Sashe 10
Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da asubah sautin kira'ar Minshawy da ya karade gidan cikin suratul Dalaq shi ya tashe ta, ta rasa daga ina karatun yake fitowa. Sai ta tashi ta fada toilet tayi wanka da brush ta dauro alwalah sannan ta fito.
Data fito tsayawa tayi tana kallon yanayin tsarin komai na dakin, kyan ginin gidan kadai ya isa, tana mamakin irin dukiyar da ya tara cikin dan lokaci kankani da dawowar sa. Hatta marbles din gidan sa bata taba ganin shi a ko’ina ba. Tsaki ta ta yi a fili ta ce.
“Allah ya sa halal yake ci”.
Bayan ta idar da sallolin ta na farillah da na nafila da kayan da ta zo da su tun jiya ajikin ta ta koma gado ta nade cikin duvet, kayan duk sun bi sun dame ta amma ta kasa cire su ta huta don ba ta so ma ta saki jikin ta in ta tuna a gidan Habibu take, tana sauraron karatun da yake ta tashi a gidan, yanzu kuma Suratul Tagabun ake karantawa. Sai ta lumshe ido tana bin kira’ar a hankali da fatan barci ya zo ya dauke ta, ko ya mantar da ita a ina take, ko ya maida reality din ya koma mafarki, burin ta a lokacin bai wuce a ce tare da Abdallah take kwance ba tana biya masa wannan karatun, tana yi masa tambabyoyi akan rayuwar sa da bata sani ba, amma barcin kamar ya san neman sa Dr. Rahinah ke yi ruwa a jalloh sai yayi kememe ya yi kemadagas yaki zuwa. Idanun ta dai suna rufe bata bude su ba, tana cigaba da bin karatun cikin Suratul Tagabun.
Ya dawo masallaci ne zai shiga dakin barcin sa ya ji tashin sassanyar muryar ta, tana bin karatun da ya kunna kafin ya fita.
Dakin da aka sauki Rahinah wato bedroom din ta opposite din nasa ne, a kusa da natan na Abdallah ne wanda yasa aka shirya shi da duk wani abun da yaro mai shekarun sa zai bukata, an narkar da dukiya ba kadan ba a dakin Abdallah, katifar sa kadai water mattress ce.
Tsayawa yayi kasake! A kofar dakin sa yana sauraron ta. Bata son abinda zai tuna mata a gidan Habibu take, a gadon auren sa take kwance, don haka karatun ya tafi da bacin ran ta ya wanke wannan damuwar, ya sanya mata nutsuwa da confidence din jin cewa zata iya sake zama da Habib Nahuche, da So ko babu So, Albarkacin Abdallah, dawowar ta gidan sa baya nufin karshen rayuwar ta.
Karatun ta ya mishi dadi ba dan kadan ba domin ya maida gidan lively. Duk da gari bai gama wayewa ba, sai ya tuna jiya bai bata komai ta ci ba, a matsayin ta na bakuwa a gidan sa wadda bata kai ga sanin ko’ina na gidan ba, sannan bai duba ta ya ga yadda ta zo ba ko da bazata kula shi ba.
Tun jiya ya sallami kukun sa na gidan, ba zai jure wata mu’amala ko yaya ta shiga tsakanin Rahinah da wani namiji ba bayan su Musaddiq shaqiqan ta, bai san yana da kishi na fitar hankali ba sai ranar da Rahinah ta ambaci ta zabi wani Irshad a kan sa. A daren ranar ya san ba bakaken maganganun Rahinah ne suka hana shi runtsawa ba face wannan subul da bakan da ta yi a gaban sa. Har da cewa ta gwammace shi (Irshad) duk da kasancewar sa womanizer a kan sa.
Yanzu kam yana tantama a kan cigaba da aikin ta, ina amfanin tarin dukiyar da ya mallaka idan matar sa bata zauna a gida ta kula da Abdallah da kannen sa ba? Duk da ya san ita wannan Rahinah daban ta ke da sauran mata a kan boko zata iya barin komai, son Dan kawai ta sani, amma baya jin ta san yadda ake kula da yara da tarbiyyar su.
Yunwar da yake ji shima ta sa ya bar tunanin komai da sauraron karatun Rahinah ya nufi kitchen. Ya bude freezer, an zuba komai na amfani kamar yadda yayi wa Atiku umarni, one regrettable thing shine ya sallami Kukun gidan, don kada ya kalle masa mata, shi kuma ko suyar kwai bai iya ba.
Sai kawai ya jona kettle din dafa ruwan zafi ya dafa shayi ya hada shi sosai da peakmilk da lipton ya zuba a kofuna guda biyu, ya dora su akan karamin faranti, ya dauko sabon cake a firji ya aza bisa, da pizza wadda ya san Atiku ne ya ajiye masa su don baya rabo da cin su koyaushe. Kai tsaye ya koma sama, so yayi ya zauna ya ci a kicin din amma wata zuciyar ta ce a’ah, akwai hakkin ciyarwa yanzu a wuyan ka.
Don haka ya nufi dakin Rahinah kan sa tsaye, an ce faduwar gaba asarar namiji ce, kamar yadda yayi tsammani dakin a bude yake, sakaya kofar kawai aka yi. Don duk mukullan gidan suna hannun sa jiyan da dare Nene ta damka masa bayan sun koma.
Sallamar da yayi ciki ciki yayi ta kamar an tilasta shi, don ya sa a ran sa ba Rahinah yayi wa sallama ba, a’ah, mala’ikun da ke tare da ita ne. Bata ji sallamar da yayi ba haka bata ga shigowar sa ba domin ta dora filo akan ta ta rufe fuskar ta tana cigaba da bin karatun ta cikin taushin murya, sanye yake da kayan barci pajamas samfurin ‘BloomingDale’s’. Jin kamshin turaren sa yasa ta janye filon daga fuskar ta a hankali.
Yana nan a handsome HABEEBUNsa! Dan gayun nan wankakke, rashin wadatar haske ne ya hana mata ganin yanayin kyakkyawar fuskar sa wadda ko cikin duhu kyakkyawa ce.
“Sorry for the interruption Ma’am” (ya nemi afuwar katse mata karatun ta). “I brought tea for you” (na kawo miki shayi ne) ya sake fada. Tare da dora mata farantin akan bedside din ta. Wanda yake dab da inda kan ta yake.
Kamshin tsadadden lipton din ne ya tuna mata rabon ta da abinci, amma ko wannan shi ya saura shayi a duniya da garin Abuja bakidaya bazata sha shi ba.
“Dauki tsiyar ka ka fita min a daki, bana son ganin mummunar azzalumar fuskar ka” maimakon kalaman ta su bashi haushi kamar yadda ya san ta fada ne don ta bakanta masa, su yi irin wacce suka saba, sai ya hada hannuwa cikin salama yace,
“the ugly wicked man comes in peace. Maida wukar Ma’am. Albarkar haihuwa kike ci har gobe kuma ita za ki cigaba da ci har karshen rayuwar mu”.
Da fadin hakan ya juya akan takun sa zai bar dakin, yana kokarin fita ya ce,
"Welcome to your humble abode!”.
Sai ji yayi kamar daga sama ta ce
“Habib!”
Bai juyo ba amma ya dakata, hannun sa akan marikin kofa, sai ji yayi taratsatsa! Ta hada kofin shayin da shayin da bango, “to hell with your tea, wannan ya zama lokaci na karshe da zaka kuma shigo min daki, kuma ka gaggauta kawo min Da na”.
A wannan lokacin duk yadda ya so ya hakurkurtar da zuciyar sa ya kasa, juyowa yayi ya dubeta a gicciye da sexyeyes din shi, wadanda a kullum su ke gilma mata tamkar shifcin gizo.
“Na dauka kin fi kowa sanin hanyar kotu, ko kin ji nace da ke ki janye karar ki? Ba’a gaya miki na amsa sammaci na zo ba? Don in tsaya da ke a kotu a kan kwatar Da?”
Ya karasa fucewa daga dakin. Tare da cewa "kina bukatar komawa islamiyya ki kara koyo tarbiyyah, Kura da fatar Akuya kawai”.
Kafin ya kai ga bude kofar ta yi maza ta sha gabansa.
“Kayi kadan kace min jahila, tunda duk jahilcin nawa a haka ka like mini, ka hana rayuwa ta sakat tun haduwa ta da kai, bayan na samu mun rabu meyasa ka ki yin auren ka da wadda ke son ka, har sai da ka janyo aka sake lika min kai?
Wallahi ka sayar da maza, mara zuciya kawai wanda bai yarda bakin da ya furta rashin so har abada ba zai taba dawowa yayi furucin so ba. Na tsane ka Habibu Nahuche, na fada na kara bana son ka, Dan da na Haifa da kai kaddara ce ta yi min sanadin sa amma ba so ba.
Don haka ka sa a ran ka don shi na dawo, kuma zaman sa nake yi. Ka dauko min Da na duk inda ka kai shi ko in koma kai karar ka wurin Allah”.