← Book details Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 10

Sashe 2

Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aunty ta ce, "Muna tare da Rahinah tsayin shekaru masu yawa, tana karatun likita a Jamus, sai dai ta zo ta kwana biyu ta koma. Yanzu ne ta dawo gida gabadaya ta fara aiki a Abuja. Circumstances ne ya sa muka gane cewa ita ce, ba don wani cikin su (ita ko Habibu) ya gaya mana ba.
Hajiya gudun juna suke yi, bayan kuma a fili yake dayan su bai iya sake aure ba da dan uwan sa ba.
Laifin da muka yi masa har ya kwace Abdallah shi ne, mun yi plan din da ya ga Rahinar sa a gidan mu. Ba don haka ba sun zabi har su tsufa ba su kara neman juna, while dukkannin su sun san inda junan su ke rayuwa. Alaqar da ke tsakanin mu ce basu sani ba.
Hajiya, Habibu da Rahinah suna bukatar interference na iyaye da masu iko da su, domin su taimaka wajen gyara rayuwar su, su kuma ci gaba da rainon dan da Allah ya ba su a tsakiyar su".
Hajiya ta nisa cikin al'ajabi,
"Ke nan 'yar family din Sarkin Fulanin Girei Habibu ya aura?"
Daddy ya ba ta wannan tabbacin, sannan ya kara da cewa, "Uban ta shi ya sha nono ya saki na kama. Abin da dukkanin mu ba mu sani ba, kuma muke son sani shi ne, laifin da Rahinah ta yi wa Habibu, da laifin da Habibu ya yi wa Rahina suka gwammace su rayu a tagayyare cikin soyayyar juna shekara goma ba tare da juna ba".
Hajiya ta ce, "Sha'ani na miji da mata ai babu yiwuwar sai an san abin da ya hada su. Hanyar gyara kawai za a nema a sulhunta su. Oh ni Kaltume Ya Allah ka nuna min wannan ranar... da Habibullahi zai sake aure a rayuwar sa ta duniya, duniya kuma ta shaida".
Sai kawai ta soma matsar kwallah. Kwallan da ba ta komi ba ce face ta farin ciki, a dalilin sunsuno cewa lokacin auren Habibu ya zo. In dai da gaske 'yar su Aunty ita ce mahaifiyar Abdallah, ita shaida ce kan cewa babu wadda Habibu yake jira sai ita, ko da za ya soma furfura ba aure.
Uncle Usman ya ce, "Ai sulhu ba zai yiwu ba tare da an san rootcause na matsalar ma'aurata ba. Ta hanyar sanin mene ne hakikanin matsalar su ne za a san hanyar magance ta da hana ta sake faruwa a gaba.
Don haka Hajiya komai yana hannun ki yanzu. Ke kadai za ki iya tankwara Habibu ya nemi sulhu da matar sa.
Hajiya ta girgiza kai ta ce, "Wani irin lallashi ne ban yi masa ba a kan aure? Wane irin nasiha ne ban yi masa ba? Wace irin addu’a ce ban yi masa ba? Don haka tunda dai wannan din ita ce uwar Abdallah kuma mu duka shaida ne a kan cewa ita kadai yake so, sannan kai ne madaurin auren ta, to mu taru mu gyara sunnah, in ba su shirya don Allah ba sa shirya albarkacin dan su. Ku tashi yanzun nan komin dare mu wuce Nahuche in gaya wa madaura auren sa".
Ba karamin jin dadin shawarar Hajiya Daddy Usman da maidakin sa suka yi ba. A take ya kira Ambasada Shehu ya gaya masa duk abin da yake faruwa da hukuncin da Hajiya Kaltume ta yanke.
Ambasada sabida sanin da ya yi wa Habibu da Rahinah sai ya ga cewa shawarar su ba mai billewa ba ce idan har ba Rahinah da kan ta ta amince za ta koma wa Habibu ba, to fa baza’a haifi da mai ido ba, don haka ya ce su ci gaba da abin da suka tsara, shi kuma zai zauna da Dr. Rahinah formally ya tattashe ta a kan komen ta gidan Habibu don ita ce mai babbar matsala ba Habibu ba. Duk suka yi na’am da shawarar Ambasada.
*******

A Nahuche, baffanin Habibu sun ji dadin batun da Uncle da Hajiya Kaltume suka zo da shi. To kowa a kan gwiwa yake da damuwar rashin auren Habibun. Dadin dadawa an ce uwar dan sa Abdallah. Don haka kowa ya yi na’am da a maida auren.
Amma zasu jira Ambasada tukunna kamar yadda yace sai ya zauna da Rahinah officially akan maganar komen nata, matsayin ta na bazawara wadda addini ya baiwa damar zaben mijin aure.

Suna kan hanyar dawowa Zamfara daga garin Nahuche wayar Ambasada ta shigowa Uncle Usman, da sauri ya amsa cikin fara’a yana gaya masa nasarar tafiyar su Nahuche da matsayar da aka cimma idan Ambasada ya gama Magana da ita Rahinah. Ambasada Shehu sai ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya sannan yace da Usman,
“kunna data ka duba WhatsApp, na turo maka wani abu yanzun nan da ‘Daily Trust’ suka fitar cikin makon nan”.
Da sauri Uncle ya hau duba dayar wayar sa.
Salatin da ya yi ba Aunty kadai ya firgita ba har Hajiya Kaltume. Sai ya kasa Magana kuma, sabida kunyar Hajiya Kaltume, a lokaci guda yana kissima irin yadda zai saka kafar wando guda da Rahinah, ana ganin ta mai ilmi ashe bata da hankali ko kankani? Kuruciya bata bar ta ba a shekaru 29?
Kasa fada musu ya yi, yayi shiru, duk da tambayar sa ko lafiya da suke ta yi yake jera salati? Sai ya ga gara su ji a bakin sa akan su ji a media. Ya gaya musu Rahinah ce ta yi karar Habibu a kotu, gobe zasu shiga Federal High Court ita da shi su fara Shari’ah akan dan su, amma su kwantar da hankalin su (he will never let this happen) insha Allah in dai yana raye kuma shine uban ta, zai yi maganin Rahinah.
Jikin su duka sai yayi sanyi, a lokaci guda kowacce ta soma tunanin ko dai a hakura ne? Allah kadai ya san abinda ya boye a karkashin wannan takun-sakar na Habibu da Rahinahr sa, sai kuma su da suka aiwatar da rayuwar su ta dan lokaci tare a Jamus.
Har suka iso gida jikkunan su a sanyaye suke. Aunty Badiya bata kai Uncle Usman jin ciwon abinda Rahinah ta yi ba, domin ya nuna bacin ran sa a fili, fada ya ke ta yi kamar Rahinar na ganin sa har suka isa Zamfara.
Hajiya kam ta fi kowa jin babu dadi, Habibullahi a Kotu! Wani abu ne da bai taba faruwa da shi ba, kuma wai da uwar Dan ka wannan terere da bankada da me ya yi kama. In Rahinah na son karbar dan ta ta bi ta maslaha mana ko ta zo ta same ta ta gaya mata sai kawai ta sa su a bakin duniya?
Dama can Hajiya Kaltume tana jin haushin Rahinah, a bisa ganin cewa, sabida ita Habibu ya ki aure, balle yanzu da ta yi wannan danyen aikin, ana cikin kokarin gyara aure.
Sai Hajiya ta ji Rahinah ta kara sire mata, amma zata ci albarkar Usman don miji ne har miji ga ‘yar ta, wanda ba’a taba jin kan su da Badiya ba shekaru ashirin da doriya, sannan zata ci albarkacin dan ta. A yadda ta san Habibullahi, da son da ya ke wa Abdallah, to ba kotu ba, ko ina Rahinah zata je zata gaji ta bari babu mai iya raba shi da Abdallah.
Uncle Usman yayi kwafa “banda hauka irin na Rahinah? Wa ya gaya mata ana jayayya a kan Da? Da, na kowa ne kuma ajiyar Ubangiji ne ga iyayen sa, zamu gamu da ita, sai ta gwammace bata taba sanin Usman Girei ba”.
Ko da suka isa Zamfara, anan ya bar Aunty Badiya. A daren ya dawo Kaduna, washegari ya nufi ‘airport’ ya bi jirgin ‘Max Air’ zuwa Abuja don hanyar Abuja ta kazanta a wannan dan tsukin, ba’a fiya bi da mota ba, balle shi da yake a kagauce da yin tozali da Rahinah, ko a waya bai kira ta ba, burin sa ya bude ido ya gan ta gaban sa, yana kuli-kulin kubra da ita. A sanin da ya yi wa Habibu ko kadan bai son tashin hankali balle abinda zai taba mutuncin sa.
******

*RAHINAH*
Chapter 2 · 0% Book details