". Nafad'a murya ta a dashe
Koda na bud'e shinkafa ce da miya har da nama a ciki, cokali nasa na fara cin abincin amma kwata kwata bemin dad'i ba ji nike kamar ba asaka magi aciki ba
"Umar wai haka abincin nan yake?". Na tambaye sa
"mai yayi?" shima ya tambaya
"naga kan infara ci yana ta zuba 'kam shi yanzu kuma da nike ci wallahi ji nayi kamar inacin magani".
Kallo na yayi muka had'a ido dashi yace "aunty Siddeeqah inaga bakin ki ne domin kowa ya yabi girkin nan yadda yake da kamshi haka yake da dad'i abaki ma".
"To iya magana". Nafad'a ina tura masa kular abincin
"Kaddai har kin 'koshi". Yace yana kallo na
"na 'koshi mana tashi kasa momin ruwa".
"To" yace ya fice daga d'akin, jim kad'an sai gashi da ruwa a cup
yace "Momy" tace "kiyi wanka yanzu gata nan zuwa".
"To". nace
dama akwai bayi a d'aki na amma tsabar neman rigama yasa bana shiga, kuma da sabo dan munriga munsaba da bayin tsakar gida tun kafin a maida mana gidan mu ginin zamani.
Yaukam ciki na shiga wanda nike tsokanar ko sunan sa ma bana son inji ankira min
Ban wani dad'e ba na fito daka bayin kaya na tarar abakin gadon da alamar sababbi ne harda bra da fnt, dakakkiyar shadda ce marun kalo dinkin doguwar riga taji aiki mai kyau da birgewa wanda ya dace da ita.
Ina cikin mamaki saiga Khadija ta shigo fes da ita cikin wata tsaleliyar atamfa "cikin zolaya tace "amarsu har yanzu baki shirya ba Koda yake daman shirin amare ance yana da dad'e wa, sai kiyi kishirya dan ke kad'ai muke jira".
a kwati na na nufa saboda na d'auko kayan da zan saka,
da mamaki Khadija tace "Siddi'ka baga kayan ki nan ba akan gado". Momy tace "su zaki saka".
Hau shin kowa nake ji cikin masifa nace wa Khadija "naji to sai ki ban guri".
Sai da ta 'kyal-'kyale da dariya sannan tace "amarsu kada in 'bata miki rai naji ance ba'a san a 'bata ma amarya rai, musamman ranar d'aurin auren ta, idan ni baki bud'e min ba zaki bud'e ma yayana".
Khadija tagirme ni da 2 years nasan ba zata rasa sanin aure ba tunda ita abirni take kuma tana zuwa makaran ta, sa'banin ni da nike yawan gad'a a gari.
Tana fita na rufo 'kofar sai da na shirya tsaf sannan nafito sai 'kam shin turare ke tashi
Da alamar kan a kawo min kayan sai da aka fesamusu turaruka masu 'kam shin gaske da tsada
buga 'kofar naji a nayi koda na bude Umar ne hannun sa d'auke da jaka da takalmi da gyale duka masu ruwan madara
Yace "Momy tace in kawo miki ki saka idan kin shirya ki fito".
Kar 'ba nayi takalmin irin mai tsinin nan ne ni kuma banason irinsa koda nasa tafiya d'aya buyu na turgud'e
Wata yar karamar jakace kalar dai ta amare a hannu na rike ta, yayin da gyalan na yafa sa a saman kaina.
A gaskiya ina son kwalliya a rayuwa ta saboda haka nike tafiya ina taku d'ai-d'ai duk da ban iya tafiya da takalmin ba lokaci zuwa lokaci ina turgud'ewa Amman hakan bai hana ni yin yanga ba, naman ta da wani lamarin aure
Afalo nasami su Momy duk sun shirya
"Momy wai ina zamu haka?". Na fad'i haka ne sanda nike zama kusa da Inna
"Abuja". Momy ta bani amsa
zaro ido na nayi nace "Abuja kuma Momy shine zaku tafi da ni?".
"Eh" kawai tace min narai-narai nayi da ido 'kwalla na zubo min Daman koda nai wanka banyi kwalliya ba ko hoda ma ban shafa ba, saboda haka na cigaba da yin kuka na ina share 'kwallar da bayan hannu na
Inna ce ta kama hannu na tana matsar kwalla, ba tare da tace min komai ba
Cikin kuka nace "Inna kada kibari atafi dani mana Inna nasaba dake, bazan iya rabuwa ba dake ba, nasan wannan tafiyar ba irin wacce na saba yi bane saboda haka jiki na ke bani, nidai gaskiya bazan je ba".
Cikin sanyin murya Inna tace "to ba gasu Khadija ba acan kuma akwai su Jiddah, baki da damuwa zaki saba kuma duka 'yan uwan ki ne".
"Siddi'ka inaso na ingan ta miki rayuwa ne, saboda 'Karami yace min idan ban bar ki kinyi karatu ba nan gaba dani zakiyi kuka".
Ina sharar 'kwalla nace "Inna ni ba zanyi kuka dake ba ki yarda dani da iya gaskiya ta nike magana".
Daga haka bata 'kara ce min komai ba
Momy ce ta kama hannu na ta yima Inna sallama ina kuka ina kallon Inna haka na baro ta
daman driver mu yake jira a bakin 'kofar fita naci karo da Ladiyo data ke 'ko 'karin shiga gidan mu
A d'an tsora ce ta kalleni sai tayi baya
Bance mata komai ba nashi ga mota idan ta naga ya kawo 'kwalla kuma ta bani tausayi,
ganin haka nayafito ta da hannu aikuwa da gudu tanufo ni
"Siddi'ka ina zaki haka ko sallama babu?".
"Birni mana".
"inda kike zuwa?".
kai kawai na d'aga mata
"Amma shine wannan karan ko sallama babu?".
"nima bansan da tafiyar bane ladiyo kuma karatu zanyi a can d'in ba yanzu zan dawo ba".
"Karatu fa kika ce Siddi'ka, mai zakiyi da makaran ta?".
"Nima bansan me zanyi da ita ba Ladiyo amma dai an cemin tana da mutu'kar amfani kuma nan gaba zai temaka min zanji matukar dad'in karatun".
Cikin sanyin murya Ladiyo tace "to Allah ya bada sa'a Siddi'ka don Allah kada kimanta dani".
Tabani tausayi sosai nasan kaf kauyen nan Ladiyo ba tada kama ta kuma nima banida kamar ta
Wata ran ma ni zanyi tsoka na amma sai inja mata duk da haka bai sa ta rabu dani ba
Nace "Bazan manta dake ba Ladiyo zan dawo gare ku Ina yi miki fatan alkairi kema".
"Ki shiga gurin Inna kice injini taba ki kayan sawa na gabaki d'aya".
"To" tace tayi min godiya mukayi sallama ta shige gidan mu
A lokacin su Khadija sun shiga mota driver yaja muka d'au hanya
NI DA YAYA SADEEQ
بسم الله الرحمن الرحيم