← Book details nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 11 OF 31

Chapter 13

nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

_____A gaggau ce yayi faking motar sa ya fito ya shiga cikin gidan yayi sa'a babu kowa a falon sai TV da aka bar sa a kunne yana 'kira'ar alQur'ani mai girma, darect sama ya haura bai zarce ko ina ba sai d'akin sa, yana shiga ya aje wayo yinsa ya cire a gogan hannun sa sannan ya fad'a bayi bai wani d'auki lokaci ba ya fito d'aure da towel a 'kugun sa da wani a hannun sa yana tsane ruwan jikin sa gaban madubi ya zauna mayuka ne kala kala da tura ruka masu 'kamshi da tsada ya shafa wannan ya mutstsuka wancen saida yabi yagama shafa ko wanne. Sannan ya fesa body spray mai sanyin 'kamshi wata dakakkiyar shadda fara ya d'auko wanda aka 'kawata ta da ado da dinkin zamani hular zanna bukar ya ciro ya a je a gefe sannan ya d'auko agogon hannu da safa da ba'kin takalmi mai sheki, a tsana ke ya shirya abin sa tsaf sannan ya d'auki wayo yin shi ya fito. Da sauri sauri yake sauka akan step d'in tun kan ya 'karasa saukar yake jin hayaniyar su Momy bai so haka ba, saboda yanzu saita tsare shi da tambayar ina zashi "Momy". Sadeeq ya fad'a alokacin da ya 'kara so cikin falon gaba d'aya yaran gidan sun sha jinin jikin su saboda basu san ya zo ba Siddi'ka kuwa batayi mamakin ganin sa ba, bakin ko waccen su na rawa suka fara gai dasa ya amsa fuska ba yabo babu fallasa "yaushe kadawo gidan sadeeq? Kuma ina zaka haka kaci wannan kwalliyar sai kace sabon ango". Yana sosa 'keya yace "wallahi Momy ban jima da shigowa ba bikin wani aboki na zani anyi daurin auren jiya yau ake dinner shine nike ta sauri kada nayi latti".
"A dawo lafiya".

Tun a hanyar sa ya kira gimbiyar ya shaida mata ya taho 'kara kwatan ta mishi unguwar tayi, da misalin 'karfe 8:17 ya isa cikin unguwar daganin ta ma'aikatane a cikin ta saboda gidajen kusan duk iri d'aya ne kamar quarters haka unguwar take

Bayan yayi faking a gefen wani gida, ya d'auko wayar sa da ke ajiye a gefen sa yad'an shafa screen d'in sai ga number tafito da suna Baby a jiki call ya danna sai da ta fara ringing sannan ya kara a kunne

Ringing biyu ta d'auka ajiyar zuciya ya sauke yace "Baby na" daga can 'bangaren cikin shagwaba tace "my heart kazo ne?".

Ce wa yayi "akasi aka samu Baby na bayan na gama waya dake sai ga kira da ga office din mu wai ana son gani na to babu yadda na iya kin san aikin gwaumnati shine na juya a kalar tafiyar yanzu haka ina hanya ban isa ba ha'kuri na kira na baki".

Zuby da ta gama shiryawa, zuwan Sadeeq d'in kawai take jira, batasan sanda kwalla ta fara zubo mata ba cikin shagwa'ba take fad'in "amma my kasan dai bazan ji dad'i ba wallahi har Abbah na sanar masa kuma yana gida inason ka gaisa da shi ga Mamq da tun sanda ka shaida min zaka zo na fad'a mata tasa aka shirya maka abinci yanzu mai kake so na ce musu?". ta kara sa maganar tana fashe wa da kukun shagwa'ba

Tun Sadeeq yana dariya ciki ciki har saida ta fito fili saboda yadda Zuby ke shagwaba gunin ban dariya ga kuma kasala da ya rasa ta maye ta saukar masa duk a lokaci daya

"Haba my wai dariya nabaka?". Niyar fashewa da wani kukan take yi, yayi saurin cewa "gani a 'kofar gidan ku kisa mai gadi ya bud'emin get, ko ba shine mai ba'kin get ba?".
Shuru tayi saboda bata yadda da abinda yace ba
Jin shurun yayi yawa Sadeeq yace "ko in koma ne?".
"Wai da gaske My kana 'kofar gidan mu?".
"Na ta'ba yi miki 'karya ne?".

"A a". Ta bashi amsa

"to kisa abud'e min get".

Ihu ta saka 'kamar 'karamar yarinya ta cilla wayar kan gado

SADEEQ da kallo yabi screen din wayar yana mamakin Zuby d'in wani lokaci idan tayi abu saita koma kamar Baby amma duk da haka tana matu'kar burge sa saboda son ta a kullum 'kara dad'uwa yake yi acikin zuciyar sa
A yanzu haka yanajin idan ba ita bazai iya rayuwa da wata 'ya mace a matsayin matar sa ba.

Mai gadi ne ya wangale get d'in Sadeeq ya sulala da motar sa ciki kana ya nemi guri yayi faking

Bai fito daka cikin motar ba wayar sa ta hau 'kara a kasalan ce ya d'auka ya kara a kunne
Daga d'ayan 'bangaren tace "My ga Rahmatu nan yar aki zata kaika falon baki".

"Banga kowa ba ni".

"to baby ka fito daga cikin motar mana zaka ganta".
Ta fad'a tana 'kara gyara tsayiwar ta a jikin balakona saboda tun sanda Sadeeq ya shigo Zuby ke le'ken sa har kawo yanzu da take waya da shi tsaye take ko motsin kirki bata yi sai Murmushi da take yi zuwa zuwa mai wuyan fassaruwa

Daya bud'e murfin motar saida ya d'auki 10 seconds sannan ya fito da 'kafar sa guda bayan wasu seconds din ya fito da d'ayar Zuby dake la'be a balakona mamakin jan ajin Sadeeq tayi, saboda ko ita da take mace bata da kalan sa.

"Wow" shine abinda Zuby ta fad'a a lokacin da taga Sadeeq ya fito, "gaskiya gayannan 'karshan had'uwa ne kamar shi yayi kanshi Sadeeq ka riga ka shigo hannu bazan taba bari ka kubuce min ba, ban taba jin ina son nayi aure ba sai akan ka zanyi iya bakin kokari na wajen jan hankalin ka kuma zan kiyaye duk abin da zai sa ka gane wace ce Zuby bazan bari wata kawa ta ta sanka yanzu ba, gaskiya saboda gudun matsala inason asa bikin mu kusa saboda kada yan gulma su yimin cikas". Zuby ce ta fadi haka bayan ta gama 'karewa Sadeeq kallo

gaskiya Sadeeq namiji ne irin mazajen da suke da wahalar samu a wannan zamanin saboda ya had'a duk wani abu da ake san namiji ya mallaka Allah ya bashi yana da tsayi na misali ga kyau da hasken fata ga kudi da ilimi hankali ya iya daukan wanka ya iya soyayya mai daukan hankali duk shigar da yayi sai ta yi masa kyau shiba siriri ba shiba dan lukuti ba gaskiya masha Allah gayan ya hadu ajin karshe ne🥰

Wata matashiyar mace da bazata haura 35 years aduniya ba, ta 'kara so gurin sa cikin girmama sa tace "ranka shidade nice Zuby tace na kaika falon baki".

Sadeeq da wani lokaci magana take masa wuya bai amsa mata ba sai nuni da yayi mata alamar babu damuwa ta kaisa, tana gaba yana bin ta a baya har suka isa cikin wani madai-daicin falon da yake d'auke da manyan kujeru masu ruwan orange da baki sai chanis kafet da aka shimfid'a a tsakiyar falon shima ba'ki ne da d'ishi d'ishin orange a jikin sa sai 'katon TV da ya mamaye jikin bangon falon a gefe guda a kwai 'yan 'kananun tebura zagaye da babba a tsakiyar su, gaskiya d'akin ya had'u wani abun ma bazai fad'u ba

bayan Sadeeq ya shiga ya nemi kujera ya zauna a kan 1cter jim kad'an sai ga ramatu ta shigo hannun ta rike da katon tirai da aka jera kulolin abinci masu kyau da ban sha'awa a kan babban teburin ta jera kulolin sannan ta fita ta kuma dawo wa da wani 'katon turai din mai dauke da fruit, da kunin aya da zobo ta kuma jerawa ta fice
Can sai ga ta ta kuma dawo wa da jok din ruwa a tirai da kofuna biyu bayan ta ajiye ta dauki kofi daya ta zuba mai
Ruwan sannan ta saka wani farin abu a ciki kamar 'kankara nan take ruwan ya fara canza color, daga fari ya koma ja haka dai yai tayi sannan ta mi'ka masa
Amma sai yaki amsa da taga bashi da niyar amsa sai ta ajiye ta fice acikin ranta take cewa "ko ina Zuby ta samo wannan kyakkyawan saurayin tunda Zuby ke kawo samarin ta bata taba kawo mai kyau da hankali da nutsuwar wannan ba". Abinda ya daure wa ramatu kai yadda Sadeeq din yayi shigar kamala yana kama da mutanen kirki a fuska to mai yakawo sa gurin Zuby, saboda Mama ta san duk wani abu da Zuby ke aikata wa wani lokacin ma ita ke bata karfin gwuiwa sabanin Abban ta da bai san komi ba

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Gaba daya mutanen gidan zaune suke a falon sama amma kowa da abinda yake yi saboda Umar littafi ne a gaban sa yana homework yayin da khadija da Siddeeqah suke fira Momy kuwa laptop ce gaban ta tana danna wa sai Jiddah dake faman danna waya tana cika tana batsewa Ummi kuma Session flm take kalla sun dauki tsawan lokaci a haka

Bayan Momy ta gama abinda ta keyi ne ta dube ni "Siddee'ka". saida naji 'ya 'yan hanjin cikina sun kad'a saboda fargabar abinda zata cemin da hanzari na dago kaina muka hada ido nace "na'am Momy".
"dazun da rana nayi magana da Sadeeq akan maganar makarantar ki". Yace "ya samami ki admission a makarantar kwana har ya gama komai ranar lahadi zai zo ya dauke ki ya kai ki

Ba Siddeeqah kadai ba har su Khadija sai da suka dago kai suka kalli Momyn domin su dad'a tabbatarwa basu ga alamar wasa afuskan ta ba duk da Momyn daman ba mai irin wasa da yarannan bace amma kuma tana jansu a jiki ta yadda duk wani abun da yashige musu duhu suke zuwa neman shawara gurin ta.
"Momy makaranta kwana fa ki kace". Siddeeqah ta fada murayan ta a sanyaye

"Eh". Siddeeqah wallahi makaran tar kwana Sadeeq ya nemo miki naso na hana amma sai yace "ya kashe kudade masu yawan gaske saboda sunan wata a ka cire aka sa naki". Sannan yace "acan sai kin fi dagewa kiyi karatu idan kina gida wasa ba zai barki ba".

"Momy Daddy fa shima ya yarda ko bai sani ba?". Khadija ta tambayi Momy

Sai a lokacin Momy ta tuna ba tayi waya da Daddyn ba dan sanda ta kira sa ta nason suyi maganar yace "mata suna meting idan sun gama zai kira ta".

"A a" Momy tace "zuwa anjima idan ya kira ni za muyi maganar".

"Momy mai yasa yah Sadeeq zai mini haka gaskiya ni Momy ba zani ba gwara in koma 'kyauye gurin Inna ta na hakura da karatun bazan wani yi kuku da ku ba".

"Taso kizo kusa dani 'yata". Jiki na babu laka na tashi na koma kusa da ita na zauna na tsaida idanuwa na akan fuskar ta, hannun ta ta daura a kan kafad'a ta cikin lallashi tace "Siddeeqah ha'kuri zaki yi saboda ilimi gishirin rayuwa ne idan Sadeeq yayi haka ne don ya kunta ta miki to insha Allah aniyarsa ce zata bisa saboda ke gaba ta kai ki.
Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai same ki sai alkairi".

"Momy kuma wace makarantar?". Ummi tayi tambayar
"Katsina" yace "zai kaita wai akwai kanwar Farooq a can" yace "makarantar tana da koyar wa sosai kuma suna da kula da dalibai".

Jikin Siddeeqah yayi mutakar sanyi duk da bata taba jin labarin makarantar kwana ba amma dai batason tayi nisa da gida ita da take so duk bayan 2 weeks tana zuwa Dande ganin Inna
Gashi yanzu za a kaita wani garin ba garin da take ba

Da kyar Momy ta sha kanta ta amince ba dan ranta ya so ba sai dan ganin girman Momy da take yi, Momy ta cigaba da bata baki da kal momi masu dadi da sanya ya rai har ta amince

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Zuby ce zaune a kan kujerar dake kallon ta sa, kura mata ido yayi ko kiftawa ba ya yi.

Cikin shagwaba tace "muni na kake kallo ko banyi maka ba ko?".

"ko daya ina kallon irin baiwar da Allah yayi miki ne Kin kuwa san wani abu?".

"A a". Tace mai

"Ban taba ganin mace mai kyau irin kiba, gashi tun da nike a rayuwa ta ban taba haduwa da wacce na ke so har naji ina mura din auren ta ba sai ke, gaskiya ki kara godewa Allah bai rage ki ta ko ina ba a lokacin da naga kina tafiya sai kikai mini kama da wahainiya hatta muryan ki abar so da kauna ce idan kina magana kamar ana busa sarewa, ga...".

"Ya isa haka my kada kasa na kasa bacci yau amma ka zuga ni da yawa har kasa naji kaina yayi kato".

Duk kuwa da ba karamin dadin kalaman shi taji ba wani d'a na miji bai taba yaban ta haka ba duk kuwa da ita mutum ce mai san a dunga kuranta mata ana zuga ta shiyasa tace "Sadeeq dina na musamman ne".

"Ai kin wuce haka Baby na saboda kedin zara ce".

Cikin zolaya tace "Allah My kafi kyau a fili ka daina wahalar daukan picture's saboda yana rage maka kyau".

"Bawani nan kodai ban miki bane?".

Zaro ido tayi waje gami da dafa kirji tace "wane mutum inji mutuwa".

"amma kinsan labarin zuciya atambayi fuska ko?".

"fadamin nason daman dan sanda akwai ku da karantar yanayin mutum".

Zai yi magana kenan wayarsa ta hau ruri DCP Kamal yagani yana yawo a kan screen d'in cikin girmamawa ya kara wayar a kunne bayan ya daga ya gaida ogan na su.
Ko mai yace masa daga can ban garen oho, Shi dai Sadeeq din yace "okay angama ranka shidade okay okay ahaka dai suka karasa wayar

Ya a je yana kallon Zuby da ta kura masa ido ko kiftawa ba tayi.

"Ya dai" yace mata yayin da yahura mata iskar bakin sa, sai a lokacin taga rashin dacewar hakan kunya ta kamata tayi sauri ta sadda kan ta kasa tace "kamar ana neman ka A gurin akin ka ko?".

Gira yadaga mata alamar "eh"
"to bari na kira Mama ku gaisa sai na kaika gurin Abba daga nan saika wuce".

Bata jira amsar sa ba ta wuce bata wani dauki lokaci ba ta dawo tare da wata dattijuwar chocolate din mata ita ba doguwa ba ita ba Gajere ba tsaka tsakiyar.

Cikin mutunci Sadeeq ya russuna ya gaishe ta ta amsa mai cikin kula da jin dadi Sannan sukayi sallama ta wuce

"gaskiya Mama nada kirki". Sadeeq yace wa Zuby

"Allah da gaske?".

"Ehman ashe ita kika biyo".

Zuby dan dadi har rufe fuska take yi wai yau ita ake yaba haka 💃

"muje na kaika bangaren Abba ku gai sa".
"Muje to" ya fada yana mike wa tsaye

Ta wata kofar suka bi sai gasu a cikin wani madai-daicin falon da babu tarkace a cikin sa da wani datti jo zaune a kan kujera hannun sa da jarida yana karantawa fuskar sa sanye da siririn glass bayan sunyi sallama suka karasa ciki a kan kafet Sadeeq ya zauna ha gaida sirikin nasa Abban Zuby yaji dadi sosai da yaga sadeeq ne zai auri tilon gudan jinin sa bayan sun gaisa suka dan taba fira Zuby kuwa bakin ta ya ki rufawa farin cikin ta ya bayyana a fili, basu dade ba Sadeeq ya yi masa sallama.

babu laifi Abban Zuby yana da haske fata wata kila agurin sa Zuby ta dauko hasken fatar

Har bakin motar sa Zuby ta rakosa tana yi masa shagwaba kala kala da kyar ya samu ya lallashi ta ta barshi ya tafi

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
"Ku tashi kowa yaje ya kwanta dare yayi sai kuma idan Allah ya kaimu gobe" Momy ce ta fadi haka yayin da take kallon 'ya 'yan ta "to" duk suka ce masu tarkace suka dauka Ummar da dakin sa yake a kasa ya shige haka Jidda ma nata a kasa yake itama ta ce "Momy good night" tuni mu uku muka dun guma zamu haura sama amma sai Momy ta kwala min kira "Siddeeqah na manta zo ki dauki abincin yayan ku ki kai masa ban garan sa tunda saman zaku haura gab yake da shigowa

*Ash wash kash*😂
_Na gaji hhhmmmm idan ban ga ruwan comments ba za a dade banyi typing ba_ 😂

*Kada ku manta*
_Comment kyauta ne haka ma share da vote_😂

Taku har kullum _Sbeeuty✍️

NI DA YAYA SADEEQ
                  
بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
Chapter 11 · 0% Book details