← Book details nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 29 OF 31

Chapter 32

nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

______Koda na sauko zaune na samu su Easha da Dady karami da Umar afalo suna wasa, bayan na zauna, na shiga tambayar su Ina su Ammi Little Easha tace "suna dakin Momy".


"to" nace na mike na nufi part din Momy baki na dauke da sallama na kusa kai, a zaune na same su cikin dan karamin falon ta. Da alamar tattaunawa suke, nan kasa na zauna gurin Daddy nace "Daddy ina yini bamu gaisa ba "

Yace "lafiya lau Siddeeqah ya makarantar?"


"lafiya lau Daddy"

Yace "an kare ko yanzu sai cigaba?"


Nace "eh Daddy amma gaskiya ba makarantar kwana zan koma ba na gaji"


Yace "to shikenan nima nayi tunanin haka, kuma lokaci yayi da zaki tare a gidan mijin ki in yaso sai ki cigaba da karatun acan" kaina a kasa ni dai ban
ce komai ba, na mike ina tambayar Momy Khadija, tace ta aiketa gidan kawar ta Hajiya Nafisa ," to" nace nan na bar su na fito, kitchen na shiga dan na taya Suwaiba aikace-aikacen kayan shan ruwa dan naga kamar aikin zai mata yawa ita kadai, munayi ina mata firar makaranta, a haka Ummi da Fadeela suka isko mu.

Muna nan kitchen din Sadiya tazo tai mana sallama direban su yazo daukar ta, nace mata "sai mun hadu a Dande"

"to" tace tana dariya ta tafi

da dare misalin karfe 10:00 pm dukkanin mu zaune muke harda yah Sadeeq, da yah Mubarak wato yayan Ummi, kuma shine zai auri khadija, tun wata biyu da suka wuce ya kare karatun sa a harkar computer, yanzu haka aiki yake a karka shin wani company, kowannen mu kagani fuskar sa dauke da annuri, Ammi ce tace "Yaya Ali wai yaushe zamu je Dande ne dan na kosa naga Inna na wallahi nayi kewar ta" yana Murmushi yace "ki kwantar da hankalin ki nan da Jibi ma sai mutafi in yaso dukkan ku sai kuyi sallah acan tunda sallar saura kwana biyar, dakanan ma ayi maganar tarewar yarinyar nan da kuma bikin Su Khadija"


Ammi tace "to shikenan Allah ya kaimu"


Da lokaci bacci yai nace "dole Ammi a dakina zata kwana"

itama dama tana son kebewa da diyar tata, yayin da Fadeela tace ita A dakin Ummi zata kwana saboda jinin su ya hadu , Jiddah kuwa tace ita da Little Easha zata kwana dan itama jinin su ya hadu, Dady karami kuwa cewa yai tare da Umar shi zai kwana, Khadija na dariya tace yanzu ni ba Wanda zai kwana dani ai shikenan, sai mun hadu da asuba "

Tana gama fadar haka ta haura sama, muma da daidai da daidai mukai ta watsewa.


Nida Ammi a daki fira muka dasa ta tsakanin 'ya da uwa ina kwance kan cinyar ta nike ce mata" Ammi wallahi Abba na bai da mutunci kamar bashine ya haife ni ba" Ammi tai saurin toshe min baki tace "ki daina fadin haka koma yaya ne dole ki bashi kima da daraja saboda shi din mahaifin ki ne" na ce amma fa Ammi tun nataso ban sanshi ba ban taba ganin shi ba, bai taba turo dai dai da naira goma yace a saimin sabukun wanki ba, Daddy ne ya tsaya min tsayin daka akan komai na rayuwa ta, sai Momy Allah yai mata Albarka wallahi tana kula dani, ko ita ta haife ni sai haka dan ba'a taba nuna min banbanci a gidan nan ba, haka fa lokacin Aure na da Daddy yaje kar kiga yanda Abba na yaci mai mutunci nan dai ta kwashe labarin komai ta fada mata, idon ta cike da kwalla take ce min "nayi hakuri ba yin kansa bane asiri ne amma Abba na yana mutukar so da kauna ta insha Allah nan bada jimawa ba komai zai zo karshe".


Bayan kwana biyu ya kama ranar zamu je Dande lokacin Sallah sauran kwana Uku da misalin karfe goma na safe dukkanin mu a farke muke kowa sai shiri yake bayan mun gama shirya wa, mota uku mukayi da Ammi da Momy da Daddy babba da Umar da karamin Daddy mota guda suka shiga, yayin da Khadija da Jiddah da little Easha suka shiga motar yah Mubarak, ni da Ummi kuwa motar yah Sadeeq muka shiga inda na zauna gidan gaba Ummi na gidan baya muka dauki hanyar Dande sosai yah Sadeeq ke tsulala gudu ahanya, na lura dashi yana son gudu a mota, mu dai Allah ne ya sauke mu lafiya, duk da idan nai hutu ina zuwa Dande amma ba laifi ta dan samu canji dan yanzu haka ana basu wutar nefa kuma asbitin bayan gari an dan gyara shi, a kofar gidan Inna mukai farking da futuwar mu yaran unguwa akai ta kallon mu ana ga yan Indian nan sun zo, sau tari dama ni haka suke ce min yar indiya, dayin fakin din mu, sai ga motar yah Mubarak nan shima ya danno kai, muna kokarin shiga saiga motar Daddy nan ita ma ta kunno kai haka muka dunguma gunin ban sha'awa da burgewa yaran layi kuwa sai kallon mu suke,

Bakin mu dauke da sallama muka shiga, babu kowa a tsakar gidan saboda haka muka dunguma cikin falon Hajiya Inna, a zaune take tana kallon talabijin "tsohuwa mai ran karfe" na fada yayin da na isa gare ta na fada kan cinyar ta.


Tana dariya ta baka min duka tace "dagani ja'ira kada ki karasa ni"

Turo dan karamin baki na nai nace "inna ki dai ji tsoron Allah yanzu ni ina naga nauyin da zan karya ki"


Kallon mu inna ta shiga yi daya bayan daya kana tace "Karami wa nike gani wannan kamar Amina na? Ko ido na ne kuma wa'innan yaran na waye?". Wato su little Easha da Fadeela take nunawa.


TA dora da cewa "ko tsufan nawa ne yake rudar dani Karami?". Ta ambaci sunan Daddy 1


Da gudu Ammi ta isa ga Inna ta rungume ta tana cewa "nice Inna nice Aminan ki ce"


Sai hawaye shar-shar yai ta zuba daga idanun inna jikin su Daddy yai mutakar sanyaye suka samu guri suka zauna

Inna sai sumbatu take tana cewa "ashe da rabon mu gana ashe da rabon zan sake ganin ki, bayan wa'innan shekarun, dama ni ban fidda rai ba kullum cikin addua nike ina rokon Allah idan kina raye Allah ya bayayyana mana da ke, Allah maji rokon bayin sa gashi ya amsa mana, jikin kowa yai sanyi nan mukai ta taya Inna kuka ba mai lallashin wani saida mukai mai isar mu, sannan mukai shiru,


Cikin kuka mai tsuma zukata, Ammi tace "Inna ku yafe min nasan na tafi na barku cikin matsanancin tashin hankali nima ba a san raina nayi ba, alokacin ban san inda hankali na yake ba, ni dai nasan kafin faruwar abun Habiba kiyasha ta tazo daki na, ina hada ido da ita naji gabana yai mummunan faduwa daga nan tace min "dauki shegiyar yarinyar ki ki kaima uwar ki banason na kara ganin ki arayuwa ta ki tafi nesa da wannan garin, sai na same ni da bin umarnin ta ban dauki komai ba sai mayafi na, na saba Siddeeqah a kafada na fito, a harabar gidan naga Alhaji Sulaiman, kallo daya na masa naji na tsane sa, haka na wuto shi yana so yai min magana kuma ya kasa, idon sa cike da kwalla na bude get na fito, ban zarce ko ina ba sai gidan ki Inna kina gani nana ki ka shiga tambaya ta lafiya? Me yasameni amma ban ce miki uffan ba na aje miki Siddiqah na fito, tafiya nai mai nisa da kafa ba tare da nasan inda na dosa ba, yamma ta fara yi saboda haka dare ya fara lillbe yini nagaji ga yunwa ga kishin ruwa, nan na zube a kasa gefan kwalta, wani mai mota ne yazo wucewa da ya ganni ya taimaka ya dauke ni, bayan ya sakani a mota asbiti ya kaini, bayan sun gama duk wani gwaje gwajen su basu ga komai a tare dani ba illah yar yunwar da ta galabaitar dani, kwana na biyu a asbiti aka sallame ni, wannan mutumin ya dauke ni kamin nan tun a asbiti yake tambaya ta, akan ya suna na kuma ina ahali na, amma babu uhm babu uhm uhm, sai dai nai ta bin sa da ido, hakan yasa ya fahimci ba kalau nike ba, da yike babban malami ne, shine fa ya dauke ni ya kaini gidan sa gurin matan sa anan garin katsuna, inda sukai ta nema min magani har Allah cikin ikon sa ya bani lafiya, bayan na dauki tsayin sheru bana ko magana, to bayan na warke na dawo hayyaci na ya tambaye ni ahali na ko suna ina, sai na tsinci kaina da ce mai bani da kowa sai Allah sai kuma kai, to bayan kwana biyu yazo min da maganar aure, nace masa ni da ba fita nike ba ina zan samu muji?" yace" indai wannan ne bashida matsala zai samo min mijin aure na kirki wanda zai rike ni amana "


Bayan sati guda ina zaune a daki na sai gashi yazo yake cemin" ya daura min aure, yanzu haka tare da mijin nawa yazo kuma dani zai tafi saboda haka na tashi na shirya "

Haka dai na baro gidan Mlm liman ba dan raina yaso ba nabi Alhaji Imran, wato baban yarannan


Ammi ta fada tana nuna su Fadeela


TA dora da cewa, nayi zama na amana da margayi, yana yawan tambaya na Ahalina amma sai nace" ni bani da kowa ".

Na rasa kuma dalilin da yasa nike cewa haka dan ko tunanin wani nawa ma banayi, cikin ikon Allah na haifi yarana yan biyu mace da namiji masu kama da Daddyn su, ya tambayeni shawara akan sunan da zamu sa musu nace" Asa min Aisha da Aliyu ".


Haka rayuwa ta cigaba bayan wasu shekaru ina zaune a office dina saiga Sadeeq da Siddeeqah nan sun shigo, tunda na kalle su na fara tuno da iyali na kuma naji ina kwadayin na sake haduwa dasu, tunda naga Sadeeq naji a jiki na dana ne haka itama Siddeeqah, sai naja ta ajiki na ta yadda take yawan bani labarin ku, hakan yasa na kara tabbatar da tabbas ita din jini na ce, amma sai ban taba nuna mata ba, nasha tambayar ta ina mahaifiyar ta? " sai tace min" mahaifiyata ta bata tun ina yar karama kuma har yanzu bamu san inda take ba " hakan yasa na kara jin kwarin gwuiwa shine fa da akai hutu nace ta bari zan kai ta".

Ta numfasa tace "wannan shine takaitaccan abun da ya faru bayan rabuwa ta daku".


Inna tace" wannan fa?"

Fadeela take nufi


Ammi tace" marainiya ce mahaifiyar ta ta rasu wajan haihuwar ta, kuma yayar su Easha ce da suke uba daya".


Daddy yace "naji kina cewa margayi yanzu shi Alhaji Imran din ya rasu?".


Wasu hawaye ne masu zafi suka zobo wa Ammi tace "eh ya rasu a sakamakon hadarin mota da yai".


"Allah ya jikan sa su Daddy suka ce"


Wannan kenan

Bayan ko mai ya lafa Ammi da Momy suka tambayi inna abinda za'a sha ruwa dashi?

Tace su bari Garba ya siyo tunda yanzu yamma tayi, ga gajiyar mota

Bayan kwana biyu ya kama jajibari, mayafi na na saba nace "Inna zan fita" tace "zuwa ina kuma keda ba kya iya zama a guri daya?"


"gidan Ladiyo man tun nazo ban leka ta ba fa".


"to a dawo lafiya" inna ta fada ni kuma na fice a buna


A soro naci karo da Yah Sadeeq, bayan ya kare mun kallo yace" ina zuwa?".

nace" gidan kawata Ladiyo zani ".

" kuma da izinin wa" ya jefo min tambayar


"inna mana" na fada a takaice


"to bazaki ba ki koma".


Kallon in ka isa na mai na fice a bi na


karasawa cikin gidan yai ransa a mutukar bace ya fara masifa saboda duk suna tsakar gidan, fadi yake "wai Inna akan me zaki bama yarinyar nan dama ta dunga gantali, da aure na a kanta".

Momy ce tai caraf tace "eh lalle ma Sadeeq, yanzu ne kasan da ita din matar ka ce yanzu ne kaje jin haushin yawon da take yi? To tun wuri ka fita ido na bazaka takura ma yarinya ba".


Ammi da ke wanke wakan da za'a kosai dashi tace "Haba Momyn yara ai da gaskiyar sa, tunda shi ba sakaran na miji bane taya zai bar iyalin sa sakaka a gari? Ina goyan bayan sa kuma bari ta dawo sai naci mutuncin ta, na kara ganin ta fita ba da izinin sa ba


Please
Comment
Share

NI DA YAYA SADEEQ

•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•

No editing
Chapter 29 · 0% Book details