← Book details Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 10

Sashe 9

Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kasancewar Gidan Hajiya Kaltume babban gida ne mai wadatattun dakuna don haka tsaf ya dauke bakin Nahuche da na Girei. Aunty Badiya bata zauna ba suka shiga hidima ta bajinta da surukan su. Sabida yadda gidan ya cika da mata Habibu bai samu ganin Hajiyar sa ba suka wuce Hotel shi da su Uncle da PA Rasak.
Har dakin Haj. Kaltume su Nene suka kawo Rahinah, aka bada amana ta ce Allah ya taya mu riko. Yau ga Hajiya ga Rahinar Habibu! Duk da bata yi nasarar ganin fuskarta ba daga goshin ta da sumar ta ka san kasaitacciyar mace ce dole Habibu ya kasa aure akan wannan bafullatana.
Duk yadda suke boye maganar auren don kada ‘yan jarida su samu a daren ranar ta yadu a garin Zamfara, kasancewar Habibu sananne kuma fitacce wanda kiris a ke jira a kan sa. Washegari bayan kowa ya karya ya kuma kimtsa motocin suka sake kwasar su zuwa Nahuche.
A Nahuche 'yan Girei sun ga karramawa inda aka kai ta gidan su mahaifin sa kowa nasa ya zo ya gan ta, ya sa albarka, kowa sai Masha Allah yake ambato matar Habibu ta kai ta kawo, daga nan suka wuce fadar Nahuche suka gaida Kekun Nahuche wanda amini yake ga Kakan sa Bilyamin Nahuche.
Kwanan su daya a Nahuche suka wuce da amarya gidan ta.
******

ABUJA (Life-Camp)
G
idan Habibu na nan a sabuwar unguwar Life-Camp wadda ke gaba kadan da Gwarimpa. Madaidaicin gida na zamani zubin (Pent House) mai hawa biyu wato sama da kasa, Habibu ya dauko samfur din sa ne daga kasar Jamus bai jima da kammala ginin sa ba. Ba kasafai yake zama agidan ba idan yana garin Abuja rayuwar sa ta fi yawa a ‘Nahuche Hotel’ na garin Abuja. Rahinah could’tbelieve cewa yau ita ce a gidan miji, mijin kuma ba kowa ba face her ex husaband; Baban Abdullahi dan mutanen Nahuche. Wanda ta sha cin alwashin har abada bazata koma masa ba.
To an ce kana naka Allah na nasa kuma na san shine gaskiya. Bawa bai isa ya tsarawa kan sa rayuwa yadda yake fatan ta ba.
A yau da ta daga kai ta yi duba ga al’amuran duniya bakidaya, sai ta ga cewa (nothing is constant), komai canzawa yake kamar wahainiya, kuma rayuwar kanta garawa take da gudu kamar gare-gare abin wasan yara. To haka al’amarin ta da uban dan ta ke nasa juyin cikin hikima da iradar Ubangiji. Yanzu kam ta yarda ta amince a cikin kundin kaddarar su, har da na sake zama da juna.
Abinda bata da idea a kai yanzu shine irin zaman da zai gudana tsakanin ta da Habibu Nahuche. Wani kwayan mutum guda daya da ke ta walagigi da duniyar ta (for almost a decade) tun haduwar ta da shi a jirgi. Har gobe, har jibi har gata zuciyar ta ta ki aminta da shi, ta ki kwanciya da shi a kan nakasu guda daya, a kan laifin baya, ta ki yarda soyayyar sa isgenuinekuma soyayya ce yake mata ta tsakani da Allah.
Kullum da abubuwan da baudaddiyuar zuciyar ta ke gaya mata daban - daban akan sa, wanda laifin sa na farko duk shine sila, mafari kuma tushe na sanya duhun sa a zuciyar ta, duhun da ya lullube soyayyar da ke kwance lambam, ta zabi su kare rayuwar su cikin challenging juna.
Su Nene da sauran ‘yan uwan ta na Girei basu kwana gidan ba duk suka juya gidan Ambasada a daren, inda a can za su kwana, washegari kowa ya koma inda ya fito, cike da farin cikin an yi biki lafiya an kare lafiya.
Ita kadai tsakiyar makeken gadon ta wanda Uncle Usman ya yi mata, ta saka ta kwance, ta kasa kukan da amare suke yi sakamakon rashin nutsuwar da rashin ganin Abdallah har lokacin ya haifar mata.
Abdallahn da ta dawo domin sa, ta yi matukar kokari ta yi fulatanci (alkunya) bata tambayi kowa yaron ba har aka yi biki aka kare daga jama'ar Girei har zuwa na Zamfara zuwa Nahuche bata tambayi kowa ina Abdallah ba, ta dauka da ta zo gidan da shi zata fara tozali, ga ‘ya’yan Aunty Badiya babu wanda bata gani ba, kada dai ace tun dauke shin da yayi akan idon ta bai dawo da yaron daga inda ya kai shi ba? To ina ya kai shi?
Ita ba abun ta dauki waya ta kira Badiya ta tambaya ba, fillancin da ta daure ta yi a baya ya tashi a banza.
Daman dai bata yi tsammanin ganin Habibu ba. Shima kuma koda ya dawo gidan daga gidan Ambasada karfe goma sha dayan dare inda acan ya ci abincin dare bai yi tunanin neman ta ba. To yace mata me? Shekara goma da doriyar watanni masu yawa yayi babu ita cikin rayuwar sa, don haka, a ganin sa, dawowar ta yanzu ba abinda zai kare shi da shi, ba abinda zai sa ba abinda zai hana, ita da babu duk daya.
Data ga barci yaki zuwa alwala tayi, tayi sallolin shafa’i da wuturi da bata yi ba, ta zauna bisa darduma tana lazimi, anan barcin gajiya ya sace ta.
Chapter 9 · 0% Book details