← Book details nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 31

Chapter 16

nbspnbspnbsp Ni Da Yaya Sadeeq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

______"To" Umar ya fad'a yana mai mi'kewa jikin sa babu 'kwari
Khadija sai sannu take ma Jiddah da bakin ta ya kumbura yayi suntum sai zubar jini yake
Umar bai wani jima ba ya dawo "Aunty Khadeeja na fad'a masa bari na haura sama na d'auko muku mayafin"
"To" Umar khadija ta fad'a tana rungume 'yar uwar ta a 'kirji
A haka Umar yadawo ya iske ta ya mi'ka mata ta ansa ta yafa sannan ta yafa ma Jiddah "zaka bimu ne?". "Eh zani". "To muje ko". Tafad'a tana d'aga Jiddah daga jikin ta "sannu sister daure ki tashi na kamaki sai mutafi asbiti ayi miki dressing kada abinda kike rainawa yazama babba da 'kyar Jiddah ta iya kama hannun Khadeeja tana waiyo waiyo ta samu ta mi'ke kallo d'aya zaka yi mata ta baka tausayi saboda yadda bakin ta ya kumbura da taimakon Allah da na Khadija suka fito falon a lokacin Idi driver ya tada mota Habu mai gadi ne ya hango su cikin sauri ya 'kara so inda suke ya bud'a masu 'kofa yana yiwa Jiddah sannu Umar kuma ya zagaya ta d'ayan bangaren ahankali Jiddah ta shiga khadija ta mara mata baya Habu mai gadi ya wangyale musu get suka fice

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Tsaye Siddeeqah take ri'ke da kugun ta sai zum 'bure zum 'buren baki take yi a cikin ran ta take fad'in "kai kuwa matar ka ta bani ayi mutum dun kum ba za ayi fira da shi ba sai kace wani boss kullum fuska daure" "ke mai ki ka ce ina wasa dake?". Abinda Siddeeqah bata sani ba ba acikin zuciyar ta tayi maganar ba sarai sadeeq yaji mai tafad'a

'ko'korin tashi yake yazo ya cimmata sai wayar sa ta shiga naiman dauki da kamar bazai duba ba saboda wannan yarinyar ta 'bata masa rai amma sai wata zuciyar tace "ya duba dai yaga wake neman sa". Haka kuwa akayi dauko wayar yayi daga kan hannun kujera, Baby shine sunan da yake yawo akan screen d'in, take ya saki murmushi  harda d'an cije leban sa na 'kasa ya gyara kwanciyar sa da kyau
Baki bud'e Siddeeqah ke kallon sa a tunanin ta aljanin ne ya motsa
Amma sai taga ya d'aga wayar ya kara a kunne baiyi magana ba daga can 'ban garan aka ce
_"Amincin Allah ya tabbata a gare ka ina fatan wanda nafi so da kauna a duk duniya ya wayi gari lafiya koda yike naji a jiki na kana cikin koshin lafiya saboda inajin duk wani yanayi da ka ke ciki a jiki na_".

Sadeeq kusan suman kwance yayi saboda shi a rayuwar sa yana son kula wa musamman a bangaren soyayya zai iya 'bata lokaci mai yawa wajen tsara kalaman soyayya saboda shi a yadda yake gani idan bai ba ma soyayya hakkin ta ba bai more rayuwar sa ba

Bakin sa washe kamar tana ganin sa yace _"gimbiya sarautar mata ina fatan amincin tare dake"_
"Na gode My". Jiya na gaji ban san sanda bacci ya dauke ni ba dan Allah kaya kuri ban kira naji yadda ka iso gida ba".

"Kada ki damu baby Allah ya kare miki ni da kariyar sa na zo gida lafiya kema fatan dana baro ki babu abinda ya taba min ke".

Zuby na dariya tace "kana nufin har na kai a bani irin wannan kulawar sai kace wata gimbiya?".

"Haba ke kuwa ai kin wuce gimbiya a gurina ko kin mata da auren ki nike so nayi? Nan da kika ganni akan abinda nike so bani da sakaci ina basa kulawa ta musamman".

Cikin kissa da kisi sina Zuby tace "yanayin muryan ka ya nuna min baka karya ba kana jin yunwa".

Sai alokacin Sadeeq ya tuna ashe bai karya ba,


ni kuwa duk sona da gulma dole na kyale Siddeqa saboda na kasa fahimtar yanayin ta har yanzun a tsaye take idon ta akan Sadeeq kyam shi kuwa bai san tana yi ba ya tafi duniyar masoya

Ya cigaba da ce wa "wallahi Baby na manta".
"My kamanta fa kace yanzu fa 12:00 gaskiya ka daina barin mun kanka da yunwa saboda ba kan ka ke bari ba ni kake bari idan kuma kanason na cutu ai shikenan".

"Haba Baby na na daina insha Allah zan dunga kula miki da kaina kamar kina gani na dazun ma har zan karya sai wasu 'kannai na suka kama rigama har sukayi doke doken juna to shine duk naji raina babu dadi".

"Ayyah my sorry kasan sha'anin yara sai ana hakuri da su amma gaskiya ka tashi ka je ka ci abinci idan ka gama bayan sallar azahar saika kirani mu daura daga inda muka tsaya".

"To ranki shidade na gode da kulawa I love you". 💖
"I love you too"
"By"
"okay by take care for me".
zuwa yanzu Siddeeqah ta nemi guri ta zauna amma wannan karan ba shi take kallo ba da yatsun hannun ta take wasa saboda yadda take jin ranta babu dadi.

Shi kuwa Sadeeq har cikin zuciyar sa ya manta da wata Siddeeqah a d'akin sa shiyasa ya saki baki ya yi ta suru tu

Kallon sa tayi tace "yaya zanyi fitsari" banza yayi da ita kamar bai ji mai tace ba

Can da taga fitsarin zai iya zubo mata tace "yaya yafa matse ni zai zubo".

Sai a alokacin ya dago kai suka had'a ido, bai kula ta ba ya tashi ya shiga bedroom din sa bai jima ba ya fito hannun sa rike da mukkullin mota ya nufi 'kofar fita  batare da yace mata komi ba  ganin haka tayi sauri ta mike kafar ta a matse ta soma tafiya alokacin shi har ya bude kofar ya fice

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Kwance take akan gadon da ake kwantar da marasa lafiya anyi mata dressing din bakin ta kuma an sa mata ledar 'karin ruwa ga dukkan alamu ma batasan wa ke kanta ba saboda allurar baccin da aka mata Khadija na gefe tayi tagumi Umar ma haka kowa da abinda yake sakawa a cikin ransa

_Na gaji da typing amma idan harnaga ruwan comments zan kara yi muku wani typing din anjima_
🙏
NI DA YAYA SADEEQ
˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
Chapter 14 · 0% Book details