CHAPTER 27
nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read
"lafiya naga duk kin rasa nutsuwar ki lokaci guda ko wata maganar Abban ya fad'a miki?".
Mama ta tambayi Zuby dake faman safa da marwa a falo dayan hannun ta dafe da goshin ta saboda jirin da take gani.
Cikin sauri Zuby ta juyo ta kalli Mama tace "ina lafiya Mama wallahi ni mutuwa zanyi bana son Maheer Mama ki taimaka min idan Abba yace sai na aure sa mutuwa zan yi".
A dai dai lakacin Abba ya fito daga bedroom din sa da jaka trolley yana ja yar karama, da alamar tafiya zai yi, yaji duka abinda Zubaidan ta fada ransa na suya yace "aikuwa sai dai ki mutu amma ko gawar ki ce sai an kaita gidan Maheer zan can banza zan can hofi, duk laifin ki ne Mariya" ya fad'a yana maida duban sa gare ta "ke kika bata yarinyar nan amma gabaki dayan ku zanyi maganin ku bari na dawo tafiya, kuma kufara shirye shiryen biki daga yanzu zuwa kowani lokaci za'a daura aure". Yana gama fadar haka ya fice abun sa,
Maganar da yayi da Kamal jiya ta kara dawo mai sabuwa fil yaji kamar yanzu ake fada masa ita, take zuciyar sa ta fara kuna da radadi tabbas ka haifi d'a ne amma baka haifi halin sa ba, idan kuwa hakane Mariya ta dade tana raina masa hankali amma ya godewa Allah da jiya Kamal ya ganar dashi, shi dama ya dade yana zargin da akwai abinda suke boye masa ya bari ne saboda yasan dole wataran asirin su zai tonu, ya kuduri aniyar sa ido sosai akan ta saboda yagano abinda take aikata wa, aran sa yace "ya tabbata Mariya ce ta Lalata yarinyar saboda duk wani abu da take yi da sanin ta take aikatawa, tabbas idan ya gono ba abun arziki bane kashin Mariya ya bushe dan san da zai bata Zubaidan tayi alkawarin bata tarbiya kamar diyar da ta haifa ta cikin ta da haka ya kawar da tunanin ya shiga cikin mota ya bata wuta.
hhhmmmm idan Abba yasan munanan abun da take aikata wa ya zaiji acikin ransa kuma wani mataki zai dauka akan Mama Mariya ? Kudai cigaba da bina sannu ahankali ganin yanda labarin zai kaya
* * * * * *
Da misalin 9:45 Farooq ne a bakin get din su Sadeeq inda yake dannawa mai gadi hon, da sauri mai gadi ya taso daga kan kujerar sa ya zo ya dan leka ta kofa ganin Farooq ya leko yana daga hannu yasa mai gadi yai sauri yazo ya wangle gate din, yana fadin "yallabai yau kai ne a gidan namu sannun da zuwa gaskiya ka sha hanya kayi sa'a yallabai kuwa yana gida bai fita ba". Shi dai Farooq bai tanka masa ba ya sulala da motar sa kana ya nemi guri yai fakin, mai gadi ya maida get din ya rufe yana kara jinjinawa Farooq hannu.
Jim kadan ya kashe motar ya fito,
A dai dai lokacin ni kuma na fito zan je na kaiwa mai gadi wasu kaya da Daddy yace na bashi, ina ganin sa na karasa gurin sa baki na dauke da Murmushi nace "laa! Yaya Farooq yau kaine agarin namu, aradun Allah naji dadin ganin ka dama na gaji da zaman garin nan yanda kasan ina kur-kuku haka nike jina, kafa ta kafar ka sai na bika mun tafi Dan de".
Yana dariya yace "to yar Inna keda zaki tafi makaranta ina ke ina komawa kyauye ko bakya so ki zama yar birni ki dunga turanci ki waye ki zama babbar yarinya?".
Shiru nayi na yan sakwannin da baza su wuce biyu zuwa uku ba kana na ce "yaya Farooq kenan duka wa'innan abubuwan da ka lissafa ina so na zama ko dan na bawa yaya mamaki , amma saboda mugunta irin tasa makarantar kwana ya sama min kuma yace kai ne zaka kaini, ko kazo tafiya dani din ne?". na karasa maganar ina gyatsine da jijjiga kugu.
Dariya nabawa Farooq yanda yaga lokaci daya na canza yanayin magana ta zai yi magana nace" ban tari numfashin ka ba yaya amma ni babu inda zan bika mu tafi wata makarantar kwana, jeka ka dawo zanyi na kuma gayawa Daddy kuma ya yi na'am da batu na.
Dan yace " ma yaya Sadeeq in dai yana so ya kaini makarantar kwana to ya fara neman amincewa ta idan kuwa naki aminta sai dai fa ya kaini makarantar su Khadija".
Sajan sa Farooq ya shafa yace" ho ho ni Farooq yanzu ina shi Sadeeq din?". Tace" ban sani ba amma dai yana gida bai fita ba ".
" To maza je ki kai wannan sakon da aka aike ki kizo mu shiga gidan".
Nace "ban gane nazo mu shiga ba yah Farooq ni fa na fada maka in dai dan nice kazo gidan nan gwara ka koma dan bazan je ba, ba sai ka tsaya bata lokacin ka ba nasan bazaka rasa abin yi ba"
Ina gama fadar haka na wuce aiken da akai min, a zaune na gan sa hannun sa rike da radio kamar kullum ya kure volume kuma ya kara a kunnen sa, bai san nazo ba sai da yaji an kwace radio, a hasale ya jiyo ganin nice yai Murmushi yace " yar gidan Inna ya akai?" kayan hannu na na mika masa gami da fadin "wai me kake ji a radio ne? kullum da ita nike ganin ka kuma ka kure volume ko ciwan kunne baka ji".
Yace "banda abin ki yar Inna mai zan ji da ya wuce labaran dunya ai labaran duniya niki ji saboda yanzu lamarin kasar nan tamu abubuwa duk sun rukice sai addu'a".
Nace "hakane Allah ya kawo mana sauyi mafi alkairi ".
"amin" Yace gami da fadin "wannan kayan fa guga zan kai ko me?".
Nace "Daddy yace na kawo maka".
Ai kuwa yaji dadi sosoi dan kayan sabbi ne kala hudu haka dai na baro sa yana ta zabga godiya kamar wanda akace an gafar ta masa gabadaya zuniban sa.
A inda na bar sa anan na same sa tsaye da waya annu yana dannawa nace "baka tafi ba yah Farooq?".
"ina zani? ni da nike jiran ki mu shiga".
Nace "to shikenan tunda ka nace halan akwai abunda kake son yi muje".
Ina gaba yana baya har muka karasa cikin katafaron falon gidan in da naci karo da Sadeeq har saida ya ture ni, saboda shi zai fita ni kuma na kutsa kai abinka da mara nutsuwa, shi kuma ya dunfaro kofar ne cikin zafin nama, ihu na fara ina kiran sunan Daddy saboda kaina ya dan bugu da bango, shi kuwa yaya Sadeeq yayi tsaki sun fi biyar yana kara jin tsana ta a zuciyar sa yarinya sai tsinannan sharri to shi yanzu mai ya mata da take so ta tara mai jama'a?".
Daga kan da zaiyi sai yaga Farooq a tsaye jingine da jikin ban go ya harde yannayen sa a kirji sai Murmushin mugunta yake yi.
A hasale Sadeeq yace" malam maye?".
"Nishadi mana ko kar nayi?". Farooq ya fad'a still kuma yana dariyar sa
"kallon kanka ka rainawa hankali Sadeeq ya bi Farooq da shi kana yace bani wuri ni na wuce kana bata min lokaci".
A dai dai lokacin Momy ta fito tana fadin "yaya lafiya ke dawa".
Sam bata lura da Farooq ba sadeeq ta hanga a gurin aikuwa ta fara yi masa fada tana cewa "a haf ai nasan sai kai sarkin cin zali in dai kaji kukan yarinyar nan a gidan nan to ba kowa bane face kai".
Kallo na tayi tace ke tashi rabu dashi kiyi masa Allah ya isa tunda bazai daina ba Allah zai saka miki ".
Ina gunjin kuka na mike ina fiki fiki da idanu na ina kara matso kwalla a haka na haura sama na wuce daki na na kwanta a kan gado ina kallon sama ina jin zuciya ta babu dadi.
Farooq na shaafa keya yace" Momy ina kwana?".
Sai a lokacin Momy ta waigo inda yake fuskar ta a sake
Tace" lafiya lau Farooq yaushe kazo ne?".
Yace" shigowa ta kenan "
Tace" madallah ya Hajiyar taku?".
" Suna lafiya suna gaida ku".
"Masha Allah muna amsawa, kar dai tafiya da gimbiyar kazoyi ?". Ta tambaye sa
Yace "eh Momy".
Tace "bai fada maka ta fasa zuwa ba?".
"Eh bai fada min ba amma yanzu dana shigo kan na kara so cikin gidan na hadu da ita abakin get shine take sanar min cewa ta fasa zuwa".
Tace "yauwa sai kusan yadda za'ai dan Daddyn ku ya kusan gama shiryawa kuma yana so yaji matsaya ne kan ya tafi". Tana gama fadar haka ta bar falon.
A hankali Farooq ya kara so inda Sadeeq yake ya dafa kafadar sa yace "aboki na akwai matsala fa amma kana nuna kamar abin bai dame ka ba bayan kai ne mutum na farko daza ka fi kowa shiga damuwa idan har yarinyar nan tace baza ta ba. Ni wallahi mamaki kake bani yar wannan yarinyar ta gagare ka sarrafawa sai kace ba namijin duniya ba ko girman kan ne zai hana ka shaho kan ta? To idan shine zai fi kyau ka aje sa a gefe saboda.... ".
"dallah malam dakata ya kake magana kamar kana bani umarni nifa kaga wannan karatun da za tai kanta za tai mawa ba ni ba, saboda haka idan ma karatun ne tace bazatai ba kwata kwata ni ba damuwa ta bane, bayan ita zan iya auran gudu uku wa'inda suka fita komai, so kada ka tsaya bata yawun bakin ka ".
Farooq yace" nifa ba nufi na ka bata hakuri ba, ba kace yarinya ce bata da wayau ba kuma bata san komai ba, to ai shaho kanta ba zaiyi wahala ba shine nike so kayi mata yan dabaru
ko ka fasa kara auren ne?". Y
Yace" ban fasa ba amma kada ta gano ni fa kasan bana son raini".
"haba babu abinda zata gano kawai shiga ciki zan turo maka ita".
Yace "to shikenan kai anan zaka zauna?".
"eh".
Farooq ya fad'a yana mai samun kan kujera ya zauna yace "kasa a kawo min ruwa da dan abin tabawa".
"To" yace ya haura sama.
Khadija ce ta sauko bayan sun gaisa ta nufi kitchen ta hada masa kayan ciye ciye da ruwa kana ta dora akan katon tirai tazo ta aje masa akan tebur zata tashi yace "ina zuwa ki zauna muyi fira bana son zama shiru ni".
Komawa tai ta zauna ai kuwa nan Khadija tai ta basa labari yana kwasar dariya
* * * * * * *
Nan Abba ya bar Mama da Zuby cikin jimamin magan ganun sa, tabe baki Mama tayi ta kamo hannun Zuby suka zauna akan kujera tace" wai meke faruwa ne dan ni wallahi ban fahimci inda kalaman Abban ki ya dosa ba".
Sai da Zuby ta sauke gwauran numfashi kana tace "kina nufin Abba bai fada miki suna son su hada aure na da Maheer ba?". Tai maganar ne cikin sigar tambaya
Mama tace "bai fada min ba amma in dan wannan ne ki kwantar da hankalin ki ban ga aibun Maheer ba ni".
"Haba Mama ya kike so nayi da Soyayyar Sadeeq da take dawainiya dani? wallahi yanzu haka daurewa nike yi rabo na dashi tun jiya ko awaya bai kirani ba".
"shiyasa nace ki kwantar da hankalin ki yanzu ki fara shawo kan Sadeeq din daga baya sai musan yadda zamuyi da Abban naki".
"Mama kin San bamu da wannan lokacin kuma tabbas Abba da gaske yake, dan naga bacin ransa, wanda ban taba gani ba, wallahi ni ba wai Maheer din ne bana so ba tsoro nike kada asiri na ya tonu a silar auren sa da zanyi".
"Da wannan dan wannan" Mama ta fada tana sa hannu ta goge gumin daya keto mata a goshin ta , wani kallo Zuby ta bita dashi wanda ita kadai tasan ma'anar sa, kamin ta tashi ba tare da tace komai ba tanufi dakin ta, wayarta ta d'auka number Sadeeq ta shiga nema har sau uku tana kiran sa amma bai dauka ba
Shi kuwa Sadeeq zaune yake a dakin sa yana kallon kiran ta amma sai yaki dauka saboda ba karamin mamaki ta bashi jiyannan ba, gashi bata kirasa ba tun jiya bare ta basa hakuri shine yanzu zata kira sa tai masa dadin baki dan ta mayar dashi dan iska, Sam bazai dauka ba har sai tayi nadama yanda ko nan gaba baza ta maimaita makamancin sa ba.
Turo kafar dakin a kayi ko sallama batai ba ta shiga, a dai dai lokacin kiran Zubyn ya kara katsewa
Saida na turo dan karamin baki na nace "yaya gani yaya Farooq ne yace kana kira na".
Ganin yadda nike cika nike batsewa naba wa yaya dariya sai da yai Murmushin sa mai isar sa wanda yake kara baiyana ainihin kyawun sa yace "zo kiji magana zamuyi kika zo daure da dan kwali a kugu sai kace wacce tazo filin daga".
Sai alokacin na tuna da dan kwalin da naci damara dashi ni kaina dariya abun yabani saboda na dade ban yi hakan ba kwancewa na shiga yi yaya yace "a a ki bar abin ki ya miki kyau".
Dan nesa dashi ta zauna yace "ikon Allah wai ni kike gudu to bari ni nazo na same ki na fada miki ba dukan ki zanyi ba magana ce zamuyi ". Ya karasa maganar a lokacin da ya zauna kusa da ita hannayen ta ya kama gami da tallafo habar ta , hada ido sukai cikin sauri tayi kasa da nata, ba wai dan tasan kunya ba amma sai taga ya kara mata kwarjini bazata iya cigaba da kallon kwayar idon sa ba, shiko Sadeeq tausayin Siddeeqan ne ya kama shi a karo na farko a cikin rayuwar sa tun bayan ta fara tasowa, wallahi bai taba tunanin akwai ranar da zata zo yaji tausayin ta ba sai gashi rana kwatsam wai tana bashi tausayi, bai san sanda ya rungume ta a kirjin sa ba yana jin bai kyauta mata ba, Siddeeqah dai ta zama kamar mutum mutumi cikin ta har ya duru ruwa tsoro ya kamata tasan yauma aljanin yayan nata sun kuma tashi, tana so ta dago tana tsoro, saida ya gaji dan kansa ya sake ta yana shafa bayan ta yace "dan Allah Siddeeqah kiyi min wannan alfarmar ki daure ki tafi wannan makarantar wallahi saboda ina son ki ne nayi miki wannan gatan".
Da sauri Siddeeqah ta dakatar da shi ta hanyar fadin "ya isa haka yaya duk maganar da zamuyi a tsakanin mu kada ka ambaci so domin babu shi a tsakanin mu har abada, ka fada min ba zaka taba sona ba kamar yadda nima ban taba jin sonka dai-dai da rana daya a cikin zuciya ta ba, na yarda zan tafi idan har kayi alkawarin za kabi duk wani sharadi da zan fada maka".
Bakin Sadeeq na rawa Yace "naji fada min zan bi duk abinda kika ce".
Ta cigaba da cewa "na yarda zan je idan har ka yi alkawarin zaka sake ni idan nagama karatu, lokacin na girma na kara wayau ta yadda zan samu irin mijin da nike so na aura, amma ni wallahi Sam ban dace da kai ba yaya". Ta fada tana dago kai, suka hada ido tayi sauri tai kasa da nata saboda kwarjinin sa.
Yana mamakin Siddeeqah lokuta da dama idan tayi wata maganar ko babbar mace albarka koda yake ba abin mamaki bane zamani ne dan ga yaran da basu kaita nan ba suna abin da ba kowace babbar macen ba, itama dan ta taso a kauye ne shiyasa take da wayan kauye.
yace "in dai wannan ne mai sauki ne zan sake ki tunda ke ce kika bukaci haka, amma mai zaki cewa su Daddy da Momy idan suka bukaci sanin dalili?".
Sai da ta tashi daga inda take tayi tsallan murna tace "bani ce zan basu amsa ba kaine ya dace da ka basu amsa, ko dai ka fada musu gaskiyar bama son junan mu ne ko kuma kayi musu karyar da har abada bazasu gane ka ba, kaga sai ka je ka auri wacce kake so, nima na auri wanda nike so".
"to". Kawai Sadeeq yace dan tafara gundurar sa da wannan maganganun nata da yake daukar su kamar tatsuniya
Bai san ita kuwa siddeeqah har cikin ranta take fada masa wannan maganar ba
Tace "ko kaifa yaya hannu ta mika masa tace mu kulla abota yaya nayi maka alkawari daga yau zan dunga jin maganar ka zanyi kokari na zama mai nutsuwa kamar yadda kake so zan dunga yin duk abunda kace nayi ina son wannan abotar tamu ta fara daga yanzu zuwa lokacin da zaka sake ni".
A tunanin Sadeeq Siddeeqah ce bata da wayau dan shi gani yake ya gama da ita shiyasa komai tace yake yarda, yanzu ma ya yarda su kulla abota, har zuwa ranar da zata kare secondary school ya bata takardar ta.
Hannun sa ta kama tace "yaya tashi muje falo ka fadawa su Daddy na yarda".
Mikewa yayi kamar yadda tace ta shiga jan hannun sa suka soma tafiya tana gaba yana biye d a ita a baya, a haka suka fara taka step suna saukowa, tuni suka fara daukar hankalin wasu daga cikin mutanen falon da suka lura dasu kama daga Daddy Umar Jiddah da Ummee banda Farooq da Khadija da suka zauna akan kujerar da tabawa step din, Momy kuwa bata gurin tana bedroom taje daukowa Daddy wayoyin sa daya manta, gaskiya sun burge sun bada sha'awa kuma sun dace da junan su.
Ahaka suka karaso fuskokin su dauke da nishadi
Ba karamin mamaki Momy tayi ba alokacin da ta gan su, haka ma Daddy da sauran yaran gidan
Koda suka karaso falon kan kujera Siddeeqah tai wa Sadeeq masauki inda itama ta zauna kusa da shi hannun ta na sarke da nasa sai Murmushi take tana kara shige wa jikin sa, shi kuwa Sadeeq daure wa kawai yake dan bai saba da wannan sabon al'amarin ba yana so yai mata tsawa yana tsoran ta birkece masa
Momy da Daddy kuwa addua suke acikin ran su Allah yasa lokacin haduwar kan yayan sune yazo Allah yasa su d'aure ahaka
Comment
Share
Vote
NI DA YAYA SADEEQ
·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙