← Book details nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 31

Chapter 18

nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

______"haba Momy 'yar wannan abar ce zan fita da ita a matsayin iyali na?".
"Eh Ita d'in fa wallahi Sadeeq ka kiyaye ni ka raina ni ko? Duk abinda nike fad'a maka abanza nike fad'i saboda baka d'auka".
"Momy dan Allah kiyakuri na daina ki ce mata ta wuce mu tafi".
"Au bakin ka ciwo yake da bazaka  fad'a mata ba kai? Ko kafi 'karfi ne? Sadeeq ina raba ka da kiwan kyalla kana shige wa kyallah ta haihu". Momy ta fad'i haka cikin dakiya da tsitstsire sa da ido
Kame kame ya fara

Siddeeqah da taji haka tace "Momy sai mun dawo".

"to adawo lafiya 'yar albarka".

Harabar gidan ta fito  taja ta d'an tsaya kamin yayan nata ya fito su wuce,

adai dai lokacin mlm Habu ya wangele get motar su Jiddah ta silalo ciki idi driver ya samu guri yayi faking kana ya fito ya bude musu murfin motar Khadeeja ce ta fara fitowa sai Umar ya fito saida Khadeeja ta zura kan ta da hannayen ta a cikin motar ta kamo Jiddah da kyar Jiddahn ta iya fito wa tana ciccin magani, saboda yadda take jin zuciyar ta na mata daci da radadi akan dukan da Siddeeqah ta mata, ita kadai tasan kalan tanajin cin mutuncin da tayiwa Siddeeqah.

kallo daya Siddeeqah ta musu ta kawar da kan ta gefe tana dariya ciki ciki saboda yadda taga bakin Jiddah ya yi sun tumeme
Sadeeq ne ya fito shima ganin Siddeeqah na dariya ita kad'ai abin ya bashi mamaki yana shirin daka mata tsawa sai ya hangi Khadija rike da hannunan Jiddah Umar na biye da su suna taho wa
Kallo na yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya yi gaba abin sa cikin sauri nima na mara masa baya ba tare da na lura ba naji na ci karo da mutum a tsorace na ja da baya ina yarfe hannu na, ganin Jiddah ce na bige "mttsssss" na ja wani dogon tsaki naga sanda Khadija ta yi mata magana da alamar dai mantuwa tayi a mota saboda naga cikin motar ta koma  Idan jidda yayi 'kwala 'kwala murayan ta na rawa tace "wallahi zaki san kin ta'ba ni yarinya zan nuna miki kalar nawa rashin mutuncin banziya d'iyar shegu ke idan....".
"Tas tas". shine 'karan marin da Sadeeq ya wanke Jiddah da shi yana wuci yace "kada na kara jin kin ce mata shegiya duk lalacewar naka naka ne saboda hannun ka bai ru'bewa ka yanke ka wurgar ita d'in jinjin ki ce nasan kin San da haka. 'bace min dagani kafin na 'ba'b'ballaki".

Jiddah kusan suman tsaye tayi saboda yadda taji saukar marin batayi zata ba lura Sadeeq yayi da Jiddahn bata cikin hayyacin ta d'an ta'be baki yayi ala mun ko a jinkin sa, kana ya kallo ni nayi sauri nayi 'kasa da kai, zaki wuce mu tafi ko sai na had'a dake munafuka kidinga yin abu sumi sumi to ki kaddara aure na dake... ".

Bai 'karasa maganar ba kira ya shigo a wayar sa laluba aljihun sa yayi ya fiddo batare da ya kalli sunan mai kiran sa ba yayi picking call d'in gami da karawa a kunnen sa sannan yayafito ni da hannu ya yi gaba. Sai a lokacin Khadeeja ta iso kallo na take yi nima da kallon na bita yaya Sadeeq har ya shiga mota, nima bu'de gidan baya nayi na shiga na zauna, sai Sadeeq d'in ya waigo fuskar sa a murtuke yace "ke uban waye diraiban ki zaki dawo gaba ki zauna ko saina miki tsinannan duka".
"uhm" na fad'a kana na dawo gaban motar. Habu mai gadi ya buɗe masa get ya fice daga gidan

Khadija na taba Jiddah tayi luuuuu zata zube a 'kasa cikin hanzari Khadeeja ta mai do ta kirjinta ta rungumeta mamaki kwance akan fuskar Umar yace "wai aunty Khadija mai yasameta ni ma yan zu na dawo kina tafiya nima naje gurin Habu mai gadi". Cikin kuka Khadija tace "Umar wannan wace kalar rayuwa ce daga wannan sai wannan gaskiya ni na gaji Zan roki Daddy ya barni na koma kaduna da zama wallahi bana son tashin hankali, nasan ita da Siddeeqah ne ko yaya tunda ina zuwa suka bar gurin". Ta 'karasa fad'a tana rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

Tana kokarin kama Jiddah sai ga Daddy ya fito da alamar masallaci zai je soboda ankira sallar Azahar, hannun sa d'auke da gorar ruwa ta faro, hango 'ya'yan sa daya yi cikin wani hali yasa shi karasa wa gurin su da sauri

Allah sarki mahaifan mu  ko mai zamuyi musu bazamu taba biyan su ba saidai muyi musu adduar Allah ya yafe musu yayi musu sakaiya da gidan aljanna fiddausi 🙏

"Khadija mai yasameta nehaka? na gan ku cikin tashin hankali". Daddy ya tamabaye ta

Murayan Khadeeja na rawa cikin kuka tace "Daddy wallahi nima ban sani ba yanzu muka dawo daga asbiti shine na barta anan na koma mota dauko magun-gunan da aka bamu, nan dai Khadija ta kwashe labarin abin da ta sani ta fad'awa Daddy gorar ruwar  hanun sa ya bude murfin ta ya zuba rawa a tafin hannun sa ya watsa wa Jiddah a fuskar ta nan take taja dogon numfashi ta sauke 'kirjin ta na bugawa da sauri da sauri kara rungume 'yar  uwar ta tayi tana sauke ajiyar zuciya ganin ta farfado yasa Daddy cewa "ku shiga daga ciki Umar zo mu tafi masallaci". "To Daddy".

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Aban garen Sadeeq kuwa wani 'katon plaza ya kai ni mai kyau da tsari bakin Siddeeqah a sake take kallon gurin saboda ita tun da take bata ta'ba ganin kasuwa mai kyau irin wannan ba badan taga basuyi tafiya mai nisa ba da sai tace kasar ya bari da ita yana gaba tana bin sa a baya har suka isa daidai bakin wani 'katon shago mai dauke da kofar gilas tafke ke irin wacce na ciki yake ganin na waje amma shi na waje baya ganin na ciki

Wani abun Sadeeq ya danna a jikin bangon shagon can sai ga wata mata ta fito da ganin ta ba bahaushiya bace saboda a kwai 'karin gashi a kanta kuma babu mayafi a jikin ta rigar ta irin mara hannu ce sai wani d'an gajeren sikel da take sanya dashi, da turan ci Sadeeq yayi mata magana itama ta mayar masa bayan sun gama naga ya ciro kudade masu yawa ya mika mata ta amsa tana godiya yace "bita mana kika saki baki da hanci kina kollo na kamar yau kika taba gani na".

Bayan sun shiga daga ciki Siddeeqah ta ga Mata a zazzaune akan kujeru masu kyau da burgewa wasu kuma an saka musu kan su a cikin wani inji yana kara wuuuu haka dai Siddeeqah tai tabin gurin da kallo kamin ta zauna a kan wata kujera da babu kowa , tsoro ne fal a cikin ranta saboda yadda taga ana sa mutum cikin inji gaskiya ita baza ta yarda a sata ba aje a fille mata kai ana zaune 'kalau da ido matan gurin suke kallon ta ganin ta suke kamar balarabiya wata a cikin su ce tayi karambani tace "sannu baiwar Allah".
Kallon ta Siddeeqah tayi sai taga babbar maca ce saboda a kalla zata kai shekara 30 a duniya
Adan dakile tace "yauwa sannu Aunty". Saida gaba daya matan gurin suka kalli junan su saboda yadda suka ji muryan ta sanyi ga dadi haruffa suna fita dai dai kamar koyan hausar tayi masha Allah

Saida aka gama ma wasu mata sannan layi yazo kaina mai saloon din ta dube ni "kanwar oga taso ki zo layi yazo kanki".
A tsorace Siddeeqah ta tashi tace "amma ni dan Allah kada ku sani a cikin wancen injin ku wanke mun kaina kawai haka".

"To bazamu saki ba tashi muje" mai saloon tace

Bayan wasu mintocin da basu haura talatin ba saiga shi Siddeeqah ta fito das da ita an gyara mata kanta har kyalli yake bayan kamshin da yake tashi asalin kyanta ya kara baiyayana masha Allah a gaban katon madubi ta tsaya tana kallon yadda aka gyara mata gashin  duk tsayin sa da cikar sa anmayar dashi guri daya anyi mata faking a tsikayar kai sai shafa kan take tana murmushi saboda ita kanta tasan tayi kyau. Mai kula da gurin ce tazo tace "kan war oga ya dawo yace kizo ku tafi".
"to". Na ce na yafa mayafi na ta zuge min glass na futo

A jikin motar sa na hango sa hannayen sa dore akan kirjin sa ya zuba min idanu kamar wani maye😅 da ni ke kallon sa haka da yace "uban me nike kallo". ahankali na karaso inda yake bai ce min komai ba ya zagaya yashiga nima na shiga ahanya ya kunna mana karatun alkur'ani mai girma muna saurara naji na kara samun natsuwa sosai kuma hankali na ya kwanta gaskiya alkur'ani rahama ne a tare damu saboda yadda yake samara da bayin Allah nutsuwa da kwanciyar hankali.

Cikin wata unguwa ya shiga damu mai gidaje iri daya A bakin get din wani gida naga yayi faking sannan ya dauko wayar sa ya dade yana danne danne yana dariya harda yin kiss a wayar ni dai ban ga ya kira kowa ba sai na ga ya aje wayar

Can sai ga Zuby ta fito sanya da d'ikin atamfa riga da siket amma irin dinkin nan ne da ake cemai jahannama ga fasinja saboda komai na jikin ta ya bayyana mayafin ta a kafada ta doro shi bakin ta dauke da cingom tana taunawa yana kas

Tabe baki Siddeeqah tayi kana Ta cigaba da da kallon ikon Allah

Bangaren da nike tazo ta bud'e gani na da tayi a ciki yasa tayi turus harara ta wurgomin taja dogon tsaki ta maida murfin ta rufe, cikin masifa ta dawo bangaren da Sadeeq yake tana jijjiga kafa

Tace "wace ce wannan ka kwaso Sadeeq? kamar aljana ko gamo nayi ni Nike ganin ta kai baka ganin ta?".

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Ina mai baku hakuri akan rashin jina da kuke yi a

Ina godiya da yadda kuke nuna min kauna Allah yabar mu tare ya hada fuskokin mu a cikin aljanna fiddausi

Dan Allah duk wanda yake karanta min book yayi kokari ya dunga yimin comment da share nagode taku har kullum
*Siddeeqatul khairy Yahya * (S beauty✍️)


NI DA YAYA SADEEQ

Story and Writer by
Siddeeqatul khairy Yahya
( *S beauty*✍️)

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Page 19

______dawo da kallan sa yayi izuwa gare ni ya wurga min harara kana ya kalli Zuby da take cika tana ba tsewa saida ya saki fuskar sa ya fad'ad'a ta da Murmushi yace "uwar gida sarautar mata duk kishin ne haka ko gaisawa kin ki bari muyi ki kwantar da hankalin ki akan wannan abar". Ya nuna mata ni da hannu kana ya cigaba da cewa "ina da ke mai zanyi da ita ko baki kare mata kallo bane? Ko matan duniya sun kare bazan so wannan abar ba danni kallon na miji nike mata".
Muryan Zuby a dakushe tace "to maye halakar ka da ita? da zaka zo gurina sai kazo da ita, ni wallahi har kasa naji na tsane ta saboda ko macen kuda bana son tarabeka bare kuma macen da halakar aure zai iya shiga tsakanin ku, ina kishin ka ina yi maka son da bazan iya kwatan ta maka ba idanuwa basa iya ganin sa dan Allah Sadeeq kada ka ci amana ta, ka soni koda rabin son da nike maka ne ". Idan Zuby har ya cika da kwalla, Sadeeq kuwa jikin sa yayi sanyi a ransa yake shawara "shin ya fad'a wa Zuby matsayin Siddeeqah a wurin sa ko kuwa yayi mata karya". saboda ya hango tsantsar kishin sa da 'kiyayyar Siddeeqah acikin 'kwayar idanun ta gwauran numfashi ya sauke yace "Baby ki kwantar da hankalin ki 'diyar mai gadin mu ce fa".
Kallon sa Siddeeqah tayi suka had'a ido ta tintsire da dariya tace "saboda ka wulakanta ni zakace diyar mai gadin gidan ku ce ni?, to badiyar mai gadi bace kadai fadi wani".
A fusace ya daga hannu zai kwada min mari, Zuby tai saurin ce masa "abinda ta fad'a gaskiya ne shiyasa zaka dake ta na shiga uku Ni Zubadah Sadeeq mai kake nufi dani?".
"ki saurare ni baby wannan yarinyar da kike gani munafuka ce idan kuma kin yarda da abinda ta fad'a shikenan amma ni iyakar gaskiya ta na fad'a miki".
"haba Sadeeq da ganin wannan yarinyar ba d'iyar mai gadi bace jibe ta fa da larabawa take kama fatar jikin ta luwai luwai, wai ka ta'ba kare mata kollo kuwa dan Allah Sadeeq ka kalle ta yanzu". Wai gowa yayi ya kalleni na tsawan wasu yan sakonni kana ya cigaba da kallon Zuby, mi'ko masa wayar ta tayi tashiga camera tace "kaima kalli kan ka ka gani". Sadeeq bai fahimci inda Zuby ta dosa ba shidai kawai biye mata yake, bayan ya kalli kansa ya mi'ka mata wayar, tace "ina fatan ka fahimci inda na dosa yanzu?".
Kai ya girgiza mata alamar bai fahimci komai ba tace "ina son ka fad'a min maye Alakar ka da 'yar mai gadi da har kake kama da ita? Wallahi ko alqur'ani aka bani zan dafa ita d'in jinin ka ce Sadeeq maiyasa kayimin kar...".
Tsawa ya daka mata gami da cewa "ke ashe bakida hankali? ni zaki duba tsabar ido na kice min makaryaci tabbas zan nuna miki kuskuren ki".
Sai yanzu Zuby taga rashin dacewar abinda tayi a fusace Sadeeq yayi ribas Zuby na kwala masa kira, amma ina ransa ya riga ya baci figar motar yayi sosai yake gudu akan titi saura kiris ya daki wata mota da ta fito daga wani layi zata hau titi sai Allah ya takaita abun yayi sauri ya ci burki idanuwan Siddeeqah sun yi kulu kulu tsoran ta kada yaje ya kashe ta tasan ya kashe banza wayar sa ce ta fara ringing amma ko ta kanta bai bi ba koda yazo bakin get din gidan su sosai yake danna horn mai gadi a tsoroce ya leko ganin yallabai ne yasa yayi sauri ya wangale masa get din acikin ran Habu yake cewa "ko waya tabo yallabai yau?".
Bayan Sadeeq ya sulala motar sa cikin gidan, yanemi waje yai faking da sauri Siddeeqah ta kai hannun ta da niyar ta bude motar ta fita sai taji ta a kulle gam, alokacin Sadeeq ya hada kansa da sitiyarin mota tsoro ne fal acikin zuciyar ta, tana jin yadda zuciyar Sadeeq ke harbawa da sauri da sauri ahalin yanzu tasan ko sunan sa ta kira shake mata wuya zaiyi komawa tai ta zauna itama tayi tagumi hawaye na saukar mata da batasan dalilin zuwan su ba


*Dan Allah duk wanda ya karanta yayi min comment da shera ngd*


NI DA YAYA SADEEQ
                  

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
Chapter 16 · 0% Book details