← Book details nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 31

 Chapter 01

nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

بسم الله الرحمن الرحيم

_______A zaune nike a kan tabarma cikin baranda isaka na kad'a bishiyar mangwaron da ke tsakiyar gidan mu Ganyen ta na fad'owa 'kasa gunin burgewa. Dambu ne a gabana cikin wata 'yar samira inaci ina sud'e yatsun hannu na saboda dambun yayi min dad'i kamar kar ya'kare
Kawata Ladiyo. Ce ta shigo gidan mu hannunun ta rike da goshin ta yana zubar da jini koda na d'aga kaina na kalle ta bance mata komai ba Na maida kaina kasa na cigaba da cin dambu na, Saida na cinye dambun tas Sannan na kora da ruwa, Baki na bud'e iya 'karfi na Nayi wata katuwar gyatsa tarashin mutunci, Irin wacce idan yaya Sadee'k ya na guri nayi yake buge min baki.

Kallan Ladiyo nayi Na ta'be baki nace "Ladiyo lafiya kika zo ki ka tsaya min a kai ko aiko ki a kayi?".

Ladiyo. Da Dama jira take in tambaye ta, saboda tasan in bani na tambayeta ba tana iya fad'a min na bata kunya tana kuka take fad'a min abinda ya faru.
Tace "Kinsan yaron da jiya muka barar mai da markad'e ai Dazun Umma ta ta aike ni gidan su Zulai anso mata kud'in zubin a dashi,bayan na anso kud'in na had'u da yaron akan hanyata ta dawowa Ni bansani ba a she nan ne layin da yaron yake, shine yayi taimin ruwan duwatsu tako ina har wasu abokan sa suka taya sa Allah ya temake ni Baban Ramma Yazo wucewa sai yaga abinda ke faruwa. nan take ya tsawatar musu shine suka 'kyale ni, amma wallahi inaga da sai dai a d'auko gawa ta saboda jifan da suka min bana wasa bane, Ko gida banje ba nayo nan saboda ya bani sa'ko". Yace in fad'a miki "wallahi kema saiya fasa miki goshi".

Nace "Kan uban_nan yanzu dama acikin' kauyen nan a kwai wanda zaija dani har ni zaice zai fasama goshi To wallahi kaf kauyen Dande. Banga mai fasamin goshi ba amma tunda yace haka muzuba ni dashi shege ka fasa kafin ya fasa min ni zan fara zuwa gidan su in fasa na Babar sa inya so kinga yaji dad'in fasa min nawa da hujja".

Inna da fitowar ta kenan da Buta ri'ke a hannun ta da alama daga ban d'aki ta fito Tace "ke da wa siddi'ka. Ki ke yin wannan ashar d'in kamar bakya zuwa islamiya"? .

Nace "yo Inna bakiga Ladiyo bane?".sai alokacin Inna ta lura da Ladiyo da ke a tsaye gindin rijiya ta d'ora hannun ta a kai. Inna Tace "na ganta sai akai yaya"?.

Cikin 'kosawa da tambayar da Inna take min nace "yo wai ke Inna bakiga goshin ta bane a fashe jini yana zuba?".

Inna tace "na gani mana. tunda ta'ki rabuwa dake ai tana tare da wahala, gashi ta zama lusara bata iya ta'buka komi sai tsokana fal cikin ta tsokana kuma tame 'karfi ce ai".

Nace "yo Inna wanda yafasa mata goshin ne nima" yace "zai fasamin duk sanda muka had'u shine abin yabani dariya da takaici Har kika ji nayi wannan ashar d'in Idan duka 'kauyen nan gatansane wallahi sai naci ubansa duk abinda zai faru ya dad'e bai faru ba. Besan wace ce Siddi'kar Inna ba shiyasa amma ko yaran goye aka amaba ta masa suna na Nan take jikin sa yake fara rawa saboda karo dani babu dad'i".

Banyi aune ba naji anbige min baki Da masifa na d'ago kaina dan naga wani mara kunyan ne ina magana zai bigen baki.

Amma sai mukayi ido hud'u da yaya Sadeeq Turo d'an 'karamin baki na nayi. Yayin da shi kuma yai min dakuwa da hannu.

Yace "saidai ke ki ci uban ki, kamin shi yaci nasa, yau ina gida bazani gurin aiki ba Saboda haka kema babu inda zaki fita sakarya da'ki'kiya kawai ba arabi babu boko, sai yawan gad'a a dan-dali ke a cikin matan 'kauyen kin fita zakka saboda kinfisu wauta da tuma sanci.
Inna na daure miki gindi kina yin abinda kika ga dama ko, Kina ganin kamar gata take yi miki To kisani Inna ta riga da ta gama cin kasuwar ta Ke kuma yanzu kika fara taso wa. Dan baki san komi game da rayuwa ba, kwata kwata ma nawa kike? ko 14 years old baki kaiba amma kin addabi mutanan gari kullum ana cikin kawo min 'karar ki ina bada ha'kuri".

Duban Ladiyo yai Yace "ke yakike da suna ma? Ladiyo yake nunawa da d'an yatsan sa manuni ya
Ladiyo dake a tsaye hannun ta akan goshinta, tace " "sunana Ladiyo".

Yaya Sadeeq yace "oho koma dai maye sunan naki maza tashi kibi nan" yai mata nuni da hanyar fita gidan.

Yakuma cewa "ko a 'kofar gidan nan idan kika bari na kuma ganin ki to kashin ki ya bushe. Bare kuma in ga wa'innan 'yan 'kafafuwan naki a cikin gidan nan. Allah saina 'ba'b-'ba'bla 'kafa fuwan. Ina fatan kinji abinda nace miki idan kunne yaji gan-gar jiki ta tsira, oya maza zo kibi nan tun muna sheda junan mu"

Ladiyo jiki na 'bari ta bar gidan mu. A d'ari da hamsin.

Kallo na yayi muka had'a ido da shi ya wurgo min harara, Nima na rama cikin 'kun'kuni ciki-ciki nace "nima idan ido ne ba a fini ba bare ayimin barazana dasu kuma mu zuba ni da kai d'in.

Yah Sadeek yace "ke me kike cewa?".

Inna tai saurin cemai ba da kai takeyi ba tafi abinka".

Yah Sadeek yace "Inna kiba ta abinci na takawo min".

Inna taja dogon numfashi tace wai ni Garba me yarinyar nan taimaka ne haka? daka tsaneta. banason haka fa tun ba yau ba nasha fad'a maka Amma dake ka rainani bakajin magana ta. Ko kad'an saboda ni kaka ce To alhaji karami na nan zuwa wata ya kusan 'karewa idan kai ban isa da kai ba shi na isa dashi. Kuma shine mahaifin ka Idan yafad'a maka wata 'kila kaji nasa tunda ka 'ki jin nawa ni".

A sakarce yaya Sadeek ya kalli Inna yace "haba hajjaju makkatun mu karrama ranki shidad'e Ki dad'e kiyi 'kar'ko kiyi shekarun bishiyar dabino Ni na isa in raina ki duk da cewa nike aurenki amma ke ke bada umarnin Kuma yadda Kiki ce haka za ai nadena daga yau babu ruwana da ita."

washe baki inna tai tace " ko kaifa Garba shikenan ya wuce amma da kasa ka 'yar mutane a gaba se ramewa take shiga ciki yanxu zansa ta kawo maka abincin naka

💋💋💋💋💋💋
Hi guys don't forget to

Comment
Shear
Vote

_I love you all_

💋💋💋💋💋💋


   NI DA YAYA SADEEQ
  love story 2021 typing free book_

Story & Writer by
Siddiqahtul Khairy Yahya
            (S beauty ✍️)


بسم الله الرحمن الرحيم
Chapter 2 · 0% Book details