Chapter 08
nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
_______Yana yin tsarin ginin gidan mu 2 bedroom ne amma a ko wani d'aki anyi kofar da mutum zai iya bi ba sai yabi ta falo ba, sai d'akuna biyu da suke a tsakar gida d'ayan na hanyar waje shine d'akin yah Sadeeq,sai wanda idan su Momy sun zo suke sauka a ciki, a kwai kitchen a tsakar gidan da bayi,
Inna bata son amfani da kitchen din d'aki tafi sabawa da na waje,
amma ni nakan yi amfani dashi idan zanyi jagwal-gwa-lo na
Kitchen d'in na shiga na bud'e durowar da nasan muna ajiye Indomie a cikin ta na dauki guda d'aya
Gas na kunna, ruwa na fara tafasa wa nazuba Indomie d'in sannan nakawo tarugu 1 nasaka nazuba mangyad'a a ciki ina juyawa, sai ga Khadija tale'ko kitchen d'in cikin zolaya tace min "ga yaya Sadeeq can afalo".
yace "mai kwatar ki yau sai Allah". Inna tayi bacci tun d'azu, Momy kuma ta tafi d'aki, daga ni sai Umar ne a falo.
hantar ciki na ce tafara kad'awa jikina yafara rawa na kasa magana, bani da tsoro amma ina tsoran had'uwa ta da yaya sadeeq saboda ba da wasa yake min ba, amma duk da haka idan rashin kunya ta, ta tashi yi masa nike
Ad'an kid'ime nace "bari na fasa ihu tun kamin yacin min kinga su Momy za suji su zosu zo su cece ni".
Saka tafin hannaye na nayi na toshe kunnuwa na, saboda inyi 'karar iya karfi na, zan 'kwal-lara 'kara kenan Khadija tayi saurin toshe min baki da tafin hannun ta, tana 'kyal-'kyala dariya
Tace "nad'auka ked'in jaruma ce a she ba haka bane kamar ba kece shekaran jiya kika cemin sai kin rama dukan da ya miki ba, taya zaki rama kina wannan tsoran?".
"Kedalla malama sakeni nayi ihun neman agaji".Nace mata
Tana dariya tace "tsokanar ki fa nikeyi".
Sai alokacin nasaki ajiyar zuciya, nabi ta da duka ta fita tana dariya,
koda na duba Indomie na har ta dawu ta fara kamawa, kashe gas nayi, anan kitchen d'in na zauna, a cikin tukunyar naci, inaci ina santi saboda tayi mini dad'i kuma nayi mata irin dahuwar da nikeso
Bayan na gama ci ne na bud'e baki na sosai na saki wata uwar gyatsa babu ko alhamdu lillah
Na mi'ke tsaye nayi mi'ka
D'aki na na wuce inda natar da Khadija na sharar baccin ta hankalin ta kwance, kan gadon nim.
Washe gari ban farka da asuba ba sai Misalin 8:9am Khadija babu irin tashin da bata yi min da asuba ba, akan nayi sallah amma na'ki sai ma 'kara gyara kwanciya ta da nayi, Kamar yadda nasaba tashi haka nayi babu ko addu'ar tashi daga bacci, na sauka a kan gadon, brush d'ina na d'auka, ina tatsa makilin ne Khadija ta shigo fiskarta d'auke da murmushi, da ganin bakin ta a kwai magana, "au ashe kin tashi daman ke nazo tasa wallahi". Ta fad'a tana matsowa kusa da ni
"eh na tashi" nace mata "wai yanaga kina ta murmushi ne?".
Tace "ba dole ba Daddy fa yazo" shi yace "na taso ki saboda ya tambaye ni kina ina". Nace kina bacci".
"amma wannan karon yazo dawuri gaskiya" nafad"a ina ajiye makilin d'in hannu na
Tace "Eh". naji yana cewa Inna "da karfe 2:pm jirgin su da zai wuce lagos zai tashi shiyasa yayi sammakon zuwa".
Jin jina kai na nayi, alamar gamsuwa "to bari nayi sallah" nace tare muka futo ta nufi d'akin hajiya Inna
Ni kuma na nufi rijiya na janyo ruwa na zuba a bokitin wanka, na kai bayi saida na fara yin wanka sannan na d'aura al'wala
Tawul na d'auro ajiki na, amma irin 'katon nan ne, kuma na wanke kaina babu ko d'an kwali haka na fito daga cikin bayin
Adai-dai lokacin yah Sadeeq ya shigo cikin gidan, had'a ido mukayi, saida ya 'kare min kallo tsaf, sannan yaja dogon tsaki, shasha ya fad'a afili, kana ya wuce ya shiga cikin falon
Saida ya wuce sannan nima na wuce d'aki na, wata doguwar rigar atamfa na ciro mai launin blue da ruwan hoda, baseline na shafa a jiki na sannan na saka atamfar, na d'auki hijabi na nasaka na gabatar da sallar asuba
Bayan na idar na nufi falon hajiya, ina jin gabana yana fad'uwa, narasa mai yisa amma tun jiya da Umar yace "Daddy zai zo" gaba na ke fad'uwa amman yanzu bugun zuciyar tawa yafi tsanan ta
Daurewa nayi, na shiga cikin falon baki na d'auke da sallama, nasamesu su duka harda yaya sadeeq d'in, suna karyawa, Daddy da Inna da yaya Sadeeq suna cin d'an wake, Khadija Momy Umar. Kuma waina suke ci
Daddy ne ya dube ni yace "wa'alaikum'ssalamu d'iya ta shigo ga wuri ki zauna, ya nuna min tsakanin sa da na yaya Sadeeq, na 'karasa na zauna a tsakanin nasu
Sannan nace "ina kwana Daddy".
"Lafiya lau". Yace min "na same ku lafiya?".
"lafiya lau Daddy, ya hanya?". nace
"Al'hamdu lillah ". yace min, yana mi'ko min cokali yace "bimismilah
me sunan manya".
Ina lura da yanayin yah Sadeeq ya canza tun sanda na zauna, ya wani d'aure fiska sai mutsu-mutsu yake yi, ina saka cokali na cikin kwanan yana cire nasa yami'ke tsaye, Daddy ne yakalle sa, yace masa "ya-ya ana cin abinci ka tashi". na 'koshi ne Daddy".
"dawo ka zauna sai mun cinye da kai".
Badan ran Sadeeq yaso ba, haka ya dawo ya zauna ya maida cokalin sa, ina lura da yadda yake cin d'an waken kamar yana cin magani.
Misalin karfe goma 10:00am Daddy zaune a kan kujera Inna na kusa da shi Momy na 2 cter, ni da Khadija na zaune a 'kasa kusa da Momy, yah Sadeeq kuma na gefen Daddy zaune a 'kasa kanshi a 'kasa yana danna wayar sa
Daddy yayi gyaran murya
Sannan yafara da cewa "da farko ina 'kara jad-dada godiya ta ga Allah ma d'aukakin sarki da yabani damar aiwatar da wannan 'kudirin nawa, tsira da aminci ya tabbata ga fiyayyen halitta annabin mu Muhammad (S. A. W). Bakomai ne yasa na taraku anan ba, saidan ke Siddi'ka me sunan manya, ya fad'a yana kallo na, ina san yau d'in nan na ai'watar da 'kudirin mahaifiyar ki akan ki,
Ina fatan zaki yimana biyayya, nasan baki da matsala, saboda mun isa dake ne zamuyi abinda mukesan yi yanzu, ina so kisan bakida Wanda ya fimu a kaf fad'in duniya, bazamu ta'ba cutar da ke ba".
Tun da Daddy ya fara magana gaba na ke fad'uwa, shin wani kalan 'kudiri ne wannan da har Daddy yace 'kudirin mahaifiya ta ne". Banida wannan amsar saboda haka naci gaba da sauraran abinda Daddy ya cigaba da fad'a
"naso ace sauran 'yan uwanku suna nanan, amma duk da haka kuma kun isa shaida, kuma akwai abokai na guda biyu wa'inda tare dasu zamu tafi lagos, nayi magana dasu, saboda muhimmancin abinda zan tattauna daku zasu biyo tanan".
Kallon Hajiya Inna yayi yace "Hajiya ko akwai abinda ki ke san fad'a".
Tace "eh ina da abin fad'a". yace "to muna saura ranki".
Tace " 'Karami". Haka Inna ke kiran Daddy karami "ni abinda ke damu na yadda, Garba ya tsani Siddi'ka, kamar ba 'kanwar sa ba, Kaf 'kauyen nan babu wanda bai san da zaman 'kiyar-yar Siddi'ka a gun Garba ba, a gaban kowa nuna wa yake, a gida bai 'kyale ta ba, motsi kad'an tayi ya make ta".
Wani gwaran numfashi Daddy ya sauke, sannan ya fara yiwa Yaya Sadeeq fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba sosai Daddy yayi wa yaya Sadeeq fata fata
Sannan ya maida kallan sa I zuwa ga Momy yace "Aisha fa kina da abin da zaki ce".
murmushi tayi irin na su na manya tace "ai kai da Hajiya kun gama fad'an duk abinda zan fad'a, sai dai a'kara yiwa sadeeq fad'a a kuma ja mai kunne, sai muyi musa fatan Allah yasa alkairi".
"Ameeen" Inna tace yayin da Daddy yace "alhamdu lillah".
Daddy yace "mai sunan manya matso nan kusa dani kinji". Jikina a sanya ye na matsa kusa na zauna a d'ayan bangaren da ke kallon yaya Sadeeq sai ban kamin harara yake a sace
nayi kamar bansan yanayi ba
Dafa kaina Daddy yayi yace "Allah yayi miki albarka". "ameen". Nace
Sannan yaci gaba da cewa". Siddeeqah daga yau yayan ki Sadeeq zai dunga amsa matsayi buyu a gurin ki wato yayan ki kuma mijin ki insha Allah yau ne zan aiwatar da abinda nasan kanwata zatai farinciki dashi wato auran ki da Sadeeq"
duk da ban wani san maye *Aure* ba amma naji sam ba aimin adalci ba
a tare nida yah Sadeeq muka mi'ke tsaye, duk kannin mu idan mu a waje alamar rashin fahim ta.
" Koma ku zauna" Daddy ya fad'a, jikin mu babu 'kwari haka muka koma muka zauna, Khadija ma dake zaune mamaki ne yacika ta shiko Umar ko ajikin sa Inna kuwa da Momy daman sun san da batun
"'Kwarai kuwa abinda kukaji nafad'a haka ne ba mafarki kuke yiba, domin wannan shine burin 'kan wata Aminatu". 'Kwalla ce ta cika idonun sa yayin da ya kasa 'karasa maganar Handkerchief yaciro cikin aljihun sa yana share 'kwallar da ta zubo masa
Da irin murayan kuka, Daddy ya cigaba da cewa "auren ki da Sadeeq shine burin ta, bamu sani ba ko a raye take ko amace, kimanin shekaru goma sha biyu da wasu yan wattani akai kenan tun tana goyen ki". ya nuna ni "nasan kunsan komai ba sai na 'kara tada muku da zancen ba, saboda bana son na tada mana hankula".
tuni inna tafara shash-she 'kar kuka Momy ce keta faman bata ha'kuri
Da 'kyar aka shawo kan Inna tayi shuru
Ba 'karya Dady yayi ba duka family an san labarin 'batar mahaifiya ta amma bamu san yadda al'amarin ya faru ba
Daddy yaci gaba da fad'in "Siddi'ka sai dai kiyi ha'kuri, naje har gidan ku da 'kyar nasa mu ganin mahaifin ki, na je masa da batun auren ki, yace min shi babu ruwan sa yama manta dake cikin 'ya'yan sa ba tun yauba ai ya fad'a mana ya bar mana ke, idan yanka ki zamu yi, muyi, shi baya da matsala babu ruwan sa". ya 'kara da cewa ai tun ranar da Amina tabar gidan nan na manta da duk wani abu da yashafe ta yanzu haka abinda yasa bazan sa karnuka su fidda min kaiba saboda baka sani ba, amma yanzu tunda kasani kada in'kara ganin ka akoafar gidana kai ba kai ba ko Siddi'ka d'iyata ce tazo sai nasa kar nuka suncin ye naman ta d'an ye, saboda haka Get out in my house".
jiki na babu 'kwari Siddi'ka na fito daka gidan ku
Ban ta'ba jin tsanar mahaifina irin na yauba kuka nike sosai ina tir da halayen sa kowa a d'akin jikin sa yayi sanyi Daddy ne ke shafa min kai yana bani hakuri
"Siddi'ka ki cigaba da ha'kuri Allah zai miki canji da mafi alkairi, ki cigaba da kai kukan ki gurin Allah saboda shi Allah baya barin zalinci". Kuma kamar yadda nace "yau za a d'aura miki aure da sadeeq idan anyi sallar juma'a babu fashi".
SADEEQ ne zaiyi magana Daddy ya katse sa da fad'in "zan sa'ba maka sadeeq, Ko na tambaye ka ne?".
bazan iya musa wa su Daddy ba, amma shin maye aure nashi ga uku nake fad'i a zuciya ta, yayin da nike jin bugun zuciya ta yana dad'a 'karuwa
NI DA YAYA SADEEQ
بسم الله الرحمن الرحيم